WAFCON: Darussa uku daga wasan Najeriya da Masar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya wato Super Falcons ta samu nasarar tsallakewa zuwa zagayen kwata-fainal bayan ta tsallake matakin rukuni da ƙyar da gumin goshi.

Najeriya ta lallasa takwararta ta Masar da ci 6 da 2 ne a wasan wanda aka fara kowace tawaga a cikin rukunin na cike da fargabar rasa damar tsallake, musamman Najeriya da Zambia da Malawi.

Amma a lokacin da alƙalin wasan ya busa tashi daga wasa a filin wasa na Stade Larbi Zaouli da ke Casablanca, sai hankalin ƴan ƙwallon na Super Falcons da mago bayanta suka shiga farin ciki da murna.

Da farko an yi zaton Najeriya, wadda ta lashe gasar sau 10 kuma take riƙe da kambunta za ta yi ɓari tun a rukuni ne bayan ta yi rashin nasara a wasan farko na gasar.

Wannan ya sa bayan rashin nasarar a hannun Malawi a wasan farko da doke Zambia da ci 1-0 da ƙyar a wasa na biyu, Super Falcons ta shiga wasan ƙarshe na rukuni da Masar tana fargabar cewa idan ba ta samu nasara gida za ta koma tun daga matakin rukuni.

Yadda aka yi wasan Najeriya da Masar

Asisat Oshoala ce ta fara zura kwallo daga bugun fenariti, sannan Gift Monday, Uchenna Kanu, Christy Ucheibe, Rashidat Ajibade da Joy Omewa suka ƙara sauran ƙwallayen.

Duk da cewa Nadine Ghazi ta ci wa Masar ƙwallaye biyu, hakan bai hana Najeriya samun gagarumar nasara da tabbatar da tikitin zuwa zagaye na gaba ba.

Baya ga sakamakon, wasan ya bayyana muhimman darussa uku game da Super Falcons kafin fara wasannin fitar da gwani.

Yadda Najeriya ta tunkari matsin lamba

Kafin a fara wasan, Najeriya tana cikin wani mawuyacin hali.

Mai riƙe da kambun ta fara gasar da rashin nasara, lamarin da ya sa mutane da dama suka fara shakkar ko za ta iya ci gaba da kare kambunta.

Amma maimakon matsin lambar ya raunana ta, sai ya zama abin da ya ƙara mata ƙwarin gwiwa.

Tun daga farkon wasa ƴan wasan Najeriya suka nuna ƙwazo, suka riƙa ƙirƙirar damarmaki kuma suka zura ƙwallaye shida fiye da adadin da suka ci a wasanninsu biyu na farko a haɗe.

Babbar ƙungiya ba a san ta da fara gasar cikin sauƙi ba. Abin da ke bambanta ta shi ne yadda take dawowa idan ta fuskanci ƙalubale.

A wasan da Masar, Super Falcons ta nuna juriya, nutsuwa da ƙarfin zuciyar da ake buƙata domin cin nasara a ƙarƙashin matsin lamba.

Rinsola Babajide ta cancanci fara wasa

Duk da cewa ƴan wasa shida ne suka ci wa Najeriya ƙwallaye, Rinsola Babajide ce ta kasance ginshiƙin kai hare-haren ƙungiyar.

An ba ta kyautar gwarzuwar wasan bayan ta bayar da taimakon ƙwallaye biyu tare da jefa masu tsaron bayan Masar cikin ruɗani saboda saurinta, dabarunta da kuma iya yanke shawara cikin gaggawa.

Ita ce ta ba Gift Monday ƙwallon da ta ci a ƙarshen rabin farko, sannan ta sake bai wa Uchenna Kanu damar cin ta uku bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Wannan bajinta ya ƙara jefa mai horar da ƙungiyar cikin tunani kafin wasan kwata fainal.

Babajide ta nuna a duk lokacin da aka ba ta dama tana iya kawo sauyi a wasa. Tana da sauri, tana iya ƙirƙirar dama kuma tana iya karya tsaron abokan hamayya. Wannan ya nuna cewa ta cancanci fara wasa maimakon ci gaba da zama a benci.

Super Falcons ta sake gano ƙarfin kai hari

Najeriya ta shiga wannan wasa ne da fargaba biyu: Ta tunanin yadda za ta kaya da kuma nauyin kare kambunta na gasar.

Sai dai ta ƙare wasan da ƙwallaye shida daga 'yan wasa shida daban-daban.

Ko da yake uku daga cikin ƙwallayen sun fito ne daga bugun fanareti, yadda ƙungiyar ta riƙa kai hare-hare ya nuna cewa ta fara samun daidaito da fahimtar juna kamar yadda aka santa a baya.

Wani abin lura shi ne yadda aka samu masu cin ƙwallo daban-daban maimakon ta'allaƙa da ƴan wasan gaba kawai.

Yanzu duk ƙungiyar da za ta kara da Najeriya ba za ta iya mayar da hankali kan Asisat Oshoala ko Rashidat Ajibade kaɗai ba. Gift Monday, Uchenna Kanu, Christy Ucheibe da Joy Omewa sun nuna cewa Super Falcons na da 'yan wasa masu iya kawo sauyi a kowane lokaci.

Abin da wannan nasara ke nufi

Wannan nasarar ta tabbatar da cewa Najeriya na da saurin ƙwarin gwiwa tare da damar neman lashe gasar karo na 11.

Sannan kuma idan ta samu nasara a wasan kwata-fainal, shi ne zai ba ta damar zuwa gasar cin kofin dunita ta mata, kasancewa duk ƙungiyoyi huɗu da suka buga wasan kusa da na ƙarshe a gasar WAFCON, sun samu tikitin zuwa gasar duniya.