Alamu na nuna Kim Jong Un na shirya ƴarsa domin ta gaje shi

Asalin hoton, Reuters / EPA / BBC
- Marubuci, Sangmi Han
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Korean
- Aiko rahoto daga, Seoul
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Yarinyar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na cigaba da jan hankali, musamman ganin yadda take gudanar da rayuwar ƙasaita.
Sai dai yadda ake mata kallon yarinya matashiya, irin shigar da take yi da irin rayuwar da take yi, sai ake kallon Kim Ju Ae ta fara kama hanyar zama wadda za ta maye gurbin shugaban mai cikakken iko.
Rahotanni na cewa an haife ta ne a shekarar 2013, amma an fara jin ɗuriyarta ne a lokacin da ta kai shekara 9.
A watan Nuwamban 2022 ne aka fara ganinta tare da mahaifinta suna rangadin wasu makamai masu linzami.

Asalin hoton, Reuters
Tun daga lokacin ne ta fara jan hankali a ƙasar, duk da yanzu ta ƙara faɗaɗa yadda take shiga ta nuna isa da ƙasaita.
A 2020, Koriya ta Arewa ta ɗabbaƙa dokar da ta kira "Reactionary Ideology and Culture Rejection Act" domin hanawa ko taƙaita shiga da amfani da al'adun turawan ko ƙasashen waje.
Amma a shekarar 2023, kafar talabijin ɗin ƙasar ta fitar da wani bidiyo na Ju Ae tare da mahaifinta sanye da farar rigar sanyi da aka ruwaito cewa farashinta ya kai dala 1,900 da aka sayo daga kamfanin sayar da kayan ado na Christian Diro na Faransa.

Asalin hoton, Reuters
Bayan shekara ɗaya kuma, sai aka ga Ju Ae sanye da wata babbar bulawus a wani babban taro da aka yi a babban birnin ƙasar, Pyongyang.
Daga bisani an saki wani faifan bidiyo inda aka ciki aka soki yanayin shigarta, tare da gargaɗin cewa gashinta ya saɓa da al'adun ƙasar.

Asalin hoton, News1
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma a yanzu wasu sun fara kwaiwakyon salon shigar Ju Ae ta ƙasaita a sassan ƙasar.
"Yanzu zamani na canja, komai na canja cikin sauri," in ji Joung Eunlee, shugaban sashen bincike a cibiyar haɗin kan Koriya ta Arewa.
"Tun daga shekarar 2010, adadin masu zuwa ƙasashen waje suna aiki suna samun kuɗaɗen ƙasashen waje sun ƙaru sosai."
Kusan ƴan Koriya ta Arewa 2,000 ne suka kasance a China a lokacin annobar Covid-19, sannan lokacin da "suka koma birnin Pyongyang... sai suka koma da al'adun da suka koya a can."
"A shekarun baya, kayayyakin ado na ƙasaita na zuwa ne kawai daga kamfanin Zainichi na Japan. Amma yanzu alamu na nuna cewa ƴan Koriya ta Arewa sun fara sabawa da kayayyakin ƙasashen waje."
"Kasancewar jakukkuna da takalma suna da tsada (saboda fasaƙaurinsu ake yi zuwa ƙasar) sai ya zama an fi cin kasuwar turare a ƙasar a yanzu."
Amma dai ba Ju Ae ba ca ta fara fice da ado da shiga ta ƙasaita a zuriyarsu.
"Alamu na nuna cewa Ju na shiga ne da salo irin na mahaifiyarta Ri Sol Ju," in ji mataimakin daraktan cibiyar Sejong, Cheong Seong-chang.

Asalin hoton, Reuters
"Ta hanyar amfani da shiga irin ta ƙasashen turai, Ju Ae da Ri Sol Ju na zama na daban, inda suka bayyana cewa suna da bambanci da sauran ƴan ƙasar. Abin da ya sa kuma suke iya yin hakan ba tare da damuwa bai wuce damar da suke da ita."

Asalin hoton, Reuters
Haka kuma ba wai a wajen mahaifiyarta ba ne kawai Ju Ae ta fara koyon kwalliya ta ƙasaita.

Asalin hoton, Reuters
''Duk an hana sanya wandon jeans a Koriya ta Arewa saboda shigar turawa ne, ana ganin Kim Jong Un yana sanyawa,'' in ji Farfesa Lee Woo-yong na Jami'ar North Korean.
''Duk yadda aka hana amfani da al'adun ƙasashen waje ko kuma aka ɗabbaƙa dokoki, Koriya ta Arewa ƙasa ce babu abin da ba zai yiwu ba matuƙar shugaban ƙasar ya ga damar aikatawa."

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
"The limitations young Kim Jong Un faced as a successor, such as his lack of experience and age, could be offset solely by the fact that he resembled Kim Il Sung.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu haka a Koriya ta Arewa ana yi wa Ju Ae kallon sarauniya, kuma an fara mata wannan laƙabin ne saboda alamar da ake gani ta gadon mulki.

Asalin hoton, EPA
"Manyan masu faɗa a gwamnatin Koriya ta Arewa sun kasance suna yi wa ƴar uwar shugaban ƙasar mai suna Kim Yo Jong laƙaci da sarauniya kafin a haifi Kim Ju Ae," in ji Ryu Hyun-woo, tsohon muƙaddashin ambasan Koriya ta Arewa a Kuwaita, wanda ya koma Koriya ta Kudu.
Hyunjung Kim da Andrew Webb da Stephen Hawkes ne suka tace labarin.











