Iyalai 10 mafiya arziki a duniya

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Abdalla Dzungu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili
- Aiko rahoto daga, Nairobi Kenya
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Iyalai 10 mafi arziki a duniya sun mallaki ɗaruruwan biliyoyin daloli ta hanyar mallakar kamfanonin dillanci da saye da sayarwa, da ikon gudanar da dukiyar ƙasa da kuma mallakar manyan gine-gine na gani na faɗa.
A cewar shafin Investopedia mai bibiyar harkokin kuɗi da zuba jari a duniya, tasirin iyalai masu arziki yana jaddada wata al'adar ta martaba kuɗi da dukiya a duniya.
Waɗanda ke kan gaba a harkokin kasuwanci manya ne a idon mutane da yawa, kuma ana yanke masu hukunci ne kan dagewar su wajen ci gaba da nuna ɗaukaka ko kuma idan suka gaza yin hakan, saboda ana masu Kallon fitattu da suka kai ƙololuwar shahara.
Ga jerin iyalai 10 mafi arziki, bisa ga alƙaluman Bloomberg da kuma Investopedia na baya-bayan nan.
10. Iyalan Wertheimer
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan 88
Fitaccen Gidan kayan ado da kwalliya na Faransa mai suna Chanel ya shahara saboda sayar da tufafi masu tsadar gaske da turaren Chanel No.5 da kuma shahararren mai ƙera kayan kwalliya, Karl Lagerfeld, wanda ya rasu a ranar 19 ga Fabrairu, 2019.
A yanzu ƴan'uwan juna Alain da Gerhard Wertheimer ne suka mallaki kamfanin wanda kakansu ya kafa kafa tare da Gabrielle Coco Chanel. 'Yan'uwan suna matsayi na 49 a jerin masu kuɗi da Forbes ta wallafa, inda kowannensu ke da dukiyar da ta kai dala biliyan 39.4, a ƙididdigar da aka yi a ranar 26 ga Mayun 2026.
9. Iyalan Ambani

Asalin hoton, Getty Images
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan 89.2
Rukunin kamfanin Reliance Industries na Indiya, kamfani ne a nahiyar Asiya wanda ba kowa ya san shi ba.
Amma Shugaban kamfanin, Mukesh Ambani, wanda mahaifinsa ne ya kafa kamfanin a shekarar 1957, yana matsayi na 21 a jerin masu kuɗin duniya da Forbes ta wallafa, inda ya zuwa 26 ga watan Mayun 2026, ya mallaki dala biliyan 99.7, kuma yana jagorantar rassan kamfanin masu kasuwancin mai da tace shi da samar da gas da kuma rukunin masaƙu, yayin da ɗan uwan shi Anil ke kula da rukunin kamfanonin sadarwa da makamashi da nishaɗi da kuma cinikin kaddarori.
8. Iyalan Bettencourt Meyers
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan 92.1
Iyalan Bettencourt Meyers sun sami dukiyarsu ne ta hanyar L'Oréal, wani kamfanin kayan kwalliya na Faransa wanda Eugène Schueller ya kafa a 1909.
Françoise Bettencourt Meyers, jikanyar wanda ya kafa kamfanin kuma mace mafi arziki a duniya, ta taimaka wajen gudanar da dukiyar iyalin ta hanyar matsayinta na hukumar gudanarwar L'Oréal kuma shugabar kamfanin zuba jari na L'Oréal's Investment.
Bettencourt Meyers, wacce ta zaɓi yin rayuwar ta cikin sirri ta kuma shahara wajen buga piano da kuma rubuce-rubuce. A 2025, ɗanta Jean-Victor Meyers ya gaje ta a matsayin mataimakin shugaban hukumar gudanarwar L'Oréal, inda ya ci gaba da jagorantar harkokin kamfanin.
7. Iyalan Mars
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan148.2.
Mars katafaren shagon sayar da kayan maulashe ne musamman alawa da cakulet wanda ya yi suna sosai. A yanzu an fi sanin shi da M&Ms ba Mars bar ba.
A 2017, Mars, kamfanin alawa mafi girma a duniya ya faɗaɗa hanyar samun kuɗin shi inda ya mallaki wani kamfanin kula da dabbobi na VCA a dan dala biliyan 9.1.
Ƴan uwan juna Jacqueline Mars da John Mars da suka mallaki kamfanin, kowacce ta mallaki dukiyar da ta kai dala biliyan 49.1 kuma ya zuwa 26 ga watan Mayun 2026 suna a matsayi na 38 a jerin masu kuɗin duniya da Forbes ta wallafa. Kakansu, Frank Mars, ne ya kafa kamfanin.
Yanzu haka wasu daga cikin ƴaƴansu ne ke gudanar da harkokin kamfanin tare da tallafin wasu ƴan uwa.
6. Iyalan Koch

Asalin hoton, Getty Images
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan 149.5
Iyalan Charles Koch sun samu kuɗin su ne daga zuba jari a harkar mai, amma daga baya ya karkata ga harkar da ta shafi ɗaukar nauyin ƴan takara a zaɓuka da bayar da tallafin karatu a jami'oi da kuma shiga tsakani wajen neman goyon bayan aiwatar da tsare-tsaren gwamnati, da nufin yayata aƙidar mazan jiya.
Charles ya ƙulla haɗaka da ɗan uwan shi David har zuwa lokacin da ya rasu a 2019. An ƙiyasta cewa Charles ya mallaki dukiya da ta kai dala biliyan 73.8 kuma yana a matsayi na 25 a jerin masu kuɗin duniya da Forbes ta wallafa.
Ya zuwa 26 ga watan Mayun 2026, matar marigayi David, Julia Koch da iyalinta suna a matsayi na 24 a jerin masu kuɗin dunya da Forbes ta wallafa.
5. Iyalan Hermès
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan 184.5
Kamfanin kayan kwalliyan Faransa na Hermès ya karae duniya da sayar da kayayyaki kamar mayafi da nekitayil da turare da kuma shahararrun jakkunan hannu na mata na Kelly da Birkin.
A farkon ƙarni na 16, Thierry Hermes ya yi fice wajen ɗinka tufafi masu kyau da daraja a duniya.
A yanzu kamfanin ke ɗinka kayan sawan fitaccen ɗanwasan ƙwallo kwando LeBron James da sauran su. Ya koma amfani da tsohuwar basira da ta zamani wajen ƙera agongon hannu na Hermès Apple wanda ake sayar wa kan dala 1,249 zuwa sama.
Axel Dumas ne shugaban kamfanin a yanzu, kuma Pierre-Alexis Dumas ne mataimakin shi.
4. Iyalan Al Thani
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan 199.5
Iyalan Al Thani suna mulkin Qatar tun daga tsakiyar ƙarni na 19. Mulkin su ya tsallake yunƙurin juyin mulki har sau biyu da yaƙi da kuma guguwar gina sabuwar ƙasar Qatar.
Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ya sauya Qatar zuwa ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya da suka ci gaba, a cikin shekara 18. Ya karɓi ragamar mulkin Qatar ne bayan ya kifar da gwamnatin mahaifin shi ba tare da zubar da jini ba a 1995.
Daga cikin matakan da ya ɗauka harda ƙwace ƙaddarorin mahaifin shi don gudun juyin mulki daga sojoji.
Ƙasar ta ƙara yawan iskar gas da take samarwa cikin sauri.
Sheikh Hamad ya zuba jarin biliyoyin dala a kasuwanci kala-kala, ciki harda na motar Volkswagen da kamfanin mai na Total da kuma bankin Barclays. A 2018, Sheikh Hamad ya miƙa karagar mulki ga ɗan shi na huɗu, Sheikh Tamin bin Hamad al Thani.
3. Iyalan Al Saud

Asalin hoton, Getty Images
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan 213.6
Iyalan masarautar Saudiyya, waɗanda suka shafe kusan ƙarni ɗaya kan mulki, sun tara dukiya mai yawa, wadda aka kiyasta ta kai dala biliyan 140 saboda alfarmar da ke tattare da riƙon sauratar ƙasar.
Dangantaka da Saudi Aramco, ɗaya daga cikin kamfanoni mafi samun riba a duniya ya taimakawa gidan sarautar Saudiyya wajen tara dukiya mai yawan gaske.
Yana da wuya a tantance haƙiƙanin yawan dukiyar gidan sarautar Saudiyya, saboda yawan ƴan asalin gidan ya kai sama da 15,000, waɗanda da yawa daga cikinsu suna harkar kasuwanci, kuma suna samun kwangilolin gwamnati, da sauransu.
2. Iyalan Al Nahyan
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan 335.9
Iyalan Al Nahyan da ake kira da "Gidan Nahyan," su ne iyalai na biyu mafi arziki a duniya.
Jagoran gidan, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, shi ne sarkin Abu Dhabi kuma shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Tattalin arzikin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da na masarautar ƙasar ya haɓɓaka ne saboda ɗimbin albarkatun mai. Wannan ya sa Abu Dhabi ke gogayya da manyan ƙasashe masu arziki a duniya.
Sheikh Mohamed ya zamo sarkin Abu Dhabi kuma shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a 2022. Kafin lokacin, ɗan uwan shi, Sheikh Khalifa, ya mulki ƙasar daga 2004 zuwa 2022.
Ba a ganin sunan Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan a jerin masu kuɗin duniya duk da cewa dukiyar da ya mallaka ta zarce biliyoyi.
1. Iyalan Walton

Asalin hoton, Getty Images
An yi ƙiyasin dukiyarsu ta kai dala biliyan 513.4
Iyalan Walton sun ƙara zama na ɗaya a jerin masu kudin duniya bayan da a 2023 iyalan Al Nahyan suka shige gaban su.
Ƴan uwan juna Rob da Jim da kuma Alice Walton duk sun mallaki dukiyar da ta zarce dala biliyan 100, kuma suna a matsayi na 11 da 12 da kuma 14 a jerin masu kudin duniya da Forbes ta wallafa a ranar 26 ga watan Mayun 2026.
Walmart wani shagon sayar da kayayyaki ne da Sam Walton ya kafa a Arkansas a 1962, kuma shi ne kamfanin da ya fi kowanne samar da kuɗin shiga a faɗin duniya a 2025, inda aka samu dala biliyan 681.
Walmart ya mallaki manyan shagunan sayar da kayyaki fiye da 10,800 a sassan duniya.
Kamfanin ya yi suna wajen sauƙin farashin kayayyaki, kuma yana shan suka kan dokokin ƙwadago da ayake amfani da su.










