Me ya sa kamfanin Nvidia ya kasa rabuwa da shugabansa Jensen Huang?

g
    • Marubuci, Faisal Islam
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Komawar Jensen Huang kan kujerar shugabancin kamfanin Nvidia ta zo da wasu abubuwa uku masu ban mamaki cikin 'yan kwanaki.

Sanarwar da kamfanin fasaha na Nvidia ya fitar lokaci guda kan komawar Huang bakin aiki ta taimaka wajen ƙara darajar hannayen jarin kamfanin a kasuwa da dala tiriliyan ɗaya. Haka kuma, kasuwannin hannayen jari na Asiya sun samu ƙaruwa duk da ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan komawarsa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince cewa saƙon da ya aika wa kwamitin gudanarwar kamfanin, mai taken "An soke korar aiki", ya sauya matakin da aka ɗauka.

Ana iya gane girman wannan sauyi daga sanarwar da kamfanin ya fitar makon da ya gabata, inda kwamitin gudanarwarsa ya bayyana cewa Huang ba zai koma bakin aikinsa ba.

Haka kuma, shugabannin rikon kwarya na kamfanin sun tattauna yiwuwar sauya dabarun gudanar da Nvidia da kuma barin salon tafiyar da kamfanin da aka saba da shi a zamanin Huang.

Sai dai yanzu duk waɗannan tsare-tsare sun zama tarihi.

Girman wannan sauyi ya zarce yadda aka yi a wasu lokutan da manyan shugabannin kamfanonin fasaha suka koma kan muƙamansu, kamar Sam Altman na OpenAI da kuma Steve Jobs na Apple.

Dalilin wannan sauyin mataki ya fito fili tun daga sanarwar farko. Gwamnatin Amurka ta ce komawar Huang kan muƙaminsa ba za ta haifar da wata barazana ga tsaron ƙasar ba.

Irin wannan tabbaci, ba zai samu ba sai daga Fadar White House.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sa'a guda bayan haka, Donald Trump ya bayyana cewa ya tattauna a sirrance da wasu mambobin hukumar gudanarwar kamfanin Nvidia.

Wannan ya tuna min da tattaunawar da na yi da Jensen Huang a watan Satumban da ya gabata, lokacin da ya fito fili ya goyi bayan bai wa China damar samun manyan fasahohin kwamfuta na Nvidia masu inganci.

Huang na cikin tsirarun mutanen duniya da za su iya cewa da gaske sun fahimci yadda shugabannin Amurka da China, Donald Trump da Xi Jinping, ke tunani.

Rahotannin da aka wallafa a Amurka sun nuna cewa an samu saɓani a cikin gwamnatin Trump tsakanin masu tsaurin ra'ayi kan China, waɗanda ke son ƙaƙaba mata takunkumi kan kayayyakin da take fitarwa, da kuma waɗanda ke goyon bayan matsayar Huang.

Sai dai ana ci gaba da gudanar da wani bincike mai zaman kansa kan ko Nvidia na bin ƙa'idojin da Amurka ta gindaya game da fitar da kayayyakinta zuwa ƙasashen waje.

Kwakwalwar kwamfuta na Nvidia na da matuƙar muhimmanci wajen ƙera na'urorin basirar AI mafi inganci a duniya. Tasirin da Huang ke da shi kan sayar da waɗannan kwakwalwar kwamfuta ya sa ya zama mutum mai tasiri fiye da shugabannin ƙasashe da dama.

Wannan ci gaba ba wai kawai yana da muhimmanci ga sauye-sauyen da ake samu a kasuwar hannayen jarin kamfanonin fasaha na Amurka ba, har ma da makomar tattalin arzikin duniya, siyasar Amurka da kuma hamayyar siyasa da tattalin arziki tsakanin Amurka da China.

Shakkun da ake nunawa kan Nvidia sun zo ne a daidai lokacin da fasahar basirar wucin gadi ke samun gagarumin ci gaba a duniya.

Kamfanin ya samu kuɗaɗen shiga sama da dala biliyan 400 a wannan shekarar, adadin da ya nuna gagarumin ƙaruwa idan aka kwatanta da ribar dala biliyan 27 da ya samu shekaru huɗu da suka gabata.

Gudummawar da Huang ya bayar wajen sauya Nvidia daga kamfanin da ya fi ƙwarewa wajen ƙera kwakwalwan kwamfuta na sarrafa hotuna zuwa ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke jagorantar juyin fasahar basirar wucin gadi ta fito fili.

A taƙaice dai, Huang mutum ne mai muhimmanci a kamfanin Nvidia har ta kai ga ba za a iya rabuwa da shi cikin sauƙi ba.