Me ya sa cutar ƙyanda ke saurin yaɗuwa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, André Biernath and Kate Bowie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 7
An samu ɓarkewar cutar ƙyanda mai tsanani a ƙasar Bangladesh, wadda ake zargin ta kashe sama da mutane 100, yawancinsu yara, wanda a dalilin hakan ne gwamnatin ƙasar ta ƙaddamar da wani shirin rigakafi na gaggawa domin daƙile yaɗuwar cutar.
Wannan lamari ya nuna cewa akwai matsaloli a tsarin rigakafin ƙasar. Wato, ba kowa ne ke samun allurar rigakafin ba ko kuma ba a kai ga isassun mutane ba. Wannan ne ya sa cutar ta samu damar yaɗuwa cikin sauri.
Masana sun kuma yi gargadin cewa ƙyanda cuta ce mai matuƙar saurin yaɗuwa.
Saboda haka, tana iya yaɗuwa daga ƙasa zuwa wata ƙasar cikin sauƙi, musamman idan mutane suna yawan zirga-zirga tsakanin ƙasashe.
A shekarun 2024 da 2025, an samu yawan ɓarkewar cutar ƙyanda fiye da yadda aka gani cikin sama da shekaru 20 da suka gabata.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa wasu ƙasashe kamar Amurka da Mexico da Indiya da Angola da Pakistan da Kamaru da Indonesia duk sun fuskanci ɓarkewar cutar a cikin watanni shida da suka gabata.
Yadda ƙyanda ke yaɗuwa da hatsarinta
Ƙyanda wata cuta ce da ƙwayar cutar virus mai matuƙar saurin yaɗuwa ke haifarwa.
Ana kamuwa da ita ta hanyar iska, musamman idan mai cutar ya yi numfashi, tari ko atishawa, inda ƙananan ɗigon ruwa da ke ɗauke da ƙwayar cutar ke yaɗuwa cikin iska.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Haka kuma, ana iya kamuwa da ita ta hanyar taɓa abubuwan da ƙwayar cutar ta gurɓata.
Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Amurka - CDC - ta bayyana ƙyanda a matsayin "ɗaya daga cikin cutuka mafi saurin yaɗuwa a tsakanin mutane."
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ƙiyasta cewa mutum ɗaya da ya kamu da ƙyanda na iya yaɗa cutar ga kusan 9 cikin mutum 10 da ba su yi rigakafi ba idan suka kusance shi.
Mutum mai cutar ƙyanda na iya yaɗa cutar daga lokacin da alamomi suka fara bayyana har zuwa aƙalla kwanaki huɗu bayan fitowar ƙuraje a jiki.
Yawanci, ƙyanda na warkewa cikin kwanaki 7 zuwa 10. Amma a wasu lokuta, tana iya janyo matsaloli masu tsanani kamar ciwon wahalar numfashi (pneumonia) da ciwon sankarau (meningitis) da makanta, da kamuwa da jijjiga (seizures).
Yara ƙanana ƴan ƙasa da shekaru biyar da jarirai da mata masu juna biyu, da kuma mutane masu raunin garkuwar jiki sun fi haɗarin kamuwa da cutar cikin sauƙi.
A cewar binciken Jami'ar Johns Hopkins, a Amurka kusan 1 cikin mutum 5 da ba su yi rigakafi ba na bukatar a kwantar da su asibiti idan sun kamu da ƙyanda.
A shekarar 2024 kuwa, adadin ya ƙaru, inda kusan kashi 40 na waɗanda suka kamu da cutar suka buƙaci kulawar asibiti.
Duk da cewa ƙyanda na iya kisa, hakan bai cika faruwa ba.
Me ya sa cutar ƙyanda ke sake dawowa?
A ƙasar Bangladesh, an samu ƙaruwa mai yawa na cutar ƙyanda a makonnin baya-bayan nan.
Bayanai daga ma'aikatar lafiya sun nuna cewa an samu fiye da mutum 7,500 da ake zargin sun kamu da cutar tun daga tsakiyar watan Maris.
Daga cikin wannan adadi, an tabbatar da fiye da mutum 900 sun kamu da cutar, wanda ya zarce adadin 125 da aka samu a shekarar 2025.
Cutar ƙyanda ta fi yaɗuwa a wuraren da babu allurar rigakafin ƙyanda sosai. Domin hana ɓarkewar cutar, ana buƙatar kusan kashi 95% na jama'a su yi rigakafi domin samun kariya.
A Bangladesh, ana yi wa yara ƙanana allurar rigakafin ƙyanda tun suna da watanni tara. Bugu da ƙari, ana gudanar da manyan gangamin nuna muhimmancin rigakafi duk bayan shekara huɗu.
Sai dai yawancin waɗanda suka kamu da cutar a ɓarkewar cutar na baya-bayan nan jarirai ne da har yanzu ba su kai lokacin da za a fara yi musu rigakafi ba.
Haka kuma, an dakatar da gangamin rigakafin ƙyanda na musamman tun shekarar 2020, abin da ya bar giɓi a tsarin kariya.

Asalin hoton, Getty Images
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), yawan mutanen da ke samun rigakafin ƙyanda ya ragu a duniya a 'yan shekarun nan. Wannan ya bar miliyoyin yara cikin haɗarin kamuwa da cutar.
A watan Fabrairu, an samu ɓarkewar ƙyanda a wasu makarantu a arewacin London, a ƙasar Birtaniya, lamarin da ya sa hukumomin lafiya suka sake tunatar da iyaye muhimmancin yi wa 'ya'yansu rigakafi.
Haka kuma, a watan Yuli, an samu mafi yawan adadin wadanda suka kamu da cutar a tsakanin yan shekaru 33 a ƙasar Amurka. Wannan ya faru ne a daidai lokacin da ra'ayoyin kin rigakafi ke ƙara yaɗuwa a Amurka da wasu ƙasashe.
Hukumar CDC ta Amurka ta bayyana cewa, saboda ƙyanda na da matuƙar saurin yaɗuwa, tana iya ketare iyakokin ƙasashe cikin sauƙi, musamman a wuraren da yawan masu yin rigakafi ya faɗi ƙasa da kaso 95.
Duk da ƙaruwa barkewar wannan cutar a wasu ƙasashe, akwai wasu ƙasashe kamar Brazil da Timor-Leste da Sri Lanka da suka samu nasarar kawar da cutar gaba ɗaya a cikin 'yan lokutan nan.
Alamomin cutar ƙyanda

A cewar Hukumar Kiwon Lafiya ta Birtaniya (NHS), ƙyanda tana da alamomi da dama da ke fara bayyana kafin ta fara tsanani. Daga cikin su akwai:
- Zazzabi mai tsanani, yawanci jiki zai yi zafin da ya kai maki 39ºC, musamman idan ba a sha magunguna kamar paracetamol ko ibuprofen ba
- Zubar majina ko toshewar hanci
- Atishawa da tari
- Jan idanu da zubar hawaye
- Ciwon ido (conjunctivitis)
- Ƙananan fararen kuraje a kumatu
- Kuraje a jiki, wanda yawanci ba sa ƙaiƙayi. Suna bayyana bayan kwana uku zuwa huɗu da fara samun sauran alamomi. Kurajen kan fara fitowa a bayan kunnuwa da fuska, sannan su yaɗu zuwa jiki da ƙafa da hannu.
A wasu lokuta masu tsanani, cutar ƙyanda na iya haifar da kumburi a ƙwaƙwalwa (encephalitis).
Idan mace mai juna biyu ta kamu da cutar, NHS ta bayyana cewa hakan na iya haifar da zubewar cikin ko haihuwa da wuri ko jariri ƙanƙani fiye da kima, ko kuma haihuwar jariri a mace.

Asalin hoton, Getty Images
Yadda ake magance cutar ƙyanda
Babu wani magani na musamman da ke kashe ƙwayar cutar ƙyanda kai tsaye. A mafi yawan lokuta, likitoci kan ba da magunguna ne don rage alamomi yayin da garkuwar jiki ke yaƙar cutar.
Yawanci ana amfani da magunguna kamar paracetamol domin rage zazzabi da ciwo.
Hukumar Kiwon Lafiya ta Birtaniya (NHS) ta bayyana cewa ana samun saukin cutar ƙyanda yawanci a cikin kusan mako daya da kamuwa da ita.
A wannan lokaci, yana da muhimmanci mai cutar ya;
- Huta sosai
- Sha ruwa da yawa domin guje wa rashin ruwa a jiki
A wasu lokuta masu tsanani, ana iya buƙatar kulawar asibiti, inda za a iya ba da taimakon numfashi da sauran magunguna domin rage tsanani da rikicewar cutar.

Asalin hoton, Getty Images
Yadda za a kare kai daga kamuwa da cutar ƙyanda
Hanya mafi inganci wajen kare kai daga kamuwa da cutar ƙyanda ita ce ta hanyar yin allurar rigakafi.
Allurar da ake amfani da ita ita ce MMR, wadda ke kare mutum daga cututtuka uku lokaci guda da suka hada da ƙyanda da mumps da rubella.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran hukumomin lafiya sun ba da shawarar cewa a yi wa yara alluran rigakafin kyanda akalla guda biyu domin samun cikakkiyar kariya mai ɗorewa.
Allura ta farko ana yi wa yara tsakanin watanni 9 zuwa 15
Ta biyu kuma ana ba su a tsakanin watanni 15 zuwa 18, gwargwadon tsarin kowace ƙasa
Haka kuma, matasa da manya ana ba su shawarar yin rigakafin idan ba su yi ba tun suna yara.
Bugu da ƙari, manya da aka yi musu rigakafi tsakanin shekarun 1963 zuwa 1968 ana ba su shawarar su duba tarihin rigakafinsu domin tabbatar da irin allurar da aka yi musu saboda a wancan lokaci an yi amfani da wata nau'in rigakafi da ba ta da ƙarfi sosai, wadda daga baya aka daina amfani da ita.
A cewar WHO, rigakafin ƙyanda ya hana mutuwar mutane fiye da miliyan 60 tsakanin shekarun 2000 zuwa 2023.
Duk da haka, a shekarar 2023 cutar ƙyanda ta haddasa mutuwar kimanin mutum 107,500 a duniya, yawancinsu yara ƙanana da ba su yi rigakafi ba ƙasa da shekaru biyar.
Hukumar WHO ta kuma bayyana cewa yawan yaran da suka samu allurar ƙyanda ta farko ya kai kashi 83 a shekarar 2023, wanda ya yi ƙasa da na shekarar 2019 da ya kai kashi 86.










