Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Munanan haɗurra 6 da suka kashe mutane a wurin haƙar ma'adanai a Najeriya
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Haƙar ma'adinai na daga cikin ayyukan da suka jawo asarar rayukan mutane a Najeriya, musamman a wuraren da ake gudanar da aikin ba tare da ingantattun matakan kariya ba.
A wasu wuraren, masu haƙar ma'adinan na fuskantar barazanar zaizayar ƙasa da ruftawar ramuka da su a ciki, lamarin da kan jefa rayukan ma'aikata cikin haɗari.
An sha samun rahotannin mutuwar masu haƙar ma'adinai a sassan Najeriya, ko suna aikin bisa ƙa'ida ko kuma ba bisa ƙa'ida ba. Lamarin ya fi faruwa a wasu jihohin arewacin ƙasar da ake haƙar zinare.
Sai dai ba kasafai ake samun cikakkun bayanai kan irin waɗannan haɗurra ko adadin mutanen da suka mutu a cikinsu ba.
Wani bincike da kamfanin Beacon Security and Innovations Limited, mai nazarin harkokin tsaro a Najeriya da sauran sassan Afirka, ya gudanar ya yi nazari kan haɗurran da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a wuraren haƙar ma'adinai tsakanin shekarar 2021 da 2026.
Ga wasu daga cikin manyan haɗurran da aka samu a wannan lokaci.
Yaɗuwar sinadaran guba (Zamfara) - 2021-2026
Rahoton Beacon ya bayyana cewa ana ci gaba da samun mutuwar mutane da kuma illolin gubar dalma a wasu al'ummomin yankunan da ake haƙar zinare a Zamfara, sakamakon sarrafa ma'adinai ta hanyoyin da ba su da aminci da kuma rashin tsaftace wuraren da suka gurɓata.
A shekarar 2021, ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta duba yara 8,480 'yan ƙasa da shekara biyar a jihar Zamfara, inda sama da kashi 80 suke buƙatar kulawa ta musamman. Yara 3,549 daga cikinsu sun samu maganin cire gubar daga jini.
Sai dai a ƙarshen shekarar 2021, MSF ta miƙa ragowar shirinta na yaƙi da gubar dalma a Zamfara, bayan an tsaftace ƙauyukan da abin ya shafa tare da samun raguwar gubar da ke cikin jinin mutane sosai.
Duk da haka, rahoton Beacon ya ce ana ci gaba da samun illolin gubar dalma, musamman ga yara 'yan ƙasa da shekara biyar, a wasu wuraren haƙar zinare tun daga 2021 har zuwan.
Mutuwar masu haƙar ma'adanai 25 a Kogi - 2021
A watan Oktoban 2021, mutane 25 da ke haƙar ma'adinai sun mutu bayan wani rami ya rufta a yankin Bilalikoto da ke ƙaramar hukumar Ankpa a jihar Kogi.
Rahoton Beacon ya ce wannan haɗari ya nuna irin barazanar da masu haƙar ma'adinai ke fuskanta, musamman a wuraren da ake gudanar da aikin ba tare da gina ingantattun matakan da za su hana ramuka rushewa ba.
Mutuwar mutum 22 a Adamawa - 2024
A ranar 7 ga Nuwamban 2024, aƙalla masu haƙar ma'adinai 22 suka mutu bayan wani ramin haƙar zinare ya rufta a wani yanki da ke tsakanin ƙaramar hukumar Gashaka ta jihar Taraba da Toungo ta jihar Adamawa.
Rahoton Beacon Security ya ce wannan haɗari ya sake nuna irin barazanar da masu haƙar zinare ke fuskanta, musamman a wuraren da ake gudanar da aikin ba bisa ƙa'ida ba, ba tare da ingantattun matakan tsaro da za su hana ramuka rushewa ba.
Guba ta kashe mutum 37 a Filato
A tsakanin 18 zuwa 19 ga Fabrairun 2026, aƙalla masu haƙar ma'adinai 37 ne aka ruwaito sun mutu, a wurin haƙar ma'adinai da ke Kampani Zurak, ƙaramar hukumar Wase ta jihar Filato.
An kuma samu rahoton cewa wasu da dama an garzaya da su asibiti bayan wani bayan shaƙar iskar guda a wurin.
Rahoton Beacon Security ya ce ana zargin mutanen sun mutu ne sakamakon shakar iska mai guba., inda ta ce hakan ya nuna haɗarin da ke tattare da aikin haƙar ma'adinai a wuraren da ba su da ingantattun matakan tsaro da iska mai kyau.
Rushewar wurin haƙar ma'adinai ya kashe mutane 20 a Kogi - 2026
A ranar 14 ga Yulin 2026, mutane 20 da ke aikin haƙar ma'adinai sun mutu bayan wani wuri da ake haƙar ma'adinai ya rufta a Alufele, gundumar Enjema da ke ƙaramar hukumar Ankpa ta jihar Kogi.
Rahoton Beacon Security ya ce rushewar ta faru ne yayin da ake gudanar da aikin haƙar ma'adinai.
Mutuwar masu haƙar ma'adinai 37 a hannun NSCDC
A ranar 17 ga Satumban 2026, mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma'adinai ne suka mutu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) yayin da suke tsare a Minna, jihar Neja.
An kama mutanen ne a wani samame da jami'an NSCDC suka kai kan masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba. Wasu daga cikin wadanda suka tsira sun shaida wa BBC cewa sun sha wahala mai tsanani a wani ƙaramin ɗaki inda har suka riƙa shan fitsarinsu da zufarsu domin su rayu.
Rahoton Beacon Security ya ce mutuwar mutanen a hannun hukumar ta haifar da ɓacin rai a tsakanin jama'a tare da zanga-zanga.
Abin da rahoton ya ce a taƙaice
Rahoton ya ce kusan kashi 70 cikin 100 na ayyukan haƙar ma'adinai a ƙasar ana gudanar da su ne ta hanyar da ba ta dace ba. Duk da tarin ma'adinan da Najeriya ke da su, gudummawar da ɓangaren ke bayarwa ga tattalin arzikin ƙasar bai wuce kashi ɗaya zuwa biyu.
Rahoton ya nuna cewa haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba na taimakawa wajen ƙara ta'azzara rashin tsaro, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Ya ce ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na karɓar kuɗi daga masu haƙar ma'adinai, karɓe ma'adinai ko kuma zinare domin samun kuɗin sayen makamai.
Rahoton ya kuma yi ƙiyasin cewa ana asarar kusan dala biliyan tara a duk shekara ta hanyar haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da safarar ma'adinan.
Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa rashin bin ƙa'idojin muhalli da tsaro a wuraren haƙar ma'adinai na haddasa mutuwar mutane da gurbata muhalli.
Ya kawo misalin gubar dalma a Zamfara, wadda ta yi sanadin mutuwar ɗaruruwan yara tare da jikkata wasu da dama, da kuma rugujewar ramukan haƙar ma'adinai a jihohin Zamfara, Filato, Kogi, Taraba da Sakkwato.
Ana kuma amfani da yara wajen haƙar zinare da lithium, yayin da wasu sinadarai masu guba ke gurɓata ƙasa da ruwa. Rahoton ya ce rashin kula da lafiyar ma'aikata da muhalli ya sa haƙar ma'adinai ke zama barazana ga rayuwar al'umma.