Dalilin da ya sa Kim Jong Un bai taɓa magana game da mahaifiyarsa ba

- Marubuci, Sangmi Han
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Korean
- Aiko rahoto daga, Seoul
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 9

Asalin hoton, Cheong Seong-chang
Daga cikin ɗimbin asirai da suka lulluɓe shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, sirrin da ke tattare da mahaifiyarsa shi ne ya fi ɗaukar hankali.
A tsawon shekaru 15 da yake mulki, Kim bai taɓa ambaton sunanta a bainar jama'a ko sau ɗaya ba.
Saɓanin uwaye biyu da suka gabata a zuriyar su Kim Jong Un – Kang Pan Sok, mahaifiyar jagoran da ya kafa ƙasar, Kim Il Sung, da kuma Kim Jong Suk, mahaifiyar Kim Jong Il – wadanda aka daukaka a matsayin "iyayen Koriya", Ko Yong Hui kuwa mace ce da ba a fiya sanin ta ba, kuma babu wani abu da aka sanya masa sunanta.
Wannan tsauraran matakan na boye-boye game da Ko Yong Hui na iya samo asali ne daga abin da ake gani a matsayinta na zamantakewa mai rauni da kuma kasancewarta uwargida, abubuwan da masana ke cewa na iya zama barazana ga tsarin mulkin ƙasar.
Dangane da abin da masana tarihin rayuwa suka tattara, an haifi Ko a birnin Osaka, Japan a shekarar 1952. Mahaifanta sun ƴan asalin tsibirin Jeju a Koriya ta Kudu ta yanzu ne – wato yankin da ake ɗauka a matsayin na maƙiya.
A matsayin mazauna Japan, iyalan Ko sun kasance cikin rukunin "'yan Koriya na Zainichi" – wato baƙin haure da suka zauna a Japan tun lokacin mulkin mallakar Japan a yankin daga 1910 zuwa 1945.
Wadanda suka koma Koriya ta Arewa da farko ana kallon su da kishi domin sun koma da kudi, tufafi da kayan gida daga maƙwabciyar ƙasa mai tsarin jari-hujja.
Sai dai kuma an ba su laƙabin "jjaepo", kalma ta wulakanci da ake amfani da ita ga wata ƙungiya da ake ganin ta gurɓace da aƙidu na ƙasashen waje masu haɗari.
A cikin tsarin rarrabuwar zamantakewa mai tsauri na Koriya ta Arewa – wanda ake kira songbun – 'yan Koriya na Zainichi suna cikin "aji mai rauni", bisa dogaro da tsari aji-aji a cikin al'umma.
Ana sanya musu ido sosai daga gwamnati, kuma da mafi yawancin lokuta ana hana su shiga jami'o'i masu inganci ko kuma samun ayyuka masu kyau da makoma.
Al'ummar Koriya ta Arewa na da tsari mai tsananin bambancin matsayi, wanda wasu masana ke cewa yana kama da tsarin "caste" da ke bambance ƙimar mutum ta hanyar asalinsa.
Haka kuma wani "tsari ne da ake hukunta mutum bisa abin da wani dan uwansa ya aikata", inda ake ladabtar da 'yan ƙasa saboda ayyukan 'yan uwansu, a cewar Dakta Jeung Young-tae na Jami'ar Dongyang.
Labarin 'Cinderella'

Asalin hoton, Yoji Gomi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lokacin da take kusan shekara 10 da haihuwa, iyalan Ko sun yi hijira zuwa Koriya ta Arewa.
Iyalan nata suna cikin kimanin mutane 93,000 na Koriya da suka koma ƙasar kwaminisanci daga Japan tsakanin 1959 da 1984 ƙarƙashin shirin "Aljannar Duniya" – wani tsari da ya yi alkawarin rayuwa mai dadi ga wadanda suka koma, ciki har da kiwon lafiya kyauta, ilimi da kuma ayyukan yi.
Amma ga Ko, ta samu kuɓuta daga wahala da talauci da suka addabi sauran 'yan Koriya na Zainichi bayan ta ja hankalin shugaba Kim Jong Il na lokacin.
Ko da yake Kim bai taɓa bayyana matarsa ko abokiyar zamansa a bainar jama'a ba, bayanan leken asiri sun nuna cewa a lokacin yana da aure da Kim Young Sook, 'yar wani babban jami'in soja, wani aure da mahaifinsa ya zaɓa masa.
An ce Ko, wadda take mamba a fitacciyar ƙungiyar fasaha ta Mansudae Art Troupe, ta dauki hankalin Kim ne saboda "kyawunta na dabi'a da kuma kwarewarta wajen rawa", kamar yadda ɗan jarida ɗan Japan Yoji Gomi ya bayyana, wanda ya wallafa littafi game da Ko a shekarar 2025.

Asalin hoton, Cheong Seong-chang
Ko da yake ba ta taɓa auren shugaba mafi girma ba, kuma gwamnatin ba ta amince da dangantakarta da shi ba, amma Ko ta samu rayuwar da Yoji Gomi ya kira "rayuwar irin ta Cinderella".
Kim Jong Il a lokacin yana tare da matarsa Kim Young Sook, 'yar wani babban jami'in soja. Mahaifinsa Kim Il Sung ne ya zaɓa masa ita.
Rahotanni sun nuna cewa Kim ya kamu da son Ko sosai, wadda daga baya ta fara nuna sha'awa a harkokin siyasar ƙasar.
Amma saboda matarsa ta asali na zaune a babban birnin Pyongyang, Ko tare da 'ya'yanta uku an ajiye su a nesa da kusan kilomita 210, a garin Wonsan da ke bakin teku.
"Kim Jong Un ba ɗan uwar gidan ba ne. A haƙikƙ shi 'ɗan gaba da fatiha ne' na Ko Yong Hui," in ji Kim Hyung-su na ƙungiyar cibiyar bincike ta Northern Research Association.
Ana yi wa "Zuriyar Paektu masu mulki kallon mai tsarki, don haka tunanin cewa shugaba zai kasance ɗan 'jjaepo' abu ne da ba za a iya yarda da shi ba."
Yara da aka haifa ba tare da aure ba suna fuskantar tsananin wariya a Koriya ta Arewa, wadda duk da kamanninta na tsarin kwaminisanci, har yanzu tana cike da tsoffin aƙidu na falsafa Confucius.
Masana sun ce ana amfani da ra'ayoyi kamar biyayya ga iyaye da kuma aminci wajen koyar da mutane yadda za su kasance masu bin doka da oda.

Asalin hoton, Cheong Seong-chang
Gomi ya bayar da wani ƙarin dalili kan yadda Kim Jong Un ya taso nesa da babban birnin ƙasar. A wancan lokaci, jirgin ruwa na zirga-zirga tsakanin Wonsan da Japan, wanda hakan ke sauƙaƙa wa Ko haɗuwa da mutanen da ke isa daga Japan.
Ya ce: "Ko ta yi kewar ƙasarta ta Japan sosai, kuma ta koyar da 'ya'yanta harshen Japan."
Kenji Fujimoto, wani mai girki na sushi da ya yi wa Kim Jong Il aiki daga 1988 zuwa 2001, ya rubuta a littafinsa cewa Kim Jong Un "yana iya rera waƙoƙin Japan sosai" kuma "yana kishin bunƙasar tattalin arziƙin Japan".
Har ma Kim Jong Un ya taɓa ziyartar Disneyland na Tokyo a Japan tare da babban ɗan'uwansa, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai na Japan suka ruwaito suna ambaton jami'an wancan lokaci. Gomi ya ce Ko ma ta riƙa zuwa Japan ita da sakatariyarta.
Gado
Ko Yong Hui ba ta taɓa amincewa a matsayin surukar Kim Il Sung ba," in ji Ryu Hyun-woo, wani jami'in diflomasiyyar Koriya ta Arewa da ke gudun hijira, a littafinsa mai suna Kim Jong Un's Secret Vault.
Dakta Cheong Seong-chang na Cibiyar Sejong ya ce da ace Ko ta samu yardar tsohon Kim, da hotunan Kim Il Sung tare da jikansa Jong Un sun bazu sosai a ko'ina.
Sai dai duk da hakan bai faru ba, Ko ta samu amincewar Kim Jong Il — inda ta rika taka rawa a matsayin uwargidan shugaban ƙasa tana rakiyar mijinta wajen duba rundunonin soji tare da ƙulla alaƙa da muƙarrabansa.
Har ma Kim yakan nemi ra'ayinta kafin ya yanke wasu muhimman shawarwari na siyasa, kamar yadda Fujimoto, mai girki, ya rubuta.
Wani shirin bidiyo na hukuma da aka shirya bayan mutuwar Kim Jong Il a shekarar 2011 ya nuna Ko tana tare da shugaban a wasu ziyarce-ziyarce na cikin gida — amma ba a bayyana sunanta ko matsayinta ba.
Ba a taɓa fitar da wannan bidiyo ga jama'a ba; an nuna shi ne kawai ga manyan ƴan jam'iyya a watan Yuni na 2012, a cewar Dakta Cheong. Daga baya kuma sai aka fara yaɗa shi a tsakanin talakawa ta hanyar na'urorin USB da aka shigo da su ba bisa ƙa'ida ba.
"Lokacin da ya fara yaɗuwa... sha'awar mutane game da Ko Yong Hui ta ƙaru matuƙa, don haka gwamnati ta gaggauta janye [bidiyon]," in ji shi, yana mai ƙara da cewa tarihinta na iya sa a fara shakkar halaccin mulkin ƙasar.

To, ta yaya ɗan na biyu na uwargida – wato ƙaramin ɗan Kim Jong Il – ya samu gadon mulki?
Masana tarihi da dama sun yi imanin cewa Ko ce ta shirya Kim Jong Un ya gaji mulki.
Ƙanwarta ta gaya mata cewa dole ne ya zama shugaban gaba, in ba haka ba iyalinsu za su shiga haɗari, kamar yadda fitacciyar 'yar jarida Anna Fifield ta rubuta a littafinta The Great Successor: The Secret Rise and Rule of Kim Jong Un.
Babban dan Kim Jong Il, Kim Jong Nam, ya rasa tagomashi tun da wuri saboda ya riƙa ƙalubalantar tsarin gadon mulki na iyali a Koriya ta Arewa yana kuma goyon bayan sauye-sauye, in ji Goji, wanda suka yi ta mu'amala ta imel na tsawon shekaru.
Ra'ayoyin siyasar Jong Nam na iya kasancewa sakamakon shekaru goma da ya yi yana karatu a ƙasashen waje, kuma yana iya magana da Faransanci da Turanci sosai.
Haka kuma ya shahara da yawon shaƙatawa da halin jin daɗi saboda yawan ziyararsa gidajen caca da rayuwar tafiye-tafiye.
Bayan dawowar Jong Nam Koriya ta Arewa, jita-jita cewa Ko Yong Hui na shirya 'ya'yanta su gaji mulki ya ci gaba.
Amma an cire ɗanta na fari, Jong Chul, daga jerin masu gadon mulki saboda tsananin shan ƙwaya, a cewar littafin Ryu, tsohon jami'in diflomasiyya. Ya ce Jong Chul ma ya taɓa buga ƙofarsa da sassafe yana neman ƙwaya.
Masana sun ce Kim Jong Un ya zama ɗan lele a wurin mahaifinsa saboda kwarewarsa ta shugabanci da kuma halinsa na nuna gogayya.
An ɗorawa ƙanwar Ko da mijinta alhakin kula da Kim da babban dan'uwansa yayin da suke karatu a Switzerland.
Amma ma'auratan sun tsere zuwa Amurka a shekarar 1998 bayan an gano Ko na da cutar sankarar mama. Sun ji tsoron cewa "gwamnatin ba za ta ƙara buƙatar su ba," kamar yadda wani rahoton Washington Post na 2016 ya nuna bayan an yi hira da su.
Ko da yake Kim Jong Un ya zama magaji, tsoron nasu ya kasance da ma'ana. Bayan ya hau mulki, an kashe ɗaya daga cikin kawunnansa, yayin da aka kashe Jong Nam a Malaysia.
'Yaɗuwar jita-jita kamar wutar daji'

Asalin hoton, Yoji Gomi
Ko ta rasu kafin Kim Jong Il, amma mutuwarta – wadda ta faru a wani asibiti a Paris – ba ta samu wata muhimmiyar kulawa a kafofin yada labaran gwamnatin Koriya ta Arewa ba.
Sai dai masana na ganin cewa sirrin da ke tattare da asalin Kim Jong Un na iya zama dalilin da ya sa ba a ayyana ranar haihuwarsa a matsayin hutun ƙasa ba, saɓanin na kakansa da mahaifinsa.
Jawo hankali kan haihuwarsa na iya haifar da tambayoyi masu sarƙaƙiya game da mahaifiyarsa da kuma dalilin da ya sa aka raina shi a wajen Pyongyang.
"Bayyana gaskiya na iya yaɗa shakku cikin sauri kamar wutar daji," in ji Kim, mai bincike.
Ko da yake yana saman tsarin mulki na Koriya ta Arewa, a zahiri matsayin Kim Jong Un mai alaƙa da asalinsa zai iya shafar darajarsa inda za ta iya yin ƙasa kaɗan a tsarin zamantakewa saboda alaƙarsa da 'yan Koriya na Zainichi da kuma masu gudun hijira, kamar yadda Ryu, tsohon jami'in diflomasiyya, ya rubuta.
Sirrin da ke kewaye da zuriyarsa na iya zama ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Kim Jong Un ya fito fili da matarsa Ri Sol Ju tun farkon mulkinsa, yayin da yake ƙoƙarin shirya matashiyar 'yarsa Ju Ae a matsayin mai iya gadonsa a gaba, kamar yadda Cheong ya bayyana.
Ri, wadda tsohuwar mawaƙiya ce a wata fitacciyar ƙungiyar rawa da waƙa, ana ganin ta fito daga iyali mai matsakaicin hali zuwa ɗaukaka a Pyongyang, a cewar hukumar leken asiri ta Koriya ta Kudu. Wasu rahotanni sun nuna cewa mahaifinta farfesa ne a jami'a.
An kuma tura ta China domin karatun waƙa ta gargajiya daga ɓangaren gwamnati – alamar cewa tana da kyakkyawan matsayin mai alaƙa da asali na "songbun".
Shin Kim Jong Un zai taɓa bayyana asalin mahaifiyarsa?
Wannan zai kasance aiki mai wahala, ko da ga yaɗa farfaganda a Koriya ta Arewa.









