Ko sakamakon zaɓen 2023 zai iya zama madubin na 2027?

Manyan ƴantakara
Bayanan hoto, Da alama yantakarar da suka fafata a 2023 za su sake karawa a 2027
    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Tun bayan da jam'iyyun siyasa a Najeriya suka kammala zaɓukar fitar da gwanayen da za su tsaya musu takara a zaɓukan 2027, wasu ƴanƙasar suka soma hasashen sakamakon zaɓen da ke tafe ta hanyar kwatanta shi da na 2023 da ya gabata.

Bisa ga bayanan zaɓukan fitar da gwanayen ƴantakarar da suka fatata a 2023 ne za su sake karawa a zaɓen na 2027.

Hakan ne ma ya sa wasu ƴanƙasar ke amfani da lissafin sakamakon 2023 domin hasashen sakamakon 2027.

To sai dai masana da masu sharhin siyasar ƙasar na cewa sakamakon 2023 ba zai zama madubin na 2027 ba.

A watan Janairun 2027 ne dai za a yi zaɓen shugaban ƙasa a Najeriyar, ƙasar da ta fi kowa yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Sakamakon zaɓen 2023

A zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata, wanda Shugaba Tinubi na APC ya yi nasara, manyan ƴantakara huɗu ne suka fafata, biyu daga kudu, biyu daga yankin arewacin ƙasar.

Shugaba Tinubu na APC, ya yi nasara a zaɓen da ƙuri'a miliyan 8,794,726, inda ya samu kashi 25 a jihohin ƙasar 29, wanda kundin tsarin mulkin ƙasar ya ce dole ne ɗan takara ya samu kashi 25 a aƙalla jihohin ƙasar 24, kafin ya samu nasara.

Kuma a lokacin jam'iyyarsa ta APC ce ke mulki a ƙasar, sannan tana da gwamnoni 21.

Sai Atiku Abubakar na PDP daga Arewa maso gabas da ya samu ƙuri'a miliyan 6,984,520 ya kuma samu kashi 25 na ƙuri'un jihohi 21.

A lokacin kuma PDP na da gwamnoni 13 a ƙasar.

Peter na LP daga Kudu maso gabashin ƙasar ne ya zo na uku da ƙuri'a miliyan 6,101,533, sannan ya samu kashi 25 na ƙuri'un jihohi 16, kuma a lokacin jam'iyyar LP ba ta da gwamna ko ɗaya a ƙasar.

Sai Egnr. Dr Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP daga arewa maso yammacin ƙasar da ya samu ƙuri'a miliyan 1,496,687.

Kuma jihar Kano, wadda ta fi kowa yawan al'umma a ƙasar - kawai ya iya lashewa.

Me ya sauya a yanzu?

ƴan siyasa

Asalin hoton, Gombe State Govt

Farfesa Abubakar Umar Kari malami a Jami'ar Abuja, mai sharhi kan al'amuran siyasar ƙasar ya ce abubuwa da dama sun sauya daga 2023 zuwa yanzu waɗanda kuma dole za su yi tasiri a zaɓen na 2027.

''Da farko dai ya kamata a fahimci cewa kowane zaɓe daban yake, kuma abubuwan da suke zama manuniya game da zaɓen daban suke, zai yi wahala a samu zaɓuka guda biyu a ce duka manuniyarsu iri ɗaya ne'', in ji shi

Ya ci gaba da cewa zaɓen 2027 zai sha bamban sosai da na 2023, lakari da wasu abubuwa kamar haka:

Tinubu na kan mulki

A zaɓen 2027 da za a gudanar Shugaban Tinubu na APC na cikin masu takara, kuma zai yi takarar ne yayin da yake kan mulki, saɓanin na 2023, wanda yake ba ya kan mulki, duk da cewa jam'iyyarsa ce ke kan mulki a lokacin.

Farfesa Kari ya ce '' A zaɓen 2023, wani shugaban ƙasa ne ya shirya zaɓen, wanda ba ya cikin ƴantakara, amma a 2027 ɗaya daga cikin ƴantakarar ne shugaban ƙasa, wanda ke neman wa'adin mulki na biyu''. in ji shi.

A lokuta da dama dai a siyasar Najeriya ba a fiye kayar da shugaban ƙasa mai ci ba, kodayake an taɓa yin hakan a 2015, lokacin da Buhari ya kayar da Jonathan duk da yana kan mulki.

Raunin adawa

Masanin siyasar ya ce a zaɓen 2023 an samu manyan jam'iyyu kamar uku da suka kusan yin kankankan a sakamakon.

''Idan ka dubi tazarar - da ke tsakanin Tinubu da ya lashe zaɓe da Atiku da Obi da suka zo na biyu da na uku - ba ta da yawa, kowa na da ƙarfi a lokacin, PDP na da gwamoni, LP na da ƙarfin magoya baya'', in ji shi.

Sai dai ya ce a yanzu kusan duka ƴan hamayyar sun sauya jam'iyyu, sun koma sabbi, kuma ba su da gwamna ko guda ɗaya, don haka akwai yiwuwar ƙarfinsu ya ragu.

''Atiku Abubakar ya koma ADC, Peter Obi da Kwankwaso na NDC, kuma duka jam'iyyun suna fama da rikicin shugabanci'', in ji shi.

Haɗewar Kwankwaso da Obi

Kwankwanso da Obi

Asalin hoton, Hon Saifullahi Hassan/Fb

A zaɓen 2023 manyan ƴantakara huɗu ne suka fafata, amma da alama a 2027 manyan ƴantakara uku ne za su kara.

Domin kuwa manyan ƴantaka biyu Peter Obi da Kwankwaso sun ƙulla ƙawancen siyasa kuma za su fito a ƙarƙashin jam'iyya ɗaya, a matsayin ɗantakar shugaban ƙasa da mataimaki.

Masu nazarin siyasa na ganin idan aka duba irin tasirin da suke da shi tsakanin mabiyansu a iya cewa haɗewar tasu za ta yi tasiri.

Raguwar tasirin Addini da ɓangaranci

Farfesa Kari ya ce a zaɓen 2023 addini da ɓangaranci sun taka muhimmiyar rawa takanin ƴantakara.

''A arewa an samu masu tallata batun ''Muslim-Muslim'' na ɗantakara da mataimaki musulmi da jam'iyyar APC ta yi, kuma hakan ya yi tasiri sosai musamman a arewacin ƙasar mai tarin ƙuri'u'', in ji masanin siyasar.

Haka ma Peter Obi ya samu goyon bayan Kiristocin ƙasar da dama, haka ma ƴan jihar Kano sun zaɓi Kwankwanso da suke ganin ɗan jiharsu ne.

Masanin siyasar ya ce bisa ga dukkan alamu a 2027 addini da ɓangaranci ba za su yi tasiri ba, saboda yanzu kowa ya dawo daga rakiyar hakan.

Raba garin wasu manyan ƴansiyasa

Farfesa Kari ya ce wani abu da zai sauya a 2027 shi ne tasirin raba gari da aka yi tsakanin wasu manyan jiga-jigan wasu jam'iyyun.

''Cikin wasu da suka kasance na gaba-gaban a tallata APC a 2023, yanzu sun raba gari har ma wasu sun sauya sheƙa, kodayake dai wasu dama sun koma jam'iyyarsa'', in ji shi.

Sauya shekar gwamnoni

Wani abu da ya saɓa wa 2023 shi ne yadda a yanzu jam'iyyar APC mai mulki ke da gwamnoni 30, cikin jihohin ƙasar 36.

Hakan ya faru ne sakamakon yadda wasu gamnonin suka yi ta tururuwar sauya sheƙa tsakanin 2024 zuwa 2025 da ma 2026.

Farfesa Kari ya ce la'akari da waɗannan abubuwa za a iya cewa sakamakon zaɓen 2023 ba zai taɓa zama madubin na 2027.

''Saboda ai abubuwan da suka yi tasiri a zaɓen da ya gabata, a yanzu ba za su yi tasiri ba'', a cewar malamin jami'ar.

''Ni ina ganin alƙaluman da aka samu a 2023 ba za su yi kusa ko kama da waɗanda za a samu a 2027 ba'', in ji shi.

Masanin siyasar ya ce ƴantakarar da aka tallata a 2023, sun nuna wa masu zaɓe kansu.

''Haka su ma masu zaɓen sun fahimci abubuwa da dama, kuma idanunsu sun buɗe sun ga komai'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Mene ne zai yi tasiri a zaɓen 2027?

Masanin siyasar ya ce babban abin da zai fi tasiri a zaɓen 2027 shi ne maganar sayen ƙuri'a.

''Kodayake a 2023 ma akwai wannan batu, amma bai yi tasiri sosai ba, amma a wannan zaɓen da ke tafe zai yi tasiri, domin tun daga zaɓen 2023, duk zaɓukan da suka biyo bayansu, an ga yadda ake amfani da kuɗi sosai wajen sayen ƙuri'a'', in ji Farfesa Kari.

Ya kuma ce sakar wa jam'iyyun hamayya mara na daga cikin abubuwan da za su yi tasiri a zaɓen.

''Idan ƴan hamayya suka samu damar shiga zaɓen, to nan ne za a yi gwagwagwar da za a iya gani, amma idan jam'iyyun hamayyar suka ci gaba da fuskantar matsalolin shari'a to tabbas tasirinsu zai ragu'', in ji si.

Ya kuma ƙara da cewa daga cikin abubuwan da za su yi tasiri a zaɓen na 2027 har da tattalin arziki da tsaro.