PSG za ta rike Barcola, Chukwueze na son ya ci gaba da taka leda a AC Milan.

Bradley Barcola

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bradley Barcola
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Paris Saint Germain ta yi kiyasin darajar dan wasan Faransa Bradley Barcola ta zarce fam miliyan 116 ,kuma ta tsaya kan matsayinta cewa dan wasan mai shekara 23 ba sai an sayar da shi ba, duk da bukatar daukarsa da Liverpool da Arsenal suka nuna. (Athletic), external

Yunkurin da Liverpool ke yi na neman dan wasa a gefen ya hada su da dan wasan kasar Belgium, Matias Fernandez Pardo mai shekaru 21, wanda ke taka leda a kungiyar Lille .(Express), external

Everton na da kwarin gwiwa za ta kulla yarjejeniya ta dindindin da dan wasan Chelsea, Tyrique George mai shekara 20 wanda suka karbe shi aro a kakar wasan da ta gabata.(Teamtalk), external

Chelsea na fatan karfafa bangaren masu kai mata hari ta hanyar daukar dan wasan Bournemouth, Eli Junior Kroupi. Dan wasan mai shekaru 20, wanda ke wakiltar Faransa a karkashin 'yan kasa da shekaru 21, ya yi kaka mai kyau, inda ya zura kwallaye 13 a gasar Premier League.(Caught Offside), external

Manchester City da Manchester United, da kuma Bayern Munich, sun bi sahun Arsenal wajen nuna sha'awa ga dan wasan Morocco, Ayyoub Bouaddi. Sai dai kungiyar Lille na neman akalla fam miliyan 70 kan matashin mai shekara 18, tare da shirin ci gaba da barinsa aro a kakar wasa mai zuwa.(Mail), external

Liverpool, da Arsenal, da Manchester United da Borussia Dortmund sun nuna sha'awa ga dan wasan Mainz Kaishu Sano mai shekaru 25, wanda ya zura wa Japan kwallo a wasan da suka sha kashi a hannun Brazil a zagayen 'yan 32 na gasar cin kofin duniya.(Bulinews, via Nikkan Sports), external

Tottenham ta cimma yarjejeniya kan sharuddan kashin kai da dan wasan Newcastle, Sandro Tonali mai shekara 26, kuma a shirye take ta biya kusan fam miliyan 100 domin siyan dan wasan na Italiya.(Teamtalk), external

Dan wasan AC Milan, Samuel Chukwueze, wanda ya shafe kakar wasan da ta gabata aro a Fulham, ya ki amincewa da komawa kungiyar Trabzonspor ta Turkiyya, yayin da dan wasan na Najeriya mai shekaru 27 ke son ci gaba da zama a Milan bayan Fulham ta zabi kada ta kulla yarjejeniya ta dindindin da shi.(Daily Post), external

Brentford na tattaunawa domin daukar dan wasan Ingila Callum Wilson, mai shekara 34, bayan kwantiraginsa da West Ham ya kare a karshen kakar wasan da ta gabata.(Athletic), external