Matakan soji uku da Amurka ta ɗauka waɗanda suka girgiza duniya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A tsawon shekaru Amurka ta jagoranci wasu matakan soji da suka kai ga kamawa da kisan jagororin wasu ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da kuma shugabannin ƙasashen da ake zargi da aikata miyagun laifuka.

Daga cikin mutanen da Amurka ta tsara da kuma ɗaukar irin wannan mataki a kansu akwai tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein da tsohon shugaban ƙasar Libya Muammar Gaddafi da kuma tsohon shugaban ƙungiyar Al-Qaeda Osama bin Laden.

Hukumomin leƙen asiri na Amurka sun ɗauki duk wasu matakai wajen ganin sun cimma burinsu na kamawa da kuma kawar da wadannan jagorori.

To amma ta yaya aka gudanar da wannan aiki mai matuƙar wahala?

Kisan Osama bin Laden

Dakarun soji da na leƙen asiri na Amurka ne suka kitsa tare da aiwatar da aikin kamawa da kuma kashe Osama bin Laden.

Tsohon shugaban na ƙungiyar Al-Qaeda ya kwashe shekaru yana cikin jerin mutanen da Amurka ke nema ruwa a jallo bisa zargin aikata laifuka daban-daban, ciki har da gagarumin farmakin nan na ranar 11 ga watan Satumban 2011 da aka kai a ƙasar.

Aikin sojin wanda aka yi wa laƙabi da 'Neptune Spear' a turance, an kwashe watanni ana tsara shi, amma an aiwatar da shi ne cikin ƴan mintuna a watan Mayun 2011.

Wata runduna da musamman ta dakarun Amurka ce ta tashi da tsakar dare daga cikin ƙasar Afghanistan ta yi tafiyar kimanin kilomita 192 zuwa cikin Pakistan, inda Osama bin Laden ke ɓuya.

Sojojin sun isa ne a cikin wani jirgi mai saukar ungulu, kuma a cikin duhun daren suka tunkari gidan da Osama yake, sun kashe mutane biyar, cikin su har da Osama bin Laden.

Bayan minti 40, sojojin sun bar gidan tare da gawar Bin Laden da kuma wata na'urar kwamfuta ɗauke da bayanan sirri a kan ƙungiyar Al-Qaeda da tsarin ayyukanta.

Sojojin sun bar sauran gawarwakin a gidan, ciki har da ta wata mata da kuma daya daga cikin ƴaƴan Osama.

Haka nan sun bar wasu mata uku da yara biyu a cikin gidan wadanda duk aka daura musu ankwa.

An gudanar da aikin ne a ranar 2 ga watan Mayun 2011, bayan shugaban Amurka na wancan lokaci Barack Obama ya bayar da umarnin hakan a safiyar ranar Juma'a 29 ga watan Afrilu.

A farkon ƙaddamar da samamen, rundunar sojojin Amurka da ake kira 'SEAL Team Six' ta bar sansanin sojin Amurka da ke birnin Jalalabad na ƙasar Afghanistan a cikin jirage masu saukar ungulu biyu wadanda aka tsara su musamman domin wannan aikin.

Haka nan akwai wasu jiragen masu saukar ungulu da ke yi wa guda biyun rakiya domin kai dauki idan an samu wata matsala.

Jiragen sun shiga sararin samaniyar Pakistan ne da tsakar dare kuma a cikin sirri, har zuwa lokacin da suka isa Abbottabad, inda Osam yake ɓuya.

Cikin tawagar akwai wani mai fassara da kuma wani kare da aka bai wa horo na musamman kan aikin soji, wanda aka yi wa laƙabi da Cairo.

Sojojin na Amurka sun yi amfani da igiya daga cikin jirgi inda suka sauka a saman rufin ginin da Osama ke ɓuya.

An tsara shirin ta yadda za a gudanar da shi babu kuskure ko kaɗan, sai dai daya daga cikin jiragen ya samu tangarɗa inda ya yi sauka ƙasa ba tare da shiri ba, amma babu wani sojan Amurka da ya jikkata.

Lokacin da sojojin suka shiga gidan, sun riƙa bi ɗaki-ɗaki har sai da suka iske Osama, inda suka kashe shi.

Amurka ta yanke shawarar ƙin sanar da Pakistan game da shigar jiragenta sararin samaniyar ƙasar domin gudun kada wani ya kwarmata wa Osama bin Laden labarin.

Kama Saddam Hussein

A ranar 13 ga watan Disamban 2003, dakarun Amurka sun ƙaddamar da wani aikin soji da aka yi wa laƙabi da 'Operation Red Dawn' a turance, a kusa da garin Ad-Dawr, kudu da birnin Tikrit na ƙasar Iraqi.

Wannan aiki ne ya kai ga kama shugaban ƙasar Iraqi na wancan lokaci Saddam Hussein da ransa.

Bayan kawar da Saddam daga kan mulki sa'ilin yaƙin Iraqi, sai sojojin Amurka suka ƙaddamar da gagarumin aikin kama Saddam da sauran jami'an da suka yi aiki ƙarƙashin gwamnatinsa.

An kwashe watanni ana aikin, inda aka riƙa tattara bayanai daga mutane daban-daban, ciki har da fursunoni da sojoji da kuma fararen hula.

Sai dai bayanin da aka samu daga wani na kusa da Saddam ne, wanda aka riga aka kama, ya taimaka wa sojojin Amurka isa wata gona da ke gefen gari a kusa da Tikrit, mahaifar Saddam.

Sojojin sun fara ne da duba wasu wurare biyu da aka yi zaton Saddam na ɓoye, kafin daga baya suka gano shi a wani ramin ƙarƙashin ƙasa.

Bayanan da sojoji suka bayar sun ce Saddam bai nuna turjiya ba, a maimakon haka ya miƙa wuya ne lokacin da ya ga an kama shi.

Kanar James Hickey, wanda shi ne jami'in sojan da ya jagoranci aikin ya ce sun samu bayanan da suka taimaka musu wajen kama Saddam ne ta hanyar wani mutum da suka kama a birnin Bagadaza.

Duk da cewa an taɓa kai samame wurin ba tare da ganin Saddam ba, akwai yiwuwar cewa lokacin da aka je wurin da farko baya nan, kasancewar ya riƙa sauya wuraren ɓuya ne domin guje wa kamu.

Lokacin da sojojin Amurka suka kama Saddam ba su iske wata na'urar sadarwa a tattare da shi ba, wanda hakan ke nuna cewa ba ya da sauran ikon bai wa dakarun ƙasar umarni.

Sojojin da suka kama Saddam sun samu tsabar kudi dala 750,000 da kuma bindiga ƙirar AK-47 a inda yake ɓuya.

Muammar Gaddafi

Yayin da guguwar sauyi ta kaɗa a ƙasashen Larabawa, wadda ta fara daga ƙasar Tunisia a watan Disamban 2010, ba a yi tsammanin cewa wannan guguwa za ta kaɗa har Libya ba.

Muammar Gaddafi ya kasance a kan mulki tun daga shekarar 1969, inda ya kwashe sama da shekara 40 yana mulkar ƙasar.

Yayin da magoya bayan Gaddafi ke kallon mulkinsa a matsayin tsaro da kariya da kuma lumana a ƙasar, ƴan adawa na zargin shi da kama-karya da kuma take hakkin bila'dama.

Lokacin da boren ya isa Libya a farko-farkon 2011 sai lamarin ya rikiɗe zuwa yaƙi, inda ƙungiyar masu ɗauke da makamai suka riƙa yaƙar gwamnatin Gaddafi.

Daga baya ƙungiyoyin yan tawayen sun haɗe ƙarƙashin lema ɗaya inda suka samar da Majalisar Tafiyar da mulki ta ƙasa (NTC), wadda ta samu nasarar karɓe iko da yanki mai girma a ƙasar.

Lokacin da yaƙin ya ƙazance sai kwamitin sulhu na MDD ya amince da shawarar tura sojoji zuwa ƙasar domin kare fararen hula.

A watan Maris din 2011, dakarun ƙawancen tsaro na NATO, wanda suka ƙunshi sojojin Amurka da Faransa da kuma Birtaniya suka isa Libya.

Sojojin sun riƙa ƙaddamar da hare-hare ta sama kan gwamnatin Gaddafi.

Waɗannan hare-hare sun taimaka wa ƴan tawaye wajen cin galaba kan dakarun Gaddafi, lamarin da ya kai ga tuntsurar da gwamnatinsa.

Gaddafi ya tsere daga Tripoli babban birnin ƙasar zuwa mahifarsa Sirte, garin da ya kasance cikin na ƙarshe-ƙarshe da suka kasance ƙarƙashin ikon Gaddafi.

A ranar 20 ga watan Oktoban 2011, Gaddafi ya yi yunƙurin tserewa daga Sirte a cikin kwamban motoci. Dakarun NATO sun kai wa kwambar motocin farmaki, lamarin da tarwatsa tafiyar.

Bayan harin na sama, mayaƙan NTC sun kama Gaddafi a wajen da ya ɓoye a cikin wani rami da ke kusa da birnin Sirte. An kama shi a raye amma da raunuka.

Ya rasu jim kadan bayan kama shi, sai dai har yanzu babu tabbataccen bayani kan abin da ya yi sanadiyyar mutuwar tasa.