Abinci uku da ke ƙara ƙarfin ƙashi a jikin mutum

Awara
Bayanan hoto, Awara
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ƙarfin ƙashin jikin mutum na fara raguwa tun kafin lokacin da ake tsammani. Sai dai cin abincin da ke ɗauke da muhimman sinadarai na taimakawa wajen kiyaye lafiyar ƙashi da ƙarfafa shi.

Shan madara na taimakawa wajen samun ƙashi mai ƙarfi. Wannan na daga cikin shawarwarin lafiya na farko da ake bai wa mutane da dama tun suna ƙanana.

A lokacin ƙuruciya, ana ƙarfafa yara su riƙa shan madararsu, musamman a lokacin hutun makaranta, bisa bayanin cewa sinadarin calcium da ke cikinta zai taimaka wajen samar musu da ƙashi mai ƙarfi da lafiya.

Sai dai duk da cewa wannan shawara ta mayar da hankali kan sinadaran da ake samu daga madara tun ƙuruciya, ba a cika tattauna yadda raunin ƙashi ke zama ruwan dare yayin da mutane suka tsufa ba.

Akwai matakan da mutum zai iya ɗauka domin inganta lafiyar ƙashinsa, ko da kuwa shekarunsa nawa ne. Cin abinci mai ɗauke da sinadarai masu muhimmanci, tare da motsa jiki akai-akai, na taimakawa wajen samun ƙashi mai ƙarfi da lafiya.

Kuma ba wai shan madara kawai ake nufi da hakan ba.

Lafiyar ƙashin mutum tana da alaƙa da abubuwan da ya riƙa yi tun shekaru masu yawa kafin ƙashinsa ya fara nuna alamun rauni.

Irin ƙarfin ƙashin da mutum zai kasance da shi a lokacin tsufa ya danganta da tarin ƙashin da ya gina tun lokacin ƙuruciya. A waɗannan lokuta ne ƙashi ke ƙara ƙarfi da kauri, kafin ya kai matakin ƙarfinsa mafi girma a farkon shekarun balaga.

Wannan na daga cikin bayanan da Farfesa Kate Ward, ƙwararriya a lafiyar ƙashi da gaɓoɓin jiki a Jami'ar Southampton da ke Birtaniya, ta bayyana.

Abincin da ke taimaka wa wajen ƙarfafa ƙashi

Woman flexing her bones

Yayin da yawan ƙashin jikin mutum ke raguwa idan ya tsufa, akwai kuma kimanin mutane miliyan 500 a faɗin duniya da ke fama da cutar osteoporosis, wadda ke raunana ƙashi, ta sa ya yi siriri kuma ya zama mai saurin karyewa.

Julie Thompson daga ƙungiyar Royal Osteoporosis Society ta Birtaniya ta ce cututtukan osteopenia da osteoporosis kan kasance ba tare da alamun da za a iya ganewa ba, har sai mutum ya samu karayar ƙashi da ka iya sauya rayuwarsa.

Ta ce mata sun fi fuskantar haɗarin raguwar ƙarfin ƙashi yayin da suke tsufa, musamman a lokacin da suke daina al'ada. Haka kuma, cutar osteoporosis ta fi yawa a tsakanin mata. Sai dai maza ma na iya kamuwa da ita.

To, waɗanne irin abinci ne ya kamata mu riƙa ci domin ƙasusuwanmu su kasance da ƙarfi?

Madara

Madara

Sinadaran calcium, bitamin D da furotin na daga cikin muhimman abubuwan da ke taimakawa wajen lafiyar ƙashi. Haka kuma, sinadarai irin su bitamin K, magnesium, zinc da phosphorus na da muhimmanci wajen kiyaye lafiyar ƙashi da tsokokin jiki.

Abincin da ake samarwa daga madara na ɗauke da sinadarin calcium mai yawa. Misali, kofin madara mai mililita 200 na ɗauke da kusan miligram 260 na calcium.

Dangane da adadin calcium da ya kamata mutum ya riƙa samu a kullum, akwai ra'ayoyi mabambanta.

A Birtaniya, ana ba da shawarar manya su riƙa samun kusan miligram 700 na calcium a kowace rana.

Ga mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar osteoporosis, adadin da ake ba da shawarar shi ne miligram 1,000 a rana. Yayin da matan da suka daina al'ada ake ba da shawarar su riƙa samun miligram 1,200 a rana.

A Amurka kuwa, ana ba da shawarar manya su riƙa samun tsakanin miligram 1,000 zuwa 1,200 na calcium a kullum, gwargwadon shekarunsu da jinsinsu.

Abincin da aka sarrafa da waken soya

Farfesa Ward ta ce akwai nau'o'in abinci da ba na madara ba waɗanda za su iya taimakawa wajen samar wa jiki da sinadarin calcium.

Ɗaya daga cikinsu shi ne abincin da ake samarwa daga waken soya, kamar tofu da ƙwayoyin edamame. Giram 100 na tofu na ɗauke da miligram 200 na calcium.

Akwai kuma ƙarin shaidu da ke nuna cewa cin abincin da ake samarwa daga waken soya na iya rage haɗarin karayar ƙashi.

Waken soya na ɗauke da wani sinadarin halitta na tsirrai mai suna isoflavone, wanda yake kama da sinadarin oestrogen da ke jikin mutum.

Wasu bincike sun kuma gano cewa matan da suka daina al'ada waɗanda ke yawan amfani da sinadaran waken soya a matsayin ƙarin abinci (supplements), na da ƙashi mai ƙarfi da yawa.

Wani nau'in abincin da ake samarwa daga waken soya shi ne tempeh, wanda ake sarrafawa ta hanyar yayyanka da kuma barin waken ya yi ferment.

Wannan hanya na taimakawa wajen rage wasu sinadarai da ake kira antinutrients, waɗanda ka iya hana jiki shan wasu ma'adanai masu muhimmanci ga lafiyar ƙashi.

Saboda haka, jiki na iya samun damar shan sinadarin calcium daga tempeh cikin sauƙi.

Kifin gwangwani

Kifin gwangwani

Ƙaramin gwangwanin kifin sardine na iya samar wa mutum da kashi 30 cikin 100 na adadin sinadarin calcium da yake buƙata a rana. Gwangwanin sardine mai giram 60 na ɗauke da kusan miligram 240 na calcium.

Kifin da ake sayarwa a gwangwani ma na da yawan sinadarin calcium. Haka kuma, yana ɗauke da furotin mai muhimmanci wajen kiyaye lafiyar ƙashi, kare ƙarfin tsokokin jiki da kuma taimakawa wajen gyaran sassan jiki.

Haka kuma kifayen da ke ɗauke da kitse mai yawa na da wadataccen bitamin D, wanda ke taimakawa jiki wajen sarrafa sinadarin calcium da kuma shanye shi.

Rashin isasshen bitamin D a jiki na da alaƙa da gajiya, raguwar ƙarfin tsokoki da kuma ƙarin haɗarin faɗuwa.