Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na son Endrick, Napoli na harin Gabriel Jesus
Chelsea na shirin bayar da aron ɗanwasan gaba na Ukraine Mykhaylo Mudryk, inda Coventry City ke cikin ƙungiyoyin Premier da ke son ɗanwasan. (Football London)
Barcelona na fatan cimma yarjejeniya da Manchester City kan ɗanwasan tsakiya na Spain Rodri, mai shekara 30, inda za ta sake taya ɗanwasan kan fam miliyan 51.3. (Times)
Inter Milan na tattaunawa da Tottenham kan sayen ɗanwasan Ingila Djed Spence kan fam miliyan 25.6, inda ɗanwasan ke son komawa ƙungiyar ta Seria A. (Athletic)
Manchester United ta nace wa ɗanwasan baya na Newcastle Lewis Hall, kuma ɗanwasan mai shekara 21 ya fi son ya tafi Old Trafford. (Sun, external)
An yi wa Chelsea da Manchester United tayin ɗanwasan tsakiya na Ingila Myles Lewis-Skelly inda Arsenal ke son sayar da shi bayan zuwan ɗanwasan Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 28 daga Newcastle. (Football London, external)
Manchester United na nazarin taya ɗanwasan baya na Club Brugge Joaquin Seys, wanda aka bayyana darajarsa fam miliyan 30. (Mirror)
Haka ma Manchester United na son karɓo aron ɗanwasan gaba na Real Madrid da Brazil Endrick, mai shekara 20, amma Jose Mourinho ba ya son rabuwa da ɗanwasan. (Mirror, external)
Napoli na ƙoƙarin cimma yarjejeniya kan ɗanwasan gaba na Brazil Gabriel Jesus amma Arsenal za ta iya sayar da ɗanwasan ne kawai idan ta samu kudi masu gwaɓi daga yuro miliyan 20. (Caught Offside)
Iliman Ndiaye ya yi watsi da tayin Al Hilal ta Saudiyya, inda ɗanwasan na Everton da Senegal mai shekara 26, ke son ci gaba da murza leda a gasar Premier. (Fabrizio Romano, external)