Najeriya ta mayar wa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo Gwaggon Birinta
Najeriya ta mayar wa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo wani ƙaramin gwaggwan biri da aka ceto, a wani mataki da Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce shi ne karon farko da ta kammala cikakken aikin ƙasa da ƙasa na yaƙi da safarar namun daji.
Jami’an Kwastam sun ceto dabbar mai suna Bili, daga hannun wata ƙungiyar masu safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba a watan Agustan 2023.
Daga nan ne aka kai ta Gidauniyar Pandrillus da ke Calabar, inda aka ba ta kulawa da jinya ta musamman. An kuma yi mata gwajin ƙwayoyin halitta domin tabbatar da cewa asalinta daga Jamhuriyar Kongo yake.
Mai magana da yawun Hukumar Kwastam ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa tafiyar Bili ta komawa gida ta fara ne ta mota daga Calabar zuwa Legas, kafin daga nan a ɗauke ta da jirgin sama zuwa Pointe-Noire.
Wata mai kula da gwaggwan birin da kuma likitan dabbobi sun raka ta zuwa gandun namun daji na Tchimpounga, inda za ta ci gaba da samun kulawa. Gandun na daga cikin manyan cibiyoyin kula da namun daji da aka ceto a Afirka.
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce an gudanar da aikin mayar da dabbar ne tare da haɗin gwiwar hukumomi da ƙungiyoyin kare muhalli, ciki har da hukumar da ke kula da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa kan safarar dabbobi da tsirran da ke fuskantar barazanar bacewa, da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya.
Hukumar ta ce aikin ya yi daidai da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa da ke samar da kariya mafi girma ga birrai da sauran nau’o’in namun daji da ke cikin barazanar bacewa.
Lamarin na cikin abubuwan da ke ƙara nuna yadda safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba ke ƙetare iyakokin ƙasashe. Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce masu safarar namun daji kan ratsa da dabbobin ta ƙasashe daban-daban, inda suke amfani da wasu ƙasashe a matsayin wuraren wucewa kafin daga bisani su kai dabbobin wuraren da za a sayar da su.
A shekarun baya-bayan nan, Najeriya ta zama muhimmiyar hanyar wucewar safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba a Afirka. Masu safarar dabbobi na amfani da ƙasar wajen safarar pangolin, hauren giwa da kuma birrai masu rai, kafin daga bisani a kai su wasu ƙasashe.
Kwastam ta ce tsakanin watan Janairu da Satumban 2026, ayyukan da ta gudanar na yaƙi da safarar namun daji sun kai ga cafke kayayyaki da dabbobi har sau 22. A yayin ayyukan, an ceto dabbobi masu rai 699 tare da kama mutane 11.
Kayayyakin da aka cafke sun haɗa da kilogram 220 na ƙwarangwal ɗin pangolin, hauren giwa guda 48 da kuma sama da kilogram 219 na hauren giwar da aka sarrafa.
Masu rajin kare muhalli sun ce mayar da dabbobin da aka ceto zuwa ƙasashensu na taimaka musu wajen samun kulawar da ta dace, tare da aika saƙo ga masu safarar namun daji cewa ketare iyakar ƙasa ba yana nufin za su tsira daga hukuma ba.