Me Sheikh Jingir ya ce kan takarar Muslim-Muslim da ya janyo masa suka?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A ƙarshen makon nan ne kafar sada zumunta da ma kafafen yada labarai suka ɗauki ɗimi da musayar yawu da cece-kuce kan kalaman da shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi dangane da takarar Muslim-Muslim.

Yayin wani jawabi ranar Asabar a Kano a lokacin walimar bikin auren gata da gwamnatin Kano ta shirya ga ma'aurata 1,500 da ta ɗauki nauyin aurensu a faɗin jihar, Sheikh Jingir ya ce bai taɓa da-na-sanin zaɓen Musulmi a matsayin shugaba da mataimakinsa ba.

Sheikh Sani Yahaya Jingir dai ya yi fice wajen goyon bayan tikitin Muslim-Muslim da kuma kiransa ga Musulmai su sake mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen 2027, kamar yadda ya nemi a yi a zaɓen 2023.

BBC ta yi duba dangane da haƙiƙanin kalaman da malamin ya faɗa da kuma martanin da ta janyo.

Abin da Sheikh Jingir ya faɗi

A cikin bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga Sheikh Jingir tsaye akan mumbarin jawabi a gaban gwamnan Kano da na Jigawa da Zamfara da Katsina, yana ta jawabi kafin mai gabatarwa ya nemi malamin ya dakata saboda ƙarancin lokaci.

Ga wani ɓangare na jawabin nasa:

"Saboda haka kuke ganin gwanina Ahmad Bola Tinubu wanda ya ɗaga tutar siyasarsu ya yi mata kirari da Muslim-Muslim, na ce ina ɗaya daga cikin masu ɗaga tutar Musulunci na kira jama'a ku taho mu yi Muslim-Muslim," in Sheikh Jingir.

Shehun malamin ya ƙara da yin suka ga masu cewa Najeriya ba ta Musulmai ba ce.

"Na sani cewa kafirai na jin zafin wannan kalma. To amma ba akwai Kiristoci ba? Ba akwai Yahudawa ba? Ba akwai masu bautawa maigirmaba? Ni Musulmi mai wa'azin Muslunci da na ce Muslim-Muslim mai na taɓa nasu? Na hana Kirista-Kirista? Na hana mai girma-mai girma ya faɗa ne? Na hana ɗan taltalbatalta ya fada ne? Amma a matsayina na Musulmi Muslim-Muslim....Amma wani zai ce a dimokraɗiyya ce akwai su wane. Ba sa sallah. To kai ne wakilinsu? To mu muna sallah, muna azumi. Kuma dimokraɗiyyar kun ce "majority carry the vote". "

Daga ƙarshe sai Sheikh Jingir ya yi kira ga al'ummar da ke wurin da su yi ƙuri'a domin nuna cewa suna da yawa.

"Jama'a gwauro da gwauruwa, tuzuru da tuzuruwa Allah ya ba ku abokan zaman tare na aure da za su iya hada wannan taron. To a nan ina kiran ku don Allah kowa ya je ya gyara ƙuri'a. Mu nuna wa duniya ƙarya kafirai suke cewa sun fi yawa a Najeriya. Ƙarya suke yi. Ba don Allah ya taimake mu na ce Muslim-Muslim ba me ragon jini zai ce sun fi yawa. Da aka gwada muka kwantar su da ƙasa. Ko na biyu ba su zo ba. Na ukun ma sai da maguɗi. Jama'a ƙuri'ata Musulunci ce. Jama'ar Musulmi taku fa? kar wani ya ruɗe ku...", In ji Sheikh Yahaya Jingir.

Tasiri biyu na kalaman Sheikh Jingir

Dakta Kabiru Sufi malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, CAS sannan mai nazarin kimiyyar siyasa ya ce kalaman Shehun Malamin na da tasiri guda biyu a siyasance.

  • Zaburar da Musulmi sake zaɓar Tinubu: "Kalaman za su iya yin abubuwa guda biyu. Na ɗaya yana ƙoƙarin zaburar da waɗanda yake yi wa jawabi waɗanda Musulmai ne akan cewa su yi ƙoƙarin tabbatar da abin da suka yi a baya na zaɓen tikitin da ke ɗauke da Musulmi da Muslmi domin dalilan da ya kawo na tabbatar da ƙarfin Musulunci da sauran wasu dalilai," in ji Sufi.
  • Tunzura wadanda ba Musulmi ba ƙin zaɓar APC: To amma kuma a ɗaya ɓangaren ya manata da cewa kalaman kamar yadda muke gani sun zaman kamar na tunzuri ga wasu ɓangarorin ƙasar wadanda kuma a baya sun zaɓi shugaba Tinubun. Yanzu ana ganin kamar hakan ya fusata wasu daga cikinsu. Hakan ka iya sa wasun su su barranta da tikitin da a baya suka zaɓa a lokacin da ba su yi irin wannan kallo ba da malamin ya fito da shi a fili," in ji Dakta Kabiru Sufi.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Tun bayan kalaman malamin na addini, ƴan Najeriya suke ta tattaunawa akan batun inda mafi yawanci suke sukar kalaman Sheikh Jingir bisa cewa na tayar da tarzoma ne da rarraba kan al'umma.

Femi Fani-Kayode:

Tsohon ministan sufurin jiragen sama ta Najeriya kuma jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"I na girmama Sheikh Jingir amma kuma ya zama dole na yi nuni da kalaman tsatstsauran ra'ayi da ya gabatar a nan ba gaskiya ba ne kuma ba za su taimaka ba.

Abin da ya fi muna a duka kalaman ma shi ne sun kasance na tsokana.

Najeriya ba ƙasar Musulmi ba ce ba kuma ƙasar Kiristoci ba ce."

Adamu Garba:

Fitaccenmai sharhi kan al'amuran tsaro da tattalin arziƙi a Najeriya, Malam Adamu Garba ya ce kalaman ba su kamata ba.

"Duk da cewa ina kaucewa shiga tankiyar siyasa amma kalaman da aka alakanta da Sheikh Jingir - idan dai gaskiya ne to rashin sanin ya kamata ne, tsokana ce ya kamata a gujewa irin wannan."

Zariya Yusuf Madaki:

Shi ma wani mai shafin X, mai suna Zariya Yusuf Madaki ya bayyana takaicinsa dangane da kalaman da ake alaƙantawa da Sheikh Jingir inda ya ce abin baƙin cikin shi ne yadda malamin ya furta kalaman a gaban gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya.

"...babban haɗarin al'amarin shi ne yadda wasu za su iya ɗauke kai daga kasancewar wasu gwamnonin shiyyar arewa maso yammaci..."

Jamilu Sufi:

Wannan ma wani ne mai amfani da shafin X wanda ke nuna rashin jin daɗinsa kan kalaman da ake alaƙanta wa da Shehun Malamin.

"Wannan ba Musulunci ba ne. Wannan tsantsar tunani ne na mamaya da rigar addini. Duk wani malamin da ya fito fili ya yi kamfe na "Musulmai su yi mamaya" kan wasu ƴan Najeriya to ya ƙaddamar da yaƙi akan haɗin kan ƙasa."

Kwankwasiyya Amana:

Shafin mabiya ɗarikar Kwankwasiyya da ke X shi ma ya yi nasa tsokaci kan kalaman na Sheikh Jingir.

"...Sheikh Jingir wanda yake a matakin ƙarshen rayuwarsa yana kalamai na sarayar da rayuwar ƴan Najeriya da ma makomar ƙasar."