Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda sabon rikici ya kunno kai a NDC a yankin arewa maso gabashin Najeriya
Wani sabon rikici ya fara kunno kai a jam'iyyar NDC a yankin arewa maso gabashin Najeriya, bayan da ƴan takarar gwamna shida na jam'iyyar suka ƙi amincewa da naɗin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, a matsayin jagoran jam'iyyar a yankin.
Rahotanni sun ce tuni 'yan takarar suka miƙa koke ga hedikwatar jam'iyyar don ɗaukar mataki.
Wannan rikici na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan komawar tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal zuwa jam'iyyar NDC, inda aka naɗa shi jagoran jam'iyyar kuma wanda zai lura da harkokin yakin neman zabe a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Ƴan takarar na gwamna a jam'iyyar da suka fito daga jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe, da Taraba da kuma Yobe, sun yi fatali da matakin, inda suka ce ba a tuntube su ba, kafin a naɗa shi.
Me ya faru?
Honorabul Yohanna Mathias, kakakin jam'iyyar NDC jihar Adamawa, ya shaida wa BBC cewa, ƴan takarar jam'iyyar ta NDC da suka fito daga yankin arewa maso gabas da arewa ta tsakiyar Najeriya, sun yi wani taro inda suka bayyana rashin jin daɗinsu akan naɗin da aka yi wa Injiniya Babachir Lawal.
"...Tun da farko uwar jam'iyya bata tuntuɓe su ba akan wannan naɗi, sannan ba a dubi abin da ya cancanta ba aka yi wannan naɗin," in ji shi.
A don haka ne ƴan dukkan takarar suka ce ba su amince da naɗin ba kasancewar su ne za su tsaya takarar gwamna a wannan yanki.
Sun kuma ce ya kamata kowanne naɗi da za a yi a duba yadda yanayin tafiyar mutum ta ke a siyasance.
"...Ba wanda bai san irin dambawar da Babachir ya yi ba da ƴan siyasa da dama a jihohin wannan yankin, don haka suke tsoro, saboda sun fi so su samu wanda hankalinsu zai kwanta ya kuma riƙe su a matsayin uba, amma suna ganin tafiyar Babachir a cewarsu, sam ba zai nuna musu adalci ba." In ji Mathias.
Martanin Babachir Lawal
Honorabul Yohanna Mathias, ya ce, "Tarihi kuma ya nuna cewa babu inda Babachir ya shiga ba a yi kuka da shi ba, don haka su abin da 'yan takarar gwamna na jam'iyyar NDC a yankin arewa maso gabashin Najeriya ke so shi ne a zauna a fahimci juna domin ba bu wanda ba ya son karuwa a jam'iyyarsa."
Sai dai a martanin da Babachir ɗin ya mayar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya zargi wasu daga cikin ƴan takarar gwamnan jam'iyyar NDC da ƙoƙarin kawo cikas ga takarar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a zaɓen 2027.
Ya ce, waɗannan bayanan dai tamkar wani martani ne kan ƙin amincewa da shigarsa jam'iyyar da kuma naɗa shi jagoran NDC a Arewa maso Gabas.
Ya ƙara da cewa shugabancin jam'iyyar na ƙasa ne ya naɗa shi, kuma ya amince da matsayin ne saboda girmama wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar NDC.
Yaushe Babachir ya shiga jam'iyyar NDC
Babachir Lawal, ya ya shiga jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a ranar Talata, 22 ga watan Satumba, 2026.
Ya sanar da wannan sauyin sheka ne a birnin Abuja, watanni uku bayan ya fice daga jam'iyyar ADC sakamakon taƙaddama kan zaɓukan fidda gwani da kuma rashin tsarin dimokuraɗiyya na gaskiya a cikinta.
Babachir ya yi zargin cewa kurakurai sun ɓata zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar kuma an jirkita sakamakon zaɓen don ya fifita ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC Atiku Abubakar da mutanen da suke goyon bayansa.
Babachir Lawal ya bayyana cewa kishin ƙasa da kuma fatan ganin an ceto Najeriya daga matsalolin tsaro, yunwa, da fatara ne suka sa shi shiga NDC.
Ya ƙara da cewa jam'iyyar ita ce ke wakiltar ingantacciyar makomar ƙasar, saboda haka kowane ɗan ƙasa na gari da ke son ci gaba ya kamata ya marawa wannan tafiya baya domin samar da canji a zaɓen shekarar 2027.
Babban dalilin da ya ƙara kai shi zuwa jam'iyyar ta NDC in ji shi, shi ne domin ya ba da cikakken goyon baya ga haɗakar takarar shugabancin ƙasa ta Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
A cewarsa, haɗakar waɗannan manyan jiga-jigan siyasa biyu a ƙarƙashin inuwar NDC ita ce mafita mafi dacewa da za ta iya ƙalubalantar jam'iyyar APC mai mulki da kuma samar da adalci ga 'yan Najeriya.
Wane ne Babachir Lawal?
Babachir David Lawal shahararren ɗan siyasar Najeriya ne kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) a lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari. An haife shi ne a ƙauyen Kwambla da ke ƙaramar hukumar Hong a jihar Adamawa.
Marigayi tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya a watan Agustan 2015.
Sai dai, a watan Oktoban 2017, Shugaba Buhari ya kore shi daga kan wannan muƙami biyo bayan zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗen tallafin da aka ware wa 'yan gudun hijira na rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas. An maye gurbinsa da Boss Mustapha.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Sai dai kuma, bayan kwashe shekaru ana shari'a, a watan Nuwamba na shekarar 2022, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta wanke Babachir Lawal da wasu mutum biyar daga dukkan zarge-zargen almundahanar kuɗi naira miliyan 544.
Ya fice daga jam'iyyar APC saboda saɓani kan takarar musulmi da musulmi ta jam'iyyar ta yi a zaɓen 2023.