Sojojin Najeriya sun ce sun ceto fasinjoji 33 da aka sace a Zamfara
Rundunar sojin Najeirya ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma sun ceto mutum 33 da 'yanbindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara, bayan samun sahihan bayanai kan sace fasinjojin da ke tafiya ta yankin Magazu.
Sanarwar da jami'in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ta ce sojojin tare da 'yan sanda a Tsafe sun samu bayanin lamarin ne da yammacin ranar 8 ga Agusta, 2026.
Nan take dakarun suka nufi wurin da lamarin ya faru, inda suka ci karo da maharan suna tafiya da waɗanda suka sace zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Bayan an yi musayar wuta, maharan suka tsere cikin daji tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Rundunar ta ce an ceto dukkan fasinjojin 33 cikin koshin lafiya ba tare da samun asarar rai ba.
A halin yanzu, dakarun na ci gaba da farautar maharan, yayin da kwamandan rundunar ya yaba wa jami'an bisa gaggawar daukar mataki tare da jaddada aniyar rundunar na kare rayuka da kuma tabbatar da tsaron manyan hanyoyin sufuri a yankin Arewa maso Yamma.