Yadda aka yi wa wata mawaƙiya bulala 74 saboda ƙin sanya hijabi a Iran.

Mawaƙiyar Iran, Parastoo Ahmadi, yayin wani wasa da ta gabatar, wanda aka nuna kai taye a shafinta na YouTube a watan Disamban 2024.
Bayanan hoto, Mawaƙiyar Iran, Parastoo Ahmadi, yayin wani wasa da ta gabatar, wanda aka nuna kai taye a shafinta na YouTube a watan Disamban 2024.
    • Marubuci, David Gritten
    • Marubuci, Ghoncheh Habibiazad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

An yi wa wata fitacciyar mawaƙiya da mutum huɗu daga tawagarta bulala a Iran saboda wani wasa da suka gabatar ba tare da ta sanya hijabi ba, in ji lauyoyinsu.

Lauyoyin nasu sun shaida wa BBC cewa an yi wa Parastoo Ahmadi, da mawaƙa uku da wani furodusa bulala 74 kowannensu a birnin Qom.

Ahmadi mai shekara 29 ta fito sanye da riga marar hannu a wani wasa da aka watsa kai tsaye ta intanet a watan Disamban 2024. Dokokin Iran sun haramta wa mata yin wasa a bainar jama'a tare da wajabta musu sanya hijabi.

A watan Yunin da ya gabata, wata kotu a Qom ta same ta da wasu mutum takwas da laifin "saɓa tarbiyyar jama'a" ta hanyar wallafa "abubuwan da ba su dace ba kuma na rashin ɗa'a", zargin da suka musanta.

Baya ga hukuncin bulala 74 da aka yi musu, an kuma hana su gudanar da ayyukan sauti da bidiyo tare da hana su fita ƙasar na tsawon shekara biyu.

Lauyoyinsu sun ce a ƙarshen watan Satumba, wata kotun ɗaukaka ƙara a Qom ta yi watsi da ƙarar da waɗanda aka hukunta suka shigar, tare da tabbatar da hukuncin da aka yanke musu.

Hukuncin ya jawo suka daga wasu masu rajin kare haƙƙin bil'adama a Iran, waɗanda suka ce hukuncin bulala azabtarwa ce mai tsauri da wulaƙanci, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da ke haramta azabtarwa.

A ranar Litinin, ɗaya daga cikin lauyoyin waɗanda aka hukunta ya shaida wa BBC cewa an yi wa Ahmadi da wasu maza huɗu da ake tuhuma tare da ita bulala a reshe na uku na ofishin aiwatar da hukuncin laifuffuka da ke birnin Qom.

Ya ce: "Mun yi duk mai yiwuwa domin a soke hukuncin, ko a rage shi, ko a dakatar da aiwatar da shi, amma hakan bai yiwu ba."

Ya ƙara da cewa: "Ni da sauran lauyoyi mun kuma yi ƙoƙarin neman a ɗage aiwatar da hukuncin, amma jami'an da ke da alhakin aiwatar da hukuncin sun nace sai an zartar da shi nan take."

Jaridar Etemad mai goyon bayan sauye-sauye ta ambato wani lauya mai kare waɗanda aka hukunta, Mostafa Nili, yana cewa mazan huɗun da aka yi wa bulala tare da Ahmadi su ne Soheil Faghih-Nasiri da Amin Taheri da Amirali Pirnia da kuma Mohsen Lashkari.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bahar Ghandehari ta Cibiyar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Iran (CHRI) mai hedikwata a Amurka ta ce yi wa Parastoo Ahmadi bulala saboda ta yi waƙa kuma ta sanya tufafin da ta zaɓa "babban take hakkin ɗan adam ne", kuma alama ce ta yadda hukumomin Iran ke ƙoƙarin taƙaita 'yancin mata da hukunta masu ƙalubalantar dokokinsu.

A ƙarƙashin dokokin Iran da suka samo asali daga fassarar shari'ar Musulunci da ƙasar ke bi, wajibi ne mata da 'yan mata da suka balaga su rufe gashinsu da hijabi tare da sanya tufafi masu yalwa.

A shekarar 2022, zanga-zanga ta ɓarke a faɗin Iran bayan rasuwar Mahsa Amini mai shekara 22 a hannun 'yan sandan kula da ɗa'a, bayan an kama ta kan zargin rashin sanya hijabi yadda ya kamata.

A lokacin zanga-zangar, mata da dama sun ƙona hijabansu ko suka riƙa ɗaga su sama a wani mataki na nuna adawa da dokar. Ɗaruruwan mutane sun mutu a matakin murƙushe zanga-zangar da jami'an tsaro suka aiwatar.

Tun daga lokacin, mata da 'yan mata da dama sun daina sanya hijabi a bainar jama'a, lamarin da hukumomi suka mayar da martani da kama mutane, bayar da gargaɗi da rufe wasu harkokin kasuwanci.

A watan Janairu, an kashe dubban mutane sannan an kama wasu dubban bayan da jami'an tsaro suka murƙushe wata zanga-zangar adawa da gwamnati da matsalar tattalin arziki ta haddasa.

Tun bayan fara rikicin Iran da Amurka da Isra'ila a ƙarshen watan Fabrairu, hukumomi sun ƙara ƙaimi wajen amfani da hukuncin kisa kan masu zanga-zanga.

Ƙungiyar Iran Human Rights wadda ke zaune a ƙasar Norway ta ce an kashe aƙalla mutum 39 da aka samu da laifi kan zanga-zangar Janairu, da kuma mutum biyu da aka samu da laifi kan tarzomar shekarar 2022. Haka kuma an kashe wasu mutum 16 da ake zargin suna da alaƙa da haramtattun ƙungiyoyin adawa, da wasu 17 da aka samu da laifin leƙen asiri ko haɗa baki da ƙasashen waje.

Haka kuma, a cewar ƙungiyar, wasu masu zanga-zanga 121, ciki har da mata shida da yara ƙanana biyar, na fuskantar barazanar aiwatar da hukuncin kisa.