Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Mutum 25 sun mutu, macizai sun sari wasu, mata biyu sun haihu muna wajen masu garkuwa'
Fiye da mutane 300 da aka yi garkuwa da su a hare-hare daban-daban a jihohin Kwara da Neja sun samu ƴanci bayan kusan shida, bayan wani ceto da fadar shugaban Najeriya ta bayyana a matsayin mafi girma da jami'an tsaro suka gudanar a rana guda.
Daga cikin waɗanda aka ceto akwai mutum 163 da aka yi garkuwa da su a harin da aka kai kan al'ummomin Woro da Nuku a jihar Kwara a watan Fabrairu, inda aka kashe wasu mutane.
Sai dai bayan shafe kusan wata shida a hannun masu garkuwa da su, waɗanda aka ceto sun dawo da labarai masu tayar da hankali kan irin halin da suka shiga, ciki har da mutuwar mutane, cizon macizai, yunwa da kuma haihuwa ba tare da samun kulawar lafiya yadda ya kamata ba.
Ɗan majalisar dokokin jihar Kwara mai wakiltar mazaɓar Woro, Abdullahi Halidu Danbaba, wanda ya gana da wasu daga cikin waɗanda aka ceto a Ilorin, ya ce sun bayyana irin mawuyacin halin da suka fuskanta a lokacin da suke tsare.
Muhimman bayanan da muka tattara
Ga manyan abubuwan da waɗanda aka ceto da kuma al'ummominsu suka bayyana bayan an kuɓutar da su:
Mutane kusan 25 sun mutu a hannun masu garkuwa da su
Wata daga cikin matan da aka ceto ta shaida cewa kusan mutum 25 sun mutu a lokacin da suke tsare, sannan aka binne gawarwakinsu a can.
Macizai sun sari mutum uku
Wata daga cikin wadanda aka ceto ta ce macizai sun sari mutane uku yayin da suke tsare a wurin.
Sun shafe kusan wata shida a cikin daji
An sace mutanen ne a ranar 3 ga Fabrairu, kuma suka shafe kusan wata shida a hannun masu garkuwa da su kafin a ceto su a watan Agusta.
Mata biyu sun haihu a lokacin da suke tsare
A cewar Danbaba, mata biyu sun haifi jarirai yayin da suke hannun masu garkuwa da su.
Ya ce matan ba su samu cikakkiyar kulawar lafiya ba, kuma wasu daga cikin tsofaffin waɗanda da wata nas da aka tsare tare da su ne suka taimaka wajen kula da su.
Sau daya kawai ake ba su abinci a rana
Waɗanda aka ceto sun ce masu garkuwa da su suna ba su abinci sau daya kacal a rana.
Danbaba ya ce wani karamin yaro da aka ceto ya fito yana neman ƙuli-ƙuli saboda yunwa.
Wasu yara maza har yanzu suna hannun masu garkuwa da su
Ɗan majalisar ya ce wasu yara maza masu shekaru tsakanin 13 zuwa 16 ba su cikin waɗanda aka sako.
A cewar waɗanda aka ceto, masu garkuwa da mutanen suna shirin ɗaukar yaran cikin kungiyarsu.
Al'ummomi sun tara fiye da Naira miliyan 180
Al'ummomin da abin ya shafa a ƙaramar hukumar Kaiama sun tara sama da naira miliyan 180 domin biyan kuɗin fansa da fatan samun ƴancin mutanen.
Sai dai rahotanni sun ce masu garkuwa da mutanen sun ƙi amincewa da kuɗin, suna cewa bai isa ba.
An kuma ce sun buƙaci al'ummomin da su nemi taimakon gwamnatocin jihohin Kwara da Neja domin a samu karin kudin fansa.
Ba iyalan wadanda aka sace aka nemi kudin fansa kai tsaye ba
Ƴan'uwa sun ce masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi kowace iyali kai tsaye domin neman kuɗin fansa ba.
Ƴanbindiga su yi barazanar aure ƴanmatan da kuma kashe tsofaffi
Rahotanni daga al'umma sun ce masu garkuwa da mutanen sun yi barazanar tilasta wa wasu daga cikin ƴan matan da aka sace aure.
An kuma ce sun yi barazanar kashe tsofaffin matan idan tattaunawar neman sakin wadanda aka sace ba ta samu ci gaba ba.
Wasu iyalai sun kasa yarda da labarin ceto
Da farko, wasu mazauna yankin sun kasa yarda cewa an kuɓutar da ƴanuwansu.
Sai da hotuna da bidiyon waɗanda aka ceto suka fara yaɗuwa a kafafen sada zumunta sannan iyalai suka fara tabbatar da cewa mutanen nasu suna cikin wadanda aka kubutar.
An ceto mutane 308 a aikin
Fadar shugaban ƙasa ta ce jami'an tsaro sun kuɓutar da ƴan Najeriya 308 da aka yi garkuwa da su a hare-hare daban-daban a jihohin Kwara da Neja.
Har yanzu akwai fargabar sake kai hare-hare
Duk da ƙaruwar jami'an tsaro a yankin, mazauna al'ummomin sun ce har yanzu suna cikin fargabar yiwuwar sake kai musu hare-hare.
Wasu daga cikin al'ummar sun kuma zargi makiyaya da ci gaba da zama barazana, inda suka ce ana ci gaba da kiwo a gonakinsu.