Abianosa de Muñoz: Ƙauye a ƙasar Spain da za a yi dare biyu a rana ɗaya

    • Marubuci, ريشيكا شارما
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بي بي سي
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Ƙauyen Abianosa de Muñoz na ƙasar Spain na shirin fuskantar wani dare na musamman, duk da cewa a yanzu kusan babu mazauna a ƙauyen, babu gidajen cin abinci, kuma ba kasafai baƙi ke ziyartarsa ba.

Akwai ƙauyuka da ke cike da natsuwa da kwanciyar hankali, kuma wannan ƙaramin ƙauyen na Abianosa de Muñoz na cikinsu, kuma yana lardin Burgos a arewacin ƙasar Spain ne.

Ƙauyen ba shi da gidajen cin abinci ko shaguna. Abin da ake da shi kawai shi ne wani mashaya da ba ta buɗe ƙofofinta, da kuma wani ƙaramin shagon sayar da kayan masarufi da ya daina aiki tun da daɗewa.

Idan mutum ya tsaya ya natsu a cikin ƙauyen, zai ji kaɗawar iskar yanayi. Ana jin ƙarar ƙudan zuma masu shawagi, yayin da tsuntsaye ke raira shawagi tsakanin rufin gidajen dutse da kuma kan titunan da kusan babu kowa. A bayan gidajen kuma, gilmawar wata tarakta guda ɗaya ne kaɗai ke nuna cewa har yanzu akwai rayuwar ɗan Adam a ƙauyen.

A cikin wannan yanayin, ƙaramin farin motar burodi daga wani gidan burodi da ke kusa kan shigo ƙauyen sau ɗaya a mako. Motar tana kawo burodi ga ƴan tsirarun mazauna ƙauyen, wanda ke ɗan katse shirun da ya mamaye ƙauyen.

Ga mazaunan, wannan ne tsarin rayuwarsu ta yau da kullum a wani wuri da ba kasafai yake fuskantar wani babban lamari ba. Sai dai duk da wannan yanayi, ƙauyen da aka daɗe ana danganta shi da ƙarancin baƙi, zai zama a wannan bazarar ɗaya daga cikin wuraren da za su fi jan hankalin mutane a duniya.

A ranar 12 ga Agustan 2026, za a samu cikakken kusufin rana da zai ratsa Tekun Atlantika. Wannan ne karo na farko da za a ga irin wannan kusufi daga babban yankin Turai tun shekarar 1999.

A cewar masaniyar kimiyyar lissafi da ke Madrid, Maria Teresa López Sánchez, wannan kuma shi ne cikakken kusufin rana na farko da za a gani daga babban yankin Spain tun shekarar 1912.

Sai dai za a iya ganin cikakken kusufin ne kawai daga wata ƙaramar hanya da ta ratsa nahiyar Turai, kuma ƙauyen Abianosa de Muñoz na cikin tsakiyar wannan hanya.

Yanayin ƙauyen ya sa ya zama ɗaya daga cikin wurare mafi dacewa don kallon wannan abin al'ajabi. Gonakin alkama masu launin zinariya da ƙananan tuddai sun bazu zuwa yamma ba tare da manyan gine-gine ba. Haka kuma, ƙarancin hasken wutar lantarki da rashin cunkoson jama'a da ake sa ran za a samu a shahararrun wuraren kallo na ƙara wa ƙauyen armashi.

Lokacin da kusufin zai faru ma yana ƙara jan hankali, domin zai auku ne daf da faɗuwar rana. Hakan zai haifar da abin da masana suka kira "duhu sau biyu cikin dare guda," ko kuma kamar yadda López Sánchez ta bayyana, "tamkar kana kallon faɗuwar rana sau biyu cikin ƴan mintuna kaɗan."

Bayan wannan, a cikin daren, za a kuma iya kallon taurarin Perseids, lamarin da zai haɗa manyan abubuwa biyu na sararin samaniya a dare guda, abin da ba kasafai yake faruwa ba.

An haifi Raúl Grande Rivia a wannan ƙauye shekara 73 da suka gabata, kafin daga bisani ya koma Madrid tare da iyalansa yana yaro. Ya tuna da wani mai kai wasiƙu da jaridu wanda ke zuwa ƙauyen a kan jaki.

A cewarsa, mai kai wasiƙun kan yi barci a kan jakin yayin tafiya, saboda jakin ya riga ya san duk wuraren da zai tsaya, har da ƙaramin ofishin wasiƙa da ke ƙarshen ƙauyen.

Tsawon shekaru da dama, rayuwar mazauna ƙauyen ta dogara ne da noma, lambunan kayan marmari, gonakin inabi da kuma kiwon dabbobi. Amma da aikin noma ya fara amfani da manyan injuna, tare da ƙarancin sauran damar samun aiki a yankin, mutane da dama suka bar ƙauyen zuwa manyan birane kamar Madrid, Bilbao da Barcelona domin neman abin yi.

A yau, adadin awakin da ke kiwo a kan tuddan da ke kewaye da ƙauyen ya fi yawan mutanen da ke zaune a cikinsa. Haka kuma, manyan filayen furannin sunflower sun mamaye gonakin da a da ɗaruruwan mazauna ƙauyen ke aiki a cikinsu.

Sai dai kusufin rana da za a yi a wannan bazara ya fara jawo hankalin iyalan da suka taɓa barin ƙauyen su dawo gida.

Raúl Grande ya ce yana shirin zuwa ƙauyen tare da abokiyar zamansa, ɗansa, jikokinsa da kuma manyan abokansa domin su shaida wannan abin al'ajabi. Haka kuma, ɗan'uwansa zai zo tare da ƴaƴansa uku, jikansa da kuma ƴar'uwarsu. Gaba ɗaya za su kasance kusan mutum 20, lamarin da zai ƙara yawan mutanen ƙauyen sosai a wannan dare.

Ba su kaɗai ba ne. Wani mazaunin ƙauyen, Álvarez, ya ce sauran mazauna ma suna shirin karɓar baƙuncin ƴan uwansu da abokansu. Ana sa ran mutane za su yi tururuwa zuwa ƙauyen daga sassa daban-daban na ƙasar Spain, har ma daga ƙasashen waje, domin kallon wannan gagarumin abin al'ajabi na sararin samaniya.

Farfesa Lucretia López ta Jami'ar Santiago de Compostela, ta ce abubuwan ban mamaki da ba kasafai suke faruwa ba, musamman irin su kusufin rana, inda ta ce hakan yakan sa mutane su "sake komawa wuraren da suke da alaƙa da su."

A cewarta, a ƙauyen Abianosa de Muñoz, wannan tururuwar komawa ƙauyen da ake yi ya fara wuce iyalan waɗanda suka taɓa zama a wurin, har ya fara jawo hankalin baƙi daga wurare daban-daban.

Otal ɗin Parador de Lerma, wanda ke cikin tsohon fadar Duke na Lerma, ya fara domin an fara kama ɗaki tun daga shekarar 2022 domin kallon wannan kusufin rana. Alberto Bosque Cuyo, jami'i a Hukumar Yawon Buɗe Ido ta yankin Castile da León, ya ce kusan duk wuraren kwana a yankin sun cika tun da daɗewa.

Ya ce masu son kallon kusufin ba su tsaya neman wurin da ya fi shahara ba, kawai suna neman wurin da ya fi dacewa ne domin ganin abin al'ajabin cikin inganci.

Raúl Grande ya ba da labarin wata mata daga jihar California ta Amurka da ke shirin zuwa Spain domin kallon kusufin. Ya ce ya fara zagayawa gida-gida a ƙauyen yana neman wanda zai karɓi baƙuncinsu, saboda suna son kallon kusufin daga wurin da yake ganin shi ne mafi dacewa a duk ƙasar Spain.

Ya ce har yanzu yana mamakin yadda ƙaramin ƙauyensu ya zama - ko da na ɗan lokaci ne - wurin da duniya baki ɗaya ke magana a kai.

A duk faɗin lardin Burgos, al'ummomi na shirya wuraren kallon kusufin tare da shirya tarukan jama'a domin kallon wannan gagarumin al'amari. A ƙauyen Abianosa de Muñoz kuwa, mazauna da baƙi za su nufi kogunan da ke saman ƙauyen domin kallon kusufin.

Saboda a lokacin cikakken kusufin rana zai kasance kusan digiri takwas kacal, samun fili buɗe ba tare da wani cikas ba zai kasance muhimmi. Hakan ya sa kogunan da ke kan tuddai suka zama kamar kujerun gaba domin kallon wannan abin al'ajabi da ba kasafai ake samu ba.

Sai dai waɗannan koguna ba wurin kallo kaɗai ba ne. Tsawon shekaru da dama, mazauna ƙauyen sun saba taruwa a wurin domin kallon faɗuwar rana tare. Har ma wani tsohon mazaunin ƙauyen ya buƙaci a warwatsa tokarsa a wannan wuri bayan rasuwarsa, saboda irin muhimmancin da wurin ke da shi a zuciyarsa.

Ga Álvarez, ƙauyen Abianosa de Muñoz gida ne da bai taɓa barinsa ba, kuma bai da niyyar barinsa. Shi kuwa Raúl Grande, yana komawa ƙauyen kusan kowace shekara. A duk lokacin bazara, ƴaƴan Álvarez mata kan dawo garinsu na haihuwa, al'adar da suka ce za su ci gaba da riƙewa ko bayan rasuwar mahaifiyarsu.

A yanzu Grande na zuwa tare da ƴaƴansa, jikokinsa da kuma abokansu. Burinsa shi ne alaƙar da ya gina da ƙauyen tun yana ƙarami ta koma ga jikokinsa ma, ta yadda wata rana su ma za su riƙa dawowa domin ziyartar ƙauyen.

Ya ce: "Abin da ya fi muhimmanci a gare ni shi ne ƴaƴana da jikokina su ji irin ƙaunar da nake yi wa wannan ƙauye."

A ranar da za a yi kusufin rana, ƙauyen Abianosa de Muñoz zai sake cika da hayaniyar mutane da tattaunawa. Ƙamshin gasasshen naman rago zai mamaye wuraren da babu gidajen cin abinci, yayin da dariyar yara za ta sake amo daga wurin da a da makarantar ƙauyen take.

Sannan, cikin wasu ƴan mintuna na musamman, duhu zai sauka sau biyu a dare guda, abin da ba kasafai ake gani ba.

Saboda wani abin mamaki na yanayin ƙasa, wannan ƙaramin ƙauye da kusan ba a san da shi ba a Spain zai zama ja hankalin duniya na wani ɗan lokaci, yayin da dubban mutane za su taru domin kallon ɗaya daga cikin abubuwan al'ajabi mafi ban sha'awa a sararin samaniya.

Muhimman shawarwari ga masu son kallon kusufin rana

Ƙauyen Abianosa de Muñoz yana da tazarar kusan mintuna 30 da mota daga birnin Burgos, kuma tafiya daga Madrid zuwa ƙauyen na ɗaukar sama da sa'o'i biyu.

Masauki:

Babu otal ko wuraren saukar baƙi a ƙauyen Abianosa de Muñoz. Haka kuma, Otal ɗin Parador de Lerma da ke kusa ya cika tun da daɗewa kasancewar an riga an kama ɗakunan. Har yanzu ana iya samun masauki a Burgos ko Madrid, inda mutum zai iya yin tafiyar yini zuwa ƙauyen. Sai dai ana sa ran za a fuskanci cunkoson ababen hawa sosai bayan an gama kallon kusufin.

Lokacin kallon kusufin:

Ana sa ran kusufin zai fara a ƙauyen Abianosa de Muñoz da misalin 7:33 na yamma (agogon ƙasar Spain). Cikakken kusufin kuma zai fara da misalin 8:29 na yamma, kuma zai ɗauki ƙasa da mintuna biyu.

Kada ku gaggauta barin wurin bayan faɗuwar rana:

A daren ne kuma za a iya kallon ruwan taurarin Perseids. Saboda hasken wata zai yi rauni a lokacin, sararin ƙauyen mai duhu da ƙarancin hasken lantarki zai kasance ɗaya daga cikin wurare mafi kyau don kallon taurarin da ke shawagi, muddin sararin sama ya kasance a buɗe kuma babu hasken wuta da zai hana gani.