Wane ne Andy Burnham, mutumin da ake son naɗawa sabon Firaministan Birtaniya?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Becky Morton
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Political reporter
- Marubuci, James Gregory
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Political reporter
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Sau biyu Andy Burnham na neman muƙamin shugaban Labour a Birtaniya amma bai yi nasara ba.
Wataƙila yanzu zai iya dacewa a karo na uku, biyo bayan murabus ɗin Sir Keir Starmer daga muƙamin Firaministan Birtaniya, inda yawancin ƴan majalisar Labour ke goyon bayan Burnham mai wakiltar mazaɓar Makerfield, a wannan muƙamin.
Burnham ya tabbatar da cewa yana niyyar sake neman muƙamin, kuma akwai yiwuwar ya samu kujerar sakamakon goyon bayan da yake samu daga Wes Streeting, tsohon mai kula da lafiyar Starmer, wanda shi ma yake neman muƙamin.
Babbar nasarar da Burnham ya samu ta biyo bayan lashe zaɓen cike gurbi da ya yi a makon da ya gabata.
Tsohon magajin garin Manchester ya ƙara wa jam'iyyar farin jini zuwa samun ƙarin kaso 55% na ƙuri'u daga 45% a shekarar 2024.
An rantsar da Andy Burnham a matsayin sabon ɗan Majalisar Dokokin Birtaniya, inda ya samu kyakkyawar tarba daga 'yan jam'iyyar Labour a zauren majalisar.
Amma ya aka yi yake cikin na gaba-gaba a waɗanda ake sa ran za su samu muƙamin.

Asalin hoton, Getty Images
Burnham ya fara sha'awar siyasa tun yana yaro
An haifi Andy Burnham a birnin Liverpool a shekarar 1970, amma ya taso ne a ƙauyen Culcheth da ke lardin Cheshire kusa da Warrington.
Mahaifinsa injiniya ne a kamfanin sadarwa na BT Group, yayin da mahaifiyarsa ke aiki a matsayin ma'aikaciyar jinya a asibiti.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Andy Burnham ya taɓa bayyana cewa ya samu ƙwarin gwiwar shiga jam'iyyar Labour ne tun yana da shekara 14 bayan kallon shirin talabijin na BBC mai suna Boys from the Blackstuff, wanda ya yi bayani kan wahalhalun rayuwar marasa aikin yi a Liverpool.
Masoyin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton F.C. tun yana ƙarami, inda abokansa ke kallonsa a matsayin masoyi wasanni kuma yana son gasa. Haka kuma ya iya wasan cricket sosai inda yake cikin tawagar ƴan wasa na ɗaliban a makarantar Lancashire.
A lokacin da yake sakandaren Katolika ta yankinsu, malamin Turancinsa ya tuna yadda Burnham ya tsaya takara a wani zaɓen gwaji na makaranta a matsayin ɗan takarar Labour, inda ya yi nasara da gagarumin rinjaye.
Shi da ƴan'uwansa maza biyu ne suka zama na farko a gidansu da suka samu damar shiga jami'a, inda Burnham ya karanci Turanci a jami'ar Cambridge.
A cikin littafinsa mai suna Head North, Burnham ya bayyana cewa a farkon rayuwarsa ta jami'a ya sha fama da jin kamar ba ya cikin mutanen wurin, har ma yana ganin kansa tamkar bai dace da muhallin ba.
Sai dai ya ce yana sha'awar ga waƙoƙin indie daga arewacin Ingila, musamman na ƙungiyoyin The Smiths da The Stone Roses, kuma hakan ya taimaka masa wajen samun ƙima da kuma ƙarfafa masa gwiwa a jami'a.

Asalin hoton, Getty Images
Yadda ya zama Magajin Garin Manchester
Bayan kammala karatunsa na jami'a, ya fara aikin jarida, inda ya yi aiki da mujallar kasuwanci ta Tank World da Passenger World Management.
A lokacin da yake tsakanin shekara 20, ya samu damar shiga harkokin siyasa lokacin da ya fara aiki a matsayin mai bincike ga marigayiya Tessa Jowell, wadda a lokacin take wakiltar mazaɓar Dulwich da West Norwood a majalisar dokokin Birtaniya. Daga baya Jowell ta zama minista a gwamnatocin Tony Blair da Gordon Brown.
Burnham ya yi saurin samun karɓuwa a siyasa, inda ya zama mai ba wa Ministan Al'adu Chris Smith shawara kafin a zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dokoki mai wakiltar mazaɓarsa ta Leigh da ke Greater Manchester a shekarar 2001.
Da farko ya yi aiki a matsayin ƙaramin minista a gwamnatin Blair, sannan a lokacin gwamnatin Brown ya shiga majalisar ministoci inda ya riƙe muƙaman Babban Sakataren Ma'aikatar Kuɗi, da ta Al'adu da kuma ta Lafiya.
A lokacin da yake Sakataren Al'adu, Kafafen Yaɗa Labarai da Wasanni, Burnham ya sha suka daga mahalarta wani taron tunawa da cika shekaru 20 da ibtila'in Hillsborough.
A shekarar 1989, magoya bayan Liverpool 97 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsutsun da ya auku a filin wasa.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2010, bayan da Brown ya yi murabus sakamakon kayen da jam'iyyar Labour ta sha a babban zaɓen ƙasar, Burnham ya yi takarar shugabancin jam'iyyar.
Sai dai ya zo na huɗu cikin 'yan takara biyar, inda Ed Miliband ya yi nasarar lashe zaɓen. Duk da rashin nasarar, Burnham ya shafe shekaru biyar masu zuwa yana ƙoƙarin ƙara kusanci da mambobin jam'iyyar da magoya bayanta.
A shekarar 2015 ya sake neman shugabancin Labour, amma Jeremy Corbyn ya kayar da shi.
Masu sukar Burnham sun sha zarginsa da sauya matsayinsa kan wasu batutuwan siyasa domin samun nasara.
A lokacin ƙuri'ar raba gardama kan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, Burnham yana cikin masu goyon bayan ci gaba da zama cikin ƙungiyar. Daga baya kuma ya bayyana cewa yana son ganin Birtaniya ta sake komawa Tarayyar Turai a rayuwarsa.
Sai dai yayin yaƙin neman zaɓen cike gurbi na Makerfield, ya ce ba zai mayar da batun sake komawa Tarayyar Turai a matsayin babban jigo ba, musamman ganin cewa yankin ya kada ƙuri'a sosai wajen goyon bayan Brexit.
Duk da cewa ana kallonsa a matsayin ɗan tsakiya mai ra'ayin Blair a Labour, Burnham ya yi aiki a majalisar ministoci ta Corbyn a matsayin sakataren harkokin cikin gida
A tsawon lokaci kuma, ra'ayoyinsa sun fara karkata, inda ya goyi bayan mayar da harkokin ruwa da makamashi ƙarƙashin ikon gwamnati.
Lokacin da wasu manyan jiga-jigan Labour suka yi murabus domin nuna rashin amincewa da shugabancin Corbyn a shekarar 2016, Burnham bai shiga cikinsu ba.
Maimakon haka, a shekarar 2017 ya ajiye kujerarsa ta ɗan majalisa domin neman zama magajin garin Manchester.
Ya lashe zaɓen da sama da kashi 60 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, sannan ya sake samun nasara da gagarumin rinjaye a 2021.
Yadda Burnham ya ƙara samun farin jini a Manchester
A matsayinsa na Magajin Garin Manchester, Burnham ya samu yabo daga mutane da dama saboda sauye-sauyen da ya kawo a tsarin sufurin yankin.
A ƙarƙashin shugabancinsa, Manchester ta zama yanki na farko a wajen London da ya dawo da harkokin motocin bas ƙarƙashin ikon gwamnati. Haka kuma an haɗa sufurin motocin bas da sauran hanyoyin sufuri a ƙarƙashin wani tsari guda mai suna "Bee Network".
Burnham ya kuma yi wasu alƙawura, ciki har da kawo ƙarshen matsalar mutanen da ke kwana a kan tituna a yankin kafin shekarar 2020. Sai dai duk da ƙoƙarin da aka yi, ba a cimma wannan buri ba.
Farin jininsa ya ƙaru sosai a lokacin Covid-19, lokacin da ya zargi gwamnatin jam'iyyar Conservative da nuna wariya da raini ga yankunan arewacin Ingila kan yadda ta aiwatar da dokokin kulle domin yaƙi da cutar.
Saɓanin ra'ayinsa da gwamnatin tarayya a wancan lokaci ya sa mutane da dama suka fara yi masa laƙabi da "Sarkin Arewa" (King of the North), saboda yadda ya kasance mai kare muradun yankunan arewacin Ingila.

Asalin hoton, PA Media
A duk lokacin da ake tarukan siyasa a ƙarshen shekarar 2025, Burnham ya fara nunawa a fili cewa yana da burin neman shugabancin jam'iyyar Labour.
Sai dai wasu daga cikin kalaman da ya yi sun jawo masa suka. Ya taɓa cewa gwamnati ta zama tamkar "mai bin umarnin kasuwannin hada-hadar kuɗi", inda ya buga misali da ƙa'idojin da ta ɗora wa kanta na takaita kashe kuɗi da karɓar bashi.
A watan Janairu, ya samu damar komawa Majalisar Dokokin Birtaniya bayan ɗan majalisar Manchester, Andrew Gwynne, ya sanar da ajiye kujerarsa, abin da ya sa aka gudanar da zaɓen cike gurbi a mazaɓar Gorton da Denton.
Amma shugabannin jam'iyyar Labour sun hana Burnham shiga takarar wannan kujera, matakin da aka ce ya samu amincewar Firaminista Keir Starmer.
Daga baya ne kuma al'amura suka sauya. A watan Mayun 2026, jam'iyyar Labour ta sha kashi a wasu zaɓuɓɓuka da aka gudanar a Ingila da Scotland da Wales, inda jam'iyyar Reform ke ƙara samun karɓuwa, har a yankunan da ake kallon a matsayin magoya bayan Burnham ne.
Wannan ya ƙara matsa lamba ga Starmer, inda wasu ƴan majalisar Labour suka fara kira da a samu sabon shugabanci, kuma tuni wasu ministoci suka fara yin murabus.
Ana wanan yanayi ne ɗan majalisar Labour mai wakiltar Makerfield, Josh Simons, ya sanar da cewa zai ajiye kujerarsa domin ba Burnham damar komawa majalisa da kuma neman shugabancin jam'iyyar.
Daga bisani Burnham ya zama ɗan takarar Labour a mazaɓar Makerfield, kuma ya yi nasarar lashe zaɓen cike gurbin, inda zai koma majalisar bayan shekaru yana jagorantar Manchester.










