Dalilan da suka sa Keir Starmer zai yi murabus daga firaiministan Birtaniya

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Richard Wheeler
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Political reporter
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Firaiministan Birtaniya, Keir Starmer, ya sanar da cewa zai sauka daga muƙaminsa na jagoran firaiministan ƙasar da kuma jagoran jam'iyyar Labour, bayan ya fuskanci matsin lamba daga cikin jam'iyyarsa.
Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar, inda ya ce ya riga ya sanar wa Sarki Charles game da matakin da ya ɗauka.
Starmer ya ce kafin ya karɓi jagoranci, jam'iyyar Labour tana cikin wani hali na rauni a fannonin siyasa da tattalin arziki.
Duk da wannan, ya jaddada cewa ya yi aiki tuƙuru wajen sauya alƙiblar jam'iyyar, inda ya magance wasu manyan matsaloli da suka addabe ta, ciki har da zarge-zargen wariyar addini, tare da dawo da martaba a fannoni kamar tsaro da tattalin arziki.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu jam'iyyarsa tana tambayar ko shi ne mafi dacewa da zai jagorance ta zuwa babban zaɓe mai zuwa
Starmer ya kuma ce zai ci gaba da riƙe mukamin firaminista na ɗan lokaci har sai an zaɓi sabon shugaban jam'iyyar kafin dawowar majalisar dokoki daga hutun bazara.
Ya kuma yi alƙawarin tabbatar da miƙa mulki cikin natsuwa, tare da bayar da cikakken goyon baya ga wanda zai gaje shi, yayin da ya gode wa abokan aikinsa da ma'aikatan gwamnati kan gudunmawar da suka ba shi a lokacin da ya ke kan karagar mulki.
An zaɓi Sir Keir a matsayin shugaban jam'iyyar Labour a watan Afrilun 2020 kuma ya zama Firaminista a ranar 5 ga Yuli 2024 bayan nasarar da jam'iyyarsa ta yi a babban zaɓen ƙasa da aka gudanar.
Wannan mataki da ya ɗauka na sauka daga mulki na nufin nan ba da jimawa ba Birtaniya za ta samu Firaminista na bakwai tun daga shekara ta 2016.

Asalin hoton, Getty Images
Sir Keir ya samu rakiyar matarsa Victoria yayin da ya fito daga gidan gwamnati na Downing Street don gabatar da jawabin murabus ɗinsa.
A gaban magoya bayansa da abokan aikinsa da ma'aikatansa na gidan gwamnati Sir Keir, ya yi magana kan abin da zai mai da hankali a nan gaba.
Ya ce: "Lokacin da na bar aiki mafi girma a ƙasa, zan koma yin wani aiki mai matuƙar muhimmanci, wanda shi ne kasancewa miji na gari ga matata Vic, wadda ta kasance Babbar mai mara mun baya a koda yaushe inda ta ke tare da ni a cikin lokatan jin daɗi da kuma rashin daɗi; da kuma kasancewa mahaifi ga ƴaƴana, waɗanda su ne babban abin alfahari a gare ni."
Rashin nasarar jam'iyyar Labour
Matsin lamba daga cikin jam'iyyar Labour ya sa Sir Keir na fitar da jadawalin tafiyarsa bayan nasarar da Andy Burnham ya samu a zaɓen cike gurbi na Makerfield a makon jiya.
Mutane da dama suna kallon Burnham, tsohon magajin garin Manchester, a matsayin wanda yake kan gaba cikin wadanda ake ganin za su iya maye gurbin Sir Keir bayan da ya tabbatar da komawar sa majalisa da gagarumin nasara kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar Reform UK.
A ranar Litinin ɗin nan aka rantsa da Burnham Westminster a matsayin ɗan majalisa.
Tsohon Sakataren Lafiya Wes Streeting shi ma a baya ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar ta shugabancin Labour.
Rashin gamsuwa da shugabancin Sir Keir ya samo asali ne tun gabanin rashin nasarar da jam'iyyar ta yi a zabe a Ingila, Wales da Scotland a watan Mayu.
An yi nuni da matakin da ya ɗauka na sauya alƙibla kan wasu manyan manufofi guda uku a cikin wata guda bayan matsin lamba daga cikin jam'iyyarsa.
Naɗin Mandelson jakada a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Shawarar da Sir Keir ya yanke na naɗa Lord Mandelson a matsayin jakadan Birtaniya a Amurka ya kuma haifar da tambayoyi kan yadda fadar gwamnati ta Downing street ke tsara manufofi da kuma ɗaukar matsaya kan al'amura masu sarƙakiya.
An kori Lord Mandelson ne bayan wani sabbin bayanai sun fito fili game da zurfin dangantakarsa da marigayi Jeffrey Epstein da aka samu da laifin cin zarafin mata ta hanyar jima'i.
Matsalolin tattalin arziƙi a Birtaniya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugabar jam'iyyar Conservative Kemi Badenoch ta bayyana Sir Keir a matsayin "mummunan firaminista" tare da sukar manufofinsa, ciki har da ƙaruwar gudummawar inshorar ƙasa da masu ɗaukar ma'aikata ke bayarwa da kuma "yin watsi da sake fasalin shirin tabbatar da walwalar al'umma ".
Ta rubuta shafinta na X cewa: "Amma ba Starmer ne kaɗai matsala ba''.
''Yan majalisar na Labour suna son ƙarin haraji ne kawai kamar yadda sakataren kula da walwalar al'umma ya nuna. Wannan matsaya ce ta jam'iyyar Labour, ba ta da nasaba da ko wane ne ke jagorantar jam'iyyar."
Jagoran jam'iyyar Reform UK, Nigel Farage, ya buƙaci a gudanar da babban zaɓe, yana mai cewa: "Jam'iyyar Labour za ta sha mamaki idan har ta na tunanin za ta iya ƙara lanƙaya mana wani ƙwararren ɗan siyasa a Downing Street."
Shugaban jam'iyyar Green Party Zack Polanski ya ce ƙasar "tana buƙatar wani kwakkwaran sauyi na alƙibla", inda ya ƙara da cewa Sir Keir "ya rasa goyon bayan ƙasar saboda gazawarsa wajen ƙalubalantar yadda al'amura ke gudana a fagen mulkin ƙasar ".
Taɓarɓarewar alaƙa da Trump

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Sir Keir ya naɗa Lord Mandelson a matsayin jakada shi ne fatan cewa zai ƙarfafa dangantaka da Shugaban Amurka Donald Trump.
Duk da farkon kyakkyawar mu'amala tsakanin shugabannin Amurka da Birtaniya, dangantakar "ta musamman" tsakanin ƙasashen nan ta fara tangal-tangal bayan da Sir Keir ya ƙi shiga cikin yaƙin da ake yi da Iran a farko.
Daga baya firaministan ya sauya matsayinsa, inda ya bai wa sojojin Amurka damar amfani da sansanonin Birtaniya don ƙaddamar da hare-haren da ya kira na "kariya" kan wuraren makamai masu linzami na Iran.
Sai dai wannan matakin na tsaka-tsaki bai gamsar da Trump ba, wanda ya ci gaba da yin kalamai masu zafi kan Sir Keir, kuma hakan ya ɓata ran ƴan ga-ni-kashe-nin magoya bayan jam'iyyar Labour, waɗanda suka yi watsi da duk wasu hanyoyin shiga cikin rikicin.
Ga wasu masu sukar firaministan, wannan sassaucin ra'ayi alama ce ta jagorancinsa: jinkirin cimma matsaya da zai bata wa ɓangarorin biyu rai.
Hakika, shugaban Amurka ya nuna kamar ya riga ya hango murabus ɗin Sir Keir.
A wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta a ranar Lahadi, Trump ya ce Sir Keir "zai yi murabus daga kujerar firaminista", yana zargin sa da "gazawa mai tsanani" a bangaren shige da fice da kuma manufofin makamashi.
"Na yi masa fatan alheri!" in ji Trump.










