Sanata Barau ya tara malamai 2,000 don yi wa Tinubu addu'a

Asalin hoton, Barau I Jibril/X
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin, ya nemi goyon bayan malaman addinin Musulunci daga ƙananan hukumomi 13 da ke yankin Sanatan Kano ta Arewa domin sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.
Sanata Barau ya yi wannan kira ne a ranar Litinin yayin wata ganawa da malaman addinin Musulunci sama da 2,000 a Kano.
Ya buƙace su da wayar da kan jama'a wajen mara wa Shugaba Tinubu da sauran 'yan takarar jam'iyyar APC baya, yana mai cewa shugaban ƙasar na da kyakkyawar manufa ga Jihar Kano da yankin Arewa maso Yamma da Arewa baki ɗaya da kuma Najeriya gaba ɗaya.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Isma'il Mudashir, ya fitar, Sanata Barau ya yaba da addu'o'i da shawarwari da kuma gudunmawar malaman wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano.
"Wannan taro ne na iyayenmu da shugabanninmu da malamai da limamanmu. Ku ne jagororinmu. Ina maraba da ku baki ɗaya tare da nuna godiyata bisa addu'o'i da goyon bayan da kuke ba mu''.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawar ya ce Kano ta daɗe tana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa, inda ya tuna da gudunmawar marigayi Malam Aminu Kano da sauran fitattun jagororin jihar.
Sanata Barau ya kuma tuna cewa bayan zaɓen shekarar 2023, shi ne mutum na farko daga Jihar Kano da ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.


