Wane ne Mohsen Rezaei sabon shugaban majalisar tsaron Iran?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Iran ta zaɓi Mohsen Rezaei a matsayin sabon babban sakataren Majalisar Tsaron Ƙasar, bayan murabus ɗin Mohammad Bagher Zolghadr.

Sabon shugaban zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara yadda Iran za ta tafiyar da rikicinta da Amurka da kuma Isra'ila.

An naɗa shi muƙamin ne, bayan saukar Mohammad Bagher Zolghadr, wanda rahotonni suka ce Mojtaba Khamenie ya naɗa shi babban mai ba shi shawara kan harkokin siyasa.

A baya dai Ali Larjani ne kan wannan matsayi, kafin Isra'ila ta sanar da kashe shi a wani hari a watan Maris.

Wane ne Mohsen Rezaei?

Mohsen Rezaei, tsohon ƙwararren soja ne kuma gogaggen ɗansiyasa da ya riƙe muƙamai daban-daban a Iran.

Ya riƙe manyan muƙamai a rundunar sojin ƙasar, inda har ya kai matsayin babban kwamandan dakarun juyin juyaa halin ƙasar.

Tsohon jagoran addainin ƙasar Ayatolla Ali Khamenei ne ya naɗa shi muƙamin lokacin yana matashi, muƙamin da ya shafe shekara 16 yana riƙe da shi.

Shi ne ya jagoranci rundunar juyin-juya halin ƙasar lokacin yaƙin Iran da Iraƙi na 1980 - 1988.

A shekarar 2021 ya shiga takarar shugaban ƙasar Iran, kodayake ya sha kaye a hannun tsohon shugaban ƙasar, Ebrahim Raisi.

A baya-bayan nan sabon Jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei ya naɗa babban mai ba shi shawara kan harkokin soji.

Wane tasiri zai yi?

Ana kallon naɗin nasa a matsayin alamar cewa tsofaffin jiga-jigan siyasar Iran har yanzu su ne ke riƙe da iko a ƙasar, duk da hasashen da ake yi cewa za a fara bai wa matasa damar shiga manyan muƙaman jagoranci nan gaba kaɗan.

A baya, Rezaei ya sha bayyana cewa yana da matuƙar muhimmanci Iran ta ci gaba da riƙe iko da Mashigar Hormuz.

Inda ya ce ci gaba da iko da mashigar ya fi muhimmanci ga Iran fiye da mallakar makaman nukiliya.

Masu lura da al'amura na nuna cewa mutum ne wanda kusan da wuya ya amince a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka.

Majalisar tsaron ƙasar Iran ce babbar hukumar da ke kula da harkokin tsaron ƙasar.

Ita ce ke da alhakin daidaita manufofin tsaro da harkokin ƙasashen waje, tare da haɗa manyan jami'an gwamnati da sojoji da hukumomin leƙen asiri domin yanke muhimman shawarwari.

Don haka ne masu bibiyar al'amuran siyasar ƙasar ke ganin zai taka muhimmiyar rawa wajen kare muradun ƙasar, wajen cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka

Shugaban ƙasa ne ke jagorantar majalisar, yayin da jagoran juyin juya halin ƙasar ke da wakilai biyu a cikinta.