Yadda aka sace ɗalibai sama da 2,000 a shekaru biyu a Najeriya

Bindiga

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 8

A Najeriya, ana cigaba da tattaunawa kan sace ɗaliban wasu makarantu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya da kuma jihar Oyo da ke kudu maso yammacin kasar.

A jihar Borno, bayanai sun ce gomman ɗalibai sun ɓata a wasu makarantu da ke cikin haraba guda, bayan wani hari da 'yan Boko Haram suka kai garin Mussa na ƙaramar hukumar Askira Uba.

A jihar ta Oyo kuma, hukumomi ne suka tabbatar cewa ƴanbindiga sun kai hari kan wasu makarantu guda biyu a garin Ahoro-Esinle, inda suka hallaka wani malami kuma suka sace ɗalibai.

Lamarin ya ɗauki hankali matuƙa gaya, inda har malaman makaranta suka yi zanga-zanga tare da rufe makarantu, suna masu kira ga gwamnati da ta ceto yaran, sannan ta ba su tabbacin tsaro.

Ana fara buɗe ido da garkuwa da ɗalibai ƴan makaranta ne a zamanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, inda mayaƙan Boko Haram suka sace ƴan makarantar Chibok.

Tun daga lokacin ne mayaƙan Boko Haram da ƴanbindiga suka cigaba da sace ɗalibai, inda zuwa yanzu aka sace ɗalibai a makarantu aƙalla 25 a jihohi daba-daban na Najeriya, tare da sace ɗalibai aƙalla 2,000.

BBC ta tattara bayanan wasu makarantu da aka sace, musamman waɗanda suka fi jan hankali ta hanyar tattara rahotannin jaridu irin su ICiR da Premium Times.

Makarantar Chibok

A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne mayaƙan Boko Haram suka kai wani hari makarantar sakandaren mata da ke Chibok a jihar Borno, inda suka sace ɗalibai masu yawa.

Mayaƙan ɗauke da manyan bindigoyi sun shiga garin da tsakar dare suka tashi mazauna da ƙarar harbi kafin su kutsa cikin ɗakunan kwanan ɗalibai suka loda su a motoci sannan suka yi awon gaba da ƴanmata 276.

Wannan hari shi ne irin sa na farko da mahara suka sace ɗalibai a makaranta, batun satar ɗaliban ya ja hankalin duniya.

Hakan ya sa ƙasashen duniya suka yi ta sukar gwamnatin Najeriya ta wancan lokacin bisa rashin ɗaukar mataki, inda aka fara gangamin #BringBackOurGirl a shafin Twitter wanda ke nufin 'A dawo da ƴaƴanmu mata'. An dai samu nasarar ceto da yawa daga cikin su.

Makarantar Legas

A watan Mayun shekarar 2017, ƴanbindiga suka sace ɗalibai guda shida daga makarantar Lagos State Model College da ke garin Igbonla a jihar Legas.

An sake ɗaliban bayan kimanin kwana 65 a hannun masu garkuwar.

Sakandiren mata ta Dapchi

A zamanin tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, a daidai lokacin da yake ƙoƙarin ceto ɗaliban Chibok, sai kwatsam a watan Fabrairun 2018 ƴan Boko Haram kai hari makarantar mata da ke garin Dapchi na jihar Yobe sannan suka sace ɗalibai 110.

Lamarin ya faru ne kusan shekara huɗu bayan sace ƴanmatan makarantar Chibok.

An saki 104 daga cikinsu a watan Maris na 2018 yayin da biyar suka mutu a ranar da aka sace su, amma har yanzu yarinya ɗaya mai suna Leah Sharibu na hannun mayakan na Boko Haram, inda rahotanni ke su ƙi sakinta ne 'ta ce ba za ta bar addininta na Kirista ba'.

Makarantar Ƙanƙara

A shekarar 2020 ce ƴanbindiga da ke arewa maso yammacin Najeriya suka fara aron salon na sace ɗalibai, inda a watan Disamban 2020 aka kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta maza da ke garin Ƙankara na jihar Katsina aka sace ɗalibai sama da 300.

Sai dai daga bisani an samu nasarar ceto ɗaliban, inda ƴanbindigar suka sake su bayan hukumomin jihohin Zamfara da Katsina sun shiga tsakani, kamar yadda gwamnatin jihar Katsina ta sanar a lokacin.

Kwalejin Kagara

A ranar Talata 16 ga watan Fabrairun 2021 ne ƴanbindiga suka kai hari a makarantar sakandaren maza da ke garin Kagara a jihar Neja, inda suka sace dalibai da dama.

Gwamnan jihar Neja na lokacin, Abubakar Bello ya ce an kwashe dalibai 27 da ma'aikata uku haɗi da iyalansu su goma 12.

Makarantar mata ta Jangebe

Jangebe

Asalin hoton, Getty Images

A cikin watan Fabrairun 2021 ma ƴan bindiga sun kai hari makarantar kwana ta mata da ke garin Jangeɓe a jihar Zamfara wato GGSS Jangebe, inda suka sace kimanin ɗalibai 317.

Wani shaida a lokacin ya tabbatar wa BBC cewa an sace 'yan mata kusan 300 ne sakamakon kirga dukkan 'yan makarantar da suka rage bayan ɓarayin sun tafi.

Shi ma dai wannan hari ya ja hankulan mutane da dama a ciki da wajen Najeriya, inda aka riƙa kiraye-kirayen samar da jami'an tsaro a harabar makarantun kwana domin bai wa ɗalibai tsaro.

Harin ya sa gwamnatin jihar ta rufe mafi yawan makarantun kwana da ke nesa da gari.

Makarantar Tegina

A ranar 30 ga watan Mayun 2021 ne ƴanbindiga suka sace ɗaliban makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko Islamic School da ke garin Tegina, inda suka sace ɗalibai kusan 150.

A wata sanarwa da gwamantin jihar ta fitar a wancan lokacin, ta ce an harbi mutum biyu lokacin harin kuma an tabbatar da mutuwar ɗaya daga ciki, yayin da guda ɗaya ke cikin mawuyacin hali.

A lokacin, shugaban makarantar ya shaida wa BBC cewa akwai sama da ɗalibai 200 a cikin makarantar lokacin da ƴan bindigar suka shiga cikin harabar makarantar amma "adadin ɗaliban makarantar shi ne 302."

Makarantar Bethel Baptist Kaduna

A ranar 5 ga watan Yulin 2021 ne ƴanbindiga suka kutsa makarantar sakandire ta kwana ta Bethel Baptist da ke jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da ɗalibai fiye da 120.

Masu garkuwar sun saki ɗalibai a hankali, inda suka fara da sakin ɗalibai 28 a ranar Lahadi 25 ga watan Yuli, inda kuma suka saki sauran a watannin Agusta da Satumba da kuma Oktoba.

Kwalejin gandun daji ta Afaka

A watan Maris na 2021 ne ƴanbindiga suka kutsa kwalejin horas da harkokin noma da gandun daji wato Federal College of Forestry Mechanisation da ke Afaja a ƙarnar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda suka sace ɗalibai kimanin 30.

Ƴan bindigan sun afka wa makarantar ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare, lokacin da ɗaliban ke shirin kwanciya barci.

Jami'ar Greenfield Kaduna

GREENFIELD

Asalin hoton, GREENFIELD UNIVERSITY

A watan Afrilun 2021 ne kuma ake samun aukuwar satar ɗalibai a jihar Kaduna, inda ƴanbindiga suka kai hari a Jami'ar Greenfield mai zaman kanta da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja suka sace ɗalibai da dama.

An dai sace ɗaliban ne - da suka haɗa da maza da mata - daga ɗakunansu a lokacin da suka barci.

Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli

A watan Yunin na 2021 ne kuma ƴanbindiga suka ɓalla ƙofar shiga kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ke birnin Zazzau a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutum 10 da suka haɗa da malamai guda biyu da ɗalibai 8.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa an sak su duka daga bisa bayan an biya kuɗin fansa.

Kwalejin Tarayya ta Yauri

A watan Yunin 2021 suka ƙaddamar da hari a makarantar ɗalibai ta FGC Yauri da ke jihar Kebbi, inda suka yi garkuwa da ɗalibai masu yawa.

Bayanai sun bayyana cewa ƴanbindigar sun ci ƙarfin ƴansandan da ke gadin makarantar sannan suka ƙwace motoci ƙirar Toyota Hilux daga wurinsu suka zuba ɗaliban a ciki sannan suka tafi da su.

Firamaren Alwaza, Nassarawa

A watan Janairun 2023ne ƴanbindiga suka far wa makarantar firamare ta garin Alwaza da ke jihar Nassarawa inda suka yi awon gaba da ɗalibai guda shida da rahotanni suka ce shekarunsu ba su wuce bakwai da takwas ba.

Ƴan bindigar dai sun yi garkuwa da ɗaliban ne a kan hanyar ƴan makarantar ta zuwa makaranta da misalin ƙarfe bakwai na safe.

Ƴansanda sun ce sun ceto su bayan ƙaddamar da aikin ceto.

Ɗaliban jami'ar tarayya ta Dutsimma

A watan Oktoban 2023 ne kuma ƴanbindiga suka sace kimanin ɗalibai biyar na jami'ar tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina.

BBC ta gano cewa lamarin ya faru ne a cikin dare da misalin karfe biyu a ɗakunan kwanan da ɗalibai ke kamawa a wajen makarantar.

Ɗaliban jami'ar tarayya ta Gusau

A watan Satumban 2023 ne ƴanbindiga suka kai hari a gidajen kwanan ɗaliban Jami'ar Tarayya ta Gusau a yankin Sabon Gida da ke jihar, inda rahotanni suka nuna sun sace ɗalibai kusan 22.

Ƴan bindigar waɗanda suka isa unguwar Sabon Gida da tsakar dare, sun rinƙa harbe-harbe kafin su yi awon-gaba da ɗaliban.

Makarantar Kuriga

A watan Maris na shekarar 2024 ne ƴanbindiga suka sace ɗaliban firamare da na sakandare kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.

Wani malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi wanda ya kuɓuta ne ya tabbatar da adadin ɗaliban da aka sace a lokacin.

Malamin ya ce an ɗauki ɗaliban makarantar sakandire kimanin 187, sai kuma na Firamare 125, aka kaɗa su daji, sai dai malamin ya ce da suka fara tafiya shi da wasu ɗalibai kimanin 25 sun kuɓuta.

Islamiyyar Gidan Bakuso

A watan Maris na shekarar 2024 ne ƴanbindiga suka tsallaka makatantar Islamiyya ta kwana, inda suka sace ɗalibai 15.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin da tsakar dare a daidai lokacin da ɗaliban suke kwance suna barci.

Makarantar Daarul Kitab

A wani harin da jaridar Premium Times ta ruwaito, an sace ɗalibai 26 a cibiyar Daarul Kitab da ke ƙaramar hukumar Adavi ta jihar Kogi.

Sakandiren ƴan mata ta Maga

A ranar Litinin 17 ga watan Nuwamban 2025 ne ƴanbindiga suka sace ƴan mata ɗalibai 25 daga makarnatar kwana da ke garin Maga na ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.

Bayanai sun ce maharan sun far wa makarantar ɗauke da muggan makamai inda suka yi ta harbi kafin daga bisani su tafi da ɗaliban.

Ɗaya daga cikin malaman makarantar da ya zanta da BBC ya kuma buƙaci a sakaya sunansa ya ce maharan sun kashe malami guda da maigadin makarantar a lokacin harin.

Sakandiren St. Mary's jihar Neja

A ranar Alhamis 20 ga watan Nuwamban 2025 ne wasu ƴanbindiga suka kutsa makarantar sakandire ta St. Mary's inda suka yi awon gaba da ɗaliban da ba tabbatar da yawansu ba.

Cikin wata sanarwa da cocin St. Mary's ta fitar ta ce maharan sun ƙaddamar da harin ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 3:00 na dare a cikin makarantar.

Cocin ta ce lamarin ya haifar da tashin hankali da ruɗani a cikin hotuna.

Haka kuma cocin ta ce ta yi matuƙar damuwa da harin, tare da yin Allah wadai da shi da kuma kiran al'umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami'an tsaro haɗin kai domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.

Ɗaliban jami'ar Lafiya

A watan Mayun 2026 ne ƴanbindiga suka sace ɗaliban jami'a a jihar Nasarawa, inda rahotanni suka nuna cewa ɗalibai shida aka sace, kuma suna karatu ne a tsangayar injiyanci.

Jihar Oyo

A jihar Oyo hukumomi sun tabbatar da ƴanbindiga sun kai hari kan wasu makarantu guda biyu a garin Ahoro-Esinle, inda suka sace ɗalibai 46.

Lamarin ya matuƙar jan hankali

Makarantar Borno

A watan Mayun 2026 ne mahara da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram ne suka sace ɗalibai sama 50 a garin Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira-Uba da ke jihar Borno.

An sace ɗaliban ne daga makarantar sakandaren gwamnati da makarantar firamaren gwamnati ta SUBEB.