Ko sasanci tsakanin Iran da Amurka zai zama matsala ga ƙasashen yankin Gulf?

..

Asalin hoton, Eric Lee/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Ministocin harkokin wajen Qatar, Kuwait da Amurka, yayin wani taro a Manama - Yuni 25, 2026
    • Marubuci, Manal Khalil
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Rikicin soji ya ɗan lafa kuma an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran.

Har yanzu dai ana kan matakin farko ne a attaunawa tsakanin ɓangarorin biyu kuma ya yi wuri a ce za a tattauna sakamakonsu, amma tambayar da ke tafe a yau ita ce: Wane ne ya fi kowa asara a wannan yaƙin?

Akwai ra'ayi daban-daban na siyasa game da auna fa'ida da farashi. Ƙasashen Larabawa na yankin Tekun Fasha sun damu matuƙa cewa tattaunawar da Amurka za ta yi da Iran za ta kai ga ba wa Tehran "fabin da ya wuce kima" da kuma ƙarawa Iran ƙarfi a yankin.

Yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Tehran da Washington ba ta yi maganar sanya takunkumi kan shirin makamai masu linzami na Iran ba, lamarin da ka iya ƙara sanya damuwa a zukatan wasu ƙasashen yankin Gulf da waɗannan makamai masu linzami, za su iya kai wa gare su.

A lokacin yaƙin, gwamnatin Trump ta ce lalata ƙarfin makamai masu linzami na Iran na ɗaya daga cikin manyan manufofinta. Sai dai a ziyarar da ya kai birnin Paris na baya-bayan nan, Mista Trump ya gyara matsayinsa, yana mai cewa, "Idan har wasu ƙasashe na da makamai masu linzami, ba daidai ba ne a hana Iran mallakar wasu daga cikinsu.

Andreas Craig, mataimakin farfesa kan harkokin tsaro a kwalejin King's collage da ke Landan, ya yi imanin cewa shirin makamai masu linzami na Iran ya kasance babban ƙalubalen tsaro ga ƙasashen Larabawa na Tekun Fasha, amma shugabannin waɗannan ƙasashe sun san cewa neman wargaza shrirn makaman na Iran gaba ɗaya ba zai haifar da cimma wata yarjejeniya ba.

A wata hira da ya yi da sashen larabci na BBC, Mista Craig ya yi hasashen cewa, martanin da ƙasashen yankin Gulf za su mayar zai fi kasancewa a zahiri, kuma sun haɗa da ƙarfafa ababen more rayuwa, da faɗaɗa tsarin tsaron makamai masu linzami, da ƙera makamai masu linzami, da ƙarfafa matakan tsaron, da kuma ci gaba da tabbatar da aminci hanyoyin sadarwa da Tehran, don hana yin arangama kai tsaye.

..

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Yarjejeniyar Amurka da Iran ba ta haɗa da wani takunkumi kan makamai masu linzami na Iran ba, waɗanda ta harbawa wa wasu kasashen yankin Gulf.

Duk da irin luguden wutan da ƙasashen yankin Gulf suka sha da kuma yadda hakan ya fallasa irin raunin da ke tattare da sassan samar da ababen more rayuwarsu, Andreas Craig bai ɗauki waɗannan ƙasashe a matsayin waɗanda suka yi hasara a wannan yakin ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ta fuskar dabaru, da alama Isra'ila ce ta fi kowacce asara," in ji shi. "Ta kashe wani kaso na duk wani galihun da ta ke da shi ta fuskar siyasa, da diflomasiyya, da ƙarfin soja a wurin gwamnatin Amurka, tare da lalata matsayinta idon jama'ar yammacin duniya, tare da ƙara mata ƙaurin suna a matsayinta na ƙasa da ke tunzura Washington ta rura wutar tashin hankali a yankin a matsayin wani ɓangare na manufofinta na tsaro."

Akasin haka kuma, Mista Craig ya ƙara da cewa, ƙasashen yankin Gulf sun ƙara samun daidaito da ka'idojin manufar "America First", da suka haɗa da zuba jari a tattalin arzikin Amurka, rage tashe-tashen hankula, da samar da kwanciyar hankali a yankin. A ra'ayinsa, waɗannan ƙasashe suna taimakawa Amurka ta kowane fanni, tun daga tabbatar da tsaron makamashi zuwa shiga tsakani a rikicin yankin, kuma wannan wata babbar fa'ida ce a gare su.

A halin da ake ciki kuma, Hassan Manimaneh, wani mai bincike kuma malami a cibiyar Gabas ta Tsakiya da ke Washington, ya yi imanin cewa, ƙasashen yankin Gulf ne suka fi samun nasara a wannan halin da ake ciki; ba wai don sun cimma wasu manyan manufofi ba ne, sai za su ji jiki da an ci gaba da yaƙin.

Ya shaida wa sashen labrabci na BBC cewa ƙasashen yankin Gulf sun yi babban asara a lokacin yaƙin, amma da a ce ba a sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka da Iran ba, kuma ba a kawo ƙarshen yaƙin ba, da yankin ya fuskanci asarar da wataƙila ba zai iya farfadowa daga gare ta ba..

A cewar Mr. Manimaneh, batuwan da suka shafi makamai masu linzami da ƙungiyoyin da Iran ke marawa baya, da shirin nukiliya da mashigar ruwan Hormuz, su ne batutuwan da ƙasashen yankin tekun Fasha ke buƙatar mafita a kansu. Sai dai ya ce da an ci gaba da yaƙin, da waɗannan ƙasashen sun fuskanci barazana ga rayuwa da wanzuwarsu.

A cikin ƴan shekarun nan, ƙasashen yankin Gulf sun aiwatar da shirye-shirye masu yawa don bunƙasa tattalin arzikinsu da kuma saka hannun jari a fannoni kamar yawon shakatawa, da ayyuka, da kuma fasaha.

Shin ƙasashen Gulf sun biya farashin yaƙi ne, kuma dole ne su biya farashin zaman lafiya?

Yarjejeniyar Amurka da Iran ta kuma tanadi samar da wani asusu na dalar Amurka biliyan 300 domin sake gina tattalin arzikin Iran da bunƙasa tattalin arzikinta, asusun da ake sa ran ƙasashen yankin Gulf za su taka rawa wajen samar da ita.

A baya dai Iran ta buƙaci a biya ta diyya kan asarar da wasu ƙasashen yankin suka janyo mara ta hanyar sanya hannu ko kuma suka taimakawa wajen kai mata hari.

A nasu ɓangaren kuma, ƙasashe irinsu Qatar da UAE sun buƙaci Iran ta biya diyyar duk asarar da suka samu sakamakon hare-haren da ta kai musu. Wannan yanayin ya haifar da lamarin da zai kai ga ƙasashen Gulf daga ƙarshe su biya "kudin yaƙi da ma farashin zaman lafiya".

Hakan dai na faruwa ne duk da cewa ya zuwa yanzu ba a fitar da wata ƙididdiga ko alƙalumma da ke nuna irin ɓarnar da aka yi wa ƙasashen yankin Gulf.

..

Asalin hoton, Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Images

Bayanan hoto, Iran dai ta sha neman a biya ta diyya kan irin asarar da ta yi

Mashigar Hormuz: Abin da Iran ta dogara a kai

Daga cikin batutuwan da wasu ke fargabar za su iya ƙarfafa tasirin Tehran a yankin, mashigar Hormuz na da matsayi na musamman. Iran dai na amfani da hanyar ruwan ne a matsayin ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin da za ta iya amfani da su wajen samun galaba a tattaunawa, lamarin da ke damun ƙasashen yankin tekun Fasha, waɗanda yawan man fetur da iskar gas din da suke fitarwa ya dogara kan mashigar.

Saudi Arabiya na iya kewaye wani ɓangare na tasirin mashigar Hormuz ta hanyar amfani da bututun mai da kuma hanyoyin shiga Tekun Bahar Maliya. UAE kuma tana da wasu hanyoyin ta cikin Fujairah. Amma Qatar da Kuwait sun fi shiga tsaka mai wuya saboda ƙarancin hanyoyin fitar da kayayyaki.

..

Asalin hoton, Elke Scholiers/Getty Images

Bayanan hoto, Iran na ƙoƙarin sanya harajin wucewa ta mashigar Hormuz

Andreas Craig ya yi imanin cewa batun mashigar ruwan Hormuz za ta kasance mafi mahimmanci da sarƙaƙiya a duk wata yarjejeniya makamanciyar wannan.

Ya ce bai wa Iran damar taka rawa wajen kula da harkokin tsaro ko zirga-zirgar jiragen ruwa na iya zama haɗari, musamman idan ta zama hanyar da karɓar kudaden haraji da ba na hukuma ba ko kuma samun wani nau'in iko kan mashigar.

Sai dai ƙasashen yankin Gulf na buƙatar hanyar da za ta kasance a buɗe kuma amintaciya.

Don haka suna iya fitowa fili su yi adawa da duk wani yunƙurin da Iran za ta yi na karɓar kuɗin haraji, amma a aikace za su haƙura ta karɓi wasu ƴan kuɗaɗe da ba su wuce kima ba kuma waɗanda ba su keta doka ba, tare da tallafin ƙasa da ƙasa, da kuma yin ayyukan da suka haɗa da haƙo nakiyoyin da aka binne a cikin teku, da tabbatar da tsaro sufurin jiragen ruwa, ko kula da zirga-zirgar jiragen ruwa.

Ya ƙara da cewa: "Wannan halin da ake ciki ya nuna yadda ake tilastawa ƙasashen yankin Gulf su amince da yanayin ƙasa a yadda yake, ba yadda suke so ba."

Sai dai Hassan Manimaneh ya yi imanin cewa Iran ba ta mallaki mashigar Hormuz ita kaɗai ba, a'a tana da wani nau'i na ƙawance da Oman a wannan fannin, kuma a ƙarshe Muscat na taka muhimmiyar rawa. Ya jaddada muhimmancin haɗin kai a tsakanin ƙasashen yankin Gulf kan wannan batu.

..

Asalin hoton, Hamed Malekpour / AFP via Getty Images

Bayanan hoto, A yayin ziyarar da suka kai birnin Muscat, Shugaban Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqer Qalibaf da Ministan Harkokin Wajen ƙasar Abbas Araqchi sun jaddada ƙudirin Iran na tabbatar da zirga-zirga cikin aminci ta mashigar Hormuz.

Fahimtar da ke tsakanin Iran da Amurka, idan har ta ɗore, za ta iya ba da damar daidaita dangantakar da ke tsakanin Amurka da Iran. Wannan dai ya sanya ayar tambaya kan ko batun tsaro da ƙasashen yankin tekun Fasha ke da shi ba zai zama abin da ya fi jan hankali a Washington ba, da kuma ko waɗannan ƙasashe za su iya fatan samun makoma mai ƙyau bisa amincewar juna da kyakkyawar makwabtaka da Iran.

Hassan Manimaneh ya ce cimma irin wannan buri na buƙatar ƙoƙari, da daidaito dsa tsare-tsare, da kuma shiga tsakani. A ra'ayinsa, ƙasashen yankin Gulf suna da matakan tabbatar da iko da za su iya amfani da su, ta hanyar yin nuni ga hasarar da aka yi a baya-bayan nan, don samar da tsarin zamantakewar yankin wanda ya haɗa da Iran tare kuma da taƙaita ƙarfin ikonta.

Sai dai yana ganin cewa mataki na gaba ba lallai ba ne ya zama samar da irin wannan tsarin ba, kuma matakin farko ya kamata a yi la'akari da kafa tsarin tsaro na bai-ɗaya tsakanin ƙasashen yankin Gulf, da Turkiyya da Pakistan da kuma Masar.

Ya kuma ce Isra'ila za ta yi ƙoƙarin hana irin wannan shiri ya cimma ruwa. Bugu da ƙari, Amurka, wadda Mr. Menemen ya yi imanin ita ce babbar wadda ta yi asara a cikin waɗannan ci gaba, za ta yi ƙoƙarin hana kafa tsarin da Washington ba ta da bakin magana a cikinta.

Saɓanin haka, Craig ya ce ƙasashen yankin Gulf sun daɗe suna ganin cewa ba a magance muhimman batutuwan da suka shafi tsaro a Washington ba, amma hakan na iya ba da damar dawo da martabarsu a Amurka.

Ya yi imanin cewa, idan ƙasashen Saudiyya da Qatar, da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa suka daidaita ƙoƙarinsu, za su iya yin tasiri kan manufofin Amurka a Gabas ta tsakiya da Arewacin Afirka fiye da Isra'ila a nan gaba.

Craig ya ce waɗannan ƙasashe suna da sansanonin soji, da ɗimbin kadarori, da kayayyakin more rayuwa, da tasiri a kasuwannin makamashi, da hanyoyin diflomasiyya masu inganci; abin da suka rasa shi ne haɗin gwiwar gudanar da aiki.

Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudi Arabiya da Qatar da Kuwait, da Bahrain duk sun karbi baƙuncin sansanonin sojin Amurka, waɗanda ke zama babban ginshikin tsarin tsaron Amurka a yankin gabas ta tsakiya.