Ƙasashe 10 da suka fi sayar da makamai a duniya a 2026

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mamadou Faye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Mafi yawan ƙasashen duniya da ba sa iya ƙera makaman da za su yi amfani da su kan buƙaci sayo maakaman ne daga ƙasashen duniya.
Kuma yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar rikice-rikice, ƙasashe da dama na ci gaba da tuɗaɗa domin sayen makaman a hannun ƙasashen da ke ƙera makaman.
Su kuwa ƙasashen da ke ƙera makaman kan sayar da su ne farashin da suka ga dama, kasancewar haja ce da ba a ko'ina ake samu ba.
Don haka ne kasuwar ke ci gaba da kasancewa a hannun manyan ƙasashen duniya mafiya ƙarfin soji.
A wannan muƙala mun kawo muku manyan ƙasashen duniya 10 da suka fi sayar da makamai a duniya, la'akari daga bayanai daga rahoton da Cibiyar Binciken Zaman Lafiya ta Duniya da ke Stockholm (SIPRI) ta wallafa ranar 9 ga watan Maris ɗin 2026.
1. Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta kasance kan gaba wajen sayar da makamai a duniya.
A cewar cibiyar SIPRI, Amurka ta sayar da makamai ga ƙasashe 99 tsakanin 2021 zuwa 2025, ciki har da ƙasashen Turai 35 da na yankin Amurka 18 da na Afirka 17 da na Asiya da yankin Fasifik da Gabas ta Tsakiya 12.
A cewar bayanan cibiyar ta SIPRI, Amurka ce ta fitar da kashi 42 cikin 100 na makaman da aka sayar tsakanin 2016 zuwa 2020, lamarin da ke nuna yadda ƙasar ta mamaye kasuwar cinikin makaman.
Nahiyar Turai ta kasance kan gaba wajen sayen makaman Amurka na tsawon shekara 20, inda take sayen kashi 38 cikin 100 na makaman da ƙasar ke sayarwa, sai kuma yankin Gabas ta Tsakiya da ke sayen kashi 33 ciin 100.
Ƙasar Saudiyya, wadda ke sayen kashi 12 cikin 100 na makaman Amurka, ita ce ƙasar da ta fi sayen makaman na Amurka.
SIPRI ta ce yanzu haka akwai jiragen yaƙi 460 samfurin F-35 da ke jiran aika su Turai bayan kammala cinikinsu.
2. Faransa

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Faransa da ke nahiyar Turai ce ta biyu cikin ƙasashen da suka fi sayar da makamai a duniya a 2026, inda take sayar da makaman ga ƙasashe 63.
Faransa ce ke fitar da kashi 9.8 na makaman da aka sayar a duniya tsakanin 2016 zuwa 2020.
Kamar dai Amurka, Turai ce ke sayen kusan kashi 80 cikin 100 na makaman Faransa, duk da cewa tana sayar da kaso mafi yawa ga wasu ɗaiɗaikun ƙasashe.
Dangane da ɗaiɗaikun ƙasashe kuwa Indiya da Masar da Girka da Qatarda kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ne suka fi sayen makaman Faransa.
Yanzu haka akwai jiragen saman yaƙi 180 da jiragen ruwan yaƙi 16 da aka kammala cinikinsu daga Faransa, ake kuma jiran a ƙera su domin kai su ƙasashen da suka saya.
3. Rasha

Asalin hoton, Getty Images
A baya Rasha ce ƙasa ta biyu da ta fi sayar da makamai a duniya, kafin matsayinta ya ragu a kasuwar makaman tun bayan mamayar Ukraine a 2022.
A yanzu haka Rasha ce ke da kashi 6.8 cikin 100 na makaman da ake sayarwa a duniya.
Amurka da Turai sun riƙa matsawa ƙasashen da ke sayen makaman Rasha cewa su daina.
Don haka ne yanzu ƙasashen da ke sayen makaman Rasha ba su fi uku ba, wato Indiya da China da kuma Beralus.
Haka kuma yayin da a yanzu ƙasasheh Indiya da China ke ƙera wa kansu mafi yawan makaman da suke buƙata, akwai yiyuwar Rasha za ta ƙara fuskantar koma-baya a cinikin makaman nata.
4. Jamus

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Jamus wadda ita ma ke Tarayyar Turai ce a matsayi na huɗu a jerin ƙasashen da suka fi sayar da makamai a duniya, inda take fitar da kashi 5.7 na makaman da ake sayarwa a duniya.
Ukraine ce ta fi kowace ƙasa sayen makaman Jamus, inda take sayen kashi 24 cikin 100 na makaman da take sayarwa.
Fiye da rabin makaman da Jamus ke ƙerawa tana sayar da su ne ga ƙasashen da ke wajen nahiyar Turai.
Ƙasar ta fi ƙwarewa a kera jiragen ruwa na yaƙi da tankoki da na'urorin tsaron sararin samaniya.
5. China

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar China da ke yankin Asiya ce ta kasance a matsayi na biyar cikin ƙasashen da suka fi sayar da makamai a duniya.
China ce ke sayar da kashi 5.6 cikin 100 na makaman da ake sayarwa a duniya.
Ƙasar Pakistan ce kan gaba wajen sayen makaman China, inda take sayen kashi 47 na makaman da China ke ƙerawa, daga nan sai Bangladesh.
Haka kuma China ta ƙaddamar da gagarumin cinikin makamai da nahiyar Afirka da kuma Kudancin Asiya.
6. Italiya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Italiya da ke nahiyar Turai ta ƙarfafa matsayinta a kasuwar cinikin makamai ta duniya, inda take a matsayi na 6.
Fiye da rabin makaman da Italiya ke sayarwa (kashi 59) na zuwa yankin Gabas ta Tsakiya ne, yayin da yankin Asiya da Oceania ke sayen kashi 16 cikin 100 na makaman, sai Turai da ke sayen kashi 13.
Italiya ta shahara wajen sayar da jiragen sama masu saukar ungulu, da jirage da kuma jiragen sama na horaswa.
7. Isra'ila

Asalin hoton, Getty Images
A cewar cibiyar SIPRI, Isra'ila ta zarce Birtaniya wajen sayar da makamai a duniya.
Kashi 4.4 cikin 100 na makaman da ake sayarwa a duniya, daga Isra'ila suke a cewar cibiyar.
Ƙasar ta ƙware wajen ƙera na'urorin tsaron sararin samaniya, da fasahar jirage marasa matuƙa.
Hakan ya nuna yadda duniya ke tsananin buƙatar tsaron sararin samaniya.
8. Birtaniya

Asalin hoton, Getty Images
Birtaniya ta ci gaba da riƙe matsayinta a wannan jeri, bayan da ta ƙarfafa masana'antunta na ƙera makamai.
Kashi 3.4 na makaman da ake sayarwa a duniya, daga Birtaniya suke.
Birtaniya ta ƙware wajen fitar da manyan jiragen ruwa na yaƙi da kuma jiragen sama na yaƙi.
Ƙasar na aiki da Amurka da ƙawayenta na NATO.
9. Koriya da Kudu

Asalin hoton, JUNG YEON-JE / AFP
Koriya ta Kudu ta ƙarfafa kanta a matsayin mai faɗa a ji a kasuwar makamai ta duniya.
Kashi 3 cikin 100 na makaman da ake sayarwa a duniya daga Koriya ta Kudu suke.
Mafi yawan makaman da Koriya da Kudu ke sayar, Turai ce ke sayensu, yayin da ƙasar Poland ke sayen kashi 46 na makaman.
A yankin Asiya kuma, Philippines ce kan gaba wajen sayen makaman an Koriya ta Kudu.
Koriya ta Kudu ta ƙware a fannin ƙera tankunan yaƙi, samfurin K2 da K9 howitzers da kuma jiragen sama samfurin FA-50.
10. Sifaniya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Sifaniya ce a matsayi na ƙarshe cikin wannan jeri, saboda irin yadda take ƙulla ƙawance da wasu ƙasashen Turai wajen ƙera wasu makaman.
Sifaniya ta ƙware a fannin ƙera jiragen sama na yaƙi da tankokin yaƙi, inda Ukraine da Turai ke sayen kaso mafi yawa na makaman.
Cinikin makamai na nuna yadda ƙasashen duniya suka rarrabu.
Yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar rikici, cinikin makamai zai ci gaba da sauya iko da ƙarfi tsakanin ƙasashen duniya.











