Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Asalin hoton, Getty images/Tasnim
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da hare-haren da Amurka ta kai a gaɓar tekun yankin Sirik da tsibirin Qeshm,” inda ta bayyana hakan a matsayin “keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta 10 ga Afrilu da aka cimma.
A cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar ta ce “ci gaba da nuna ƙiyayya da tsokana daga gwamnatin Amurka” na nuna rashin bin dokokin ƙasa da ƙasa da kuma Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ta ƙara da cewa hakan na nuna cewa “Amurka ba ta da niyyar rage tashin hankali ko komawa hanyar zaman lafiya mai ɗorewa.”
Sanarwar ta jaddada cewa Iran na da cikakken haƙƙin kare kanta, tare da kira ga ƙasashen yankin da su mutunta ƙa’idar kyakkyawar makwabtaka, tare da gargaɗin kada su bari “ɓangarorin da ke da mugun nufi” su yi amfani da “ƙasashensu ko wuraren aikinsu” wajen kai hare-hare.
A gefe guda, dakarun juyin juya halin Iran sun ce sun kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Kuwait da kuma hedikwatar Rukuni na Biyar na rundunar sojin ruwa ta Amurka a Bahrain da makamai masu linzami da jiragen marasa matuƙa.
Sai dai sojojin Amurka, Kuwait da Bahrain sun ce sun yi nasarar kakkao dukkanin makaman da aka harba.
Kuwait da Bahrain sun kuma yi allawadai da harin da Iran ta kai.



















