"DPO ne ya cire wa matata hijabi, ya tura ta kan titi": Mijin da aka kashe matarsa a Marabar Jos

Asalin hoton, Family
"Tun ana saura kwana biyu ta rasu nake jin gabana yana faɗuwa amma ina tsoron na faɗa mata saboda kada ta tayar da hankalinta," in ji Aliyu Muhammad, wanda a ranar Lahadi ya iske gawar matarsa Ummulkhairi ƙone kan titi, bayan mutane sun zarge ta da satar yara.
Aliyu ya tattauna da BBC ne kwana ɗaya bayan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, kan yadda mutane suka kashe tare da ƙona wata mata a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Mutumin - wanda ke aikin kanikanci - ya shaida wa BBC, cewa sun yi sallama da matarsa da safe: "lokacin da zan fita, ta ce min suna da wa'azi a makarantar Malama Mardiyya," - wata makarantar Islamiyya da ke garin, yayin da shi kuma ya kama hanya zuwa wurin aiki.
Sai dai wannan ita ce rabuwa ta ƙarshe tsakanin mata da mijin, waɗanda suka kwashe shekara 14 a tare, inda suka haifi ƴaƴa huɗu - biyu maza, biyu mata.
Ya bayyana cewa kimanin ƙarfe 11 na safe aka kira shi kan cewa matarsa tana gidan mai unguwa, bayan an kama ta da zargin kasancewa mai satar yara.
Duk da cewa Aliyu ya tura abokinsa zuwa gidan mai unguwa, amma tuni mutane suka cika ƙofar gidan suna neman a ba su ita domin su hukunta ta, bayan zargin ta da satar yara.
Yadda abin ya faru
Bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda cincirindon mutane suka yi dandazo a bakin ofishin ƴansanda na Marabar Jos, suna neman a miƙa musu Ummulkhairi.
A Najeriya, sau da dama mutane ba su da ƙarfin gwiwa kan cewa hukumomi za su hukunta masu laifi, inda suke zargin cewa 'duk mai laifin da ya je hannun ƴansanda, to ya tsira', lamarin da ba a kodayaushe yakan kasance hakan ba.
Wannan ne ya sanya mutanen garin, wadanda a cewar rahotanni ke fama da matsalar satar yara a baya-bayan nan, suka nace kan dole sai sun ɗauki mataki a kan matar duk da cewa babu wata shaida da ta tabbatar da cewa ita mai satar yara ce.
A ƙarshen bidiyon, da kuma hotunan da aka riƙa yadawa daga baya, an ga yadda aka ƙona gawar matar a kan titi, yayin da aka ɗora mata wani babur.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Mun shirya wa'azin goron sallah, inda muka yi wa'azi 11 kafin daga baya muka jinkirta, daga nan sai muka shirya yin wannan wa'azin", in ji Shugaban kwamitin wa'azin matasa na Marabar Jos, Jamilu Tahir.
Malamin wanda ya ce marigayiyar ɗalibarsa ce, ya ce ta kama hanya zuwa wurin wa'azin ne bayan sauran mata ƴan'uwanta sun wuce.
"Lokacin da ta zo unguwar, sai ta tambayi ina ne ake yin wa'azi (makarantar malama Saliha) saboda makarantun guda biyu ne - makarantar malama Saliha da makarantar malama Mardiyya.
Ya ce mutanen da ta tambaya sun fada mata cewa ana wa'azin ne a makarantar Malama Mardiyya.
A cewar Malam Tahir sai wani yaro ya nemi ya yi wa marigayiyar jagora zuwa makarantar Malama Mardiyya to amma sai wata mata da ke kusa ta nuna adawa da hakan.
Sai ta ce: "Irin waɗannan masu niƙabin ne masu satar yara, sai kawai mutane suka sa ihu, ana cewa mai satar yara," a cewar Tahir.
Daga nan ne aka samu wasu suka kai ta gidan mai unguwa, kafin daga baya aka kai ta ofishin ƴansanda.
A ranar Lahadi rundunar ƴansanda ta Najeriya reshen jihar Kaduna ta fitar da wata sanarwa tana Allah wadai da kisan da aka yi wa matar.
Sanarwar, wadda ta samu sa hannun mai magana da yawunta DSP Mansur Hassan ta ce "duk da yanƙurin da jani'an ƴansanda suka yi na bai wa matar kariya, amma an ci ƙarfinsu, inda dandazon mutane suka kashe ta tare da cinna mata wuta.
Ana zargin ƴansanda
Mijin marigayiyar ya shaida wa BBC cewa DPO ne ya fitar da ita daga ofishin ƴansandan abin da ya sa jama'a suka samu damar yi mata kisan gilla.
"DPO ne ya kama ta, ya cire mata hijabi, ya tura ta kan titi, sannan ya juya ya koma ofishinsa," in ji mijin marigayiya Ummulkhair.
Shi ma mutumin da ya yi ƙoƙarin ceton ran Ummulkhairi ya kuma jagoranci kai ta ofishin ƴansanda,Sulaiman Isah, ya tabbatar da cewa "DPO ne ya miƙa ta wurin al'umma".
BBC ta tuntunɓi ƴansanda domin jin martaninsu game da wannan zargi.
Mai magana da yawun rundunar, Mansir Hassan ya ce mutane ne suka fi ƙarfin ƴansanda suka ƙwace ta a hannunsu.
Ya kuma musanta zargin, inda ya ce: "Babu yadda za a yi DPO ya miƙa wa mutane matar.
"Shiga suka yi suka ƙwato ta da ƙarfi, kuma har yanzu muna ci gaba da bincike." a cewar DSP Hassan.
Rundunar ƴansanda ta kuma ce yanzu haka an kama mutanen da ake zargi da hannu wajen kisan matar.
'Matata mutuniyar kirki ce'
Aliyu Muhammad ya ce matarsa mutuniyar kirki ce: "Ɗaliba ce, kowa ya san ta, idan ka ga ta fita daga gidana to za ta je wa'azi ne ko kuma wurin walima ta aure.
"Ko a mafarki," bai taɓa tunanin za a yi mata irin wannan zargi ba, a cewar Aliyu.
Ya ce a lokacin da ya isa wurin da aka ƙona matarsa, ya ji abin "kamar a mafarki".
"Lokacin da je wurin sai na ga gawarta a kan titi, an ƙona ta, an sa mata ganye, jikina ma ba ya riƙe ni".
Aliyu wanda ke zantawa da BBC cikin murya mai ciki da takaici ya ƙara da cewa "mashin suka ɗora a kanta suka ƙona ta."









