Yadda muka yi ƙoƙarin sasanta Iran da Amurka a gasar Kofin Duniya - Infantino

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Hukumar kwallon ƙafa ta Duniya Gianni Infantino ya musanta wasu manya-manyan ruɗani da aka samu lokacin wasan tare da yaba wa Iran kan halartar gasar duk da rikicin da ke tsakaninta da ɗaya daga cikin masu masaukin baƙi Amurka.
A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Istagram wanda Fifa ta ƙara turawa mutum miliyan takwas da ke binta - Infantino ya yi bayani ga wadanda suka laɓe suna ta rubutu a bayan fage suna sukar su, maimakon yin abin da ya kamata.
Infantino ya shawarci masu suka da su mayar da hankalinsu kan kwallon kafa su ji daɗin wasannin da ake yi ba su riƙa yaɗa jita-jita ba kan shugabancinsa da Fifa game da Gasar Kofin Duniya.
Ya ce gasar Kofin Duniya ta "nuna mutuntaka da matuƙar matsayi" yana cewa gasar 2026 "ta samar da tsaro da kwanciyar hankali, farin ciki da murna ga masu bibiyarta".
Ya ce Fifa "ta yi ƙoƙari ba dare ba rana ta haɗa kan ƙasashe biyu da ke yaƙi da juna", kuma Iran ta shiga ƙasar wasa " ba tare da wani rikici ba".
Bayanan sa sun ci karo da na kocin Iran Amir Ghalenoei, wanda ya ce "tawagarsa ce wadda ta fi shan wuya" a gasar Kofin Duniya.

Asalin hoton, Getty Images
An hana Iran biza a kan lokaci an kuma hana wasu jagororin da suke horar da tawagar biza baki ɗaya, wasu magoya bayan da suka sayi tikitinsu duka an ƙwace, kuma an tilsata wa Iran barin inda aka tanadar mata domin atisaye a Tucson a Arizona zuwa Tijuna da ke Mexico.
Daga baya kuma suka fuskanci tsaiko na hana tafiya tsakanin wurin atisayensu da kuma inda suke wasa.
Ba iya Iran ce ta fuskanci wannan matsalar ba, magoya bayan Haiti da na Senegal da na Ivory Coast su ma hana tafiye-tafiyen da gwamnatin Trump ta yi ya shafe su.
A gefe daya kuma alƙalin wasan Somaliya Omar Artan an hana shi bizar shiga Amurka - duk da cewa yana da fasfon diflomasiyya da bizar shiga Amurka falle guda - saboda ana zargin sa da alaƙa da wata ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya.
Infantino ya rubuta cewa "Kuna ta cewa an hana wasu mutane ƙalilan biza yayin da aka bai wa miliyoyi, daga sassa daban-daban na duniya. Saboda kwallon ƙafa na haɗa kan duniya, kuma mun ga hakan a aikace a wannan gasar."
Binciken da Fifa ke yi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bugu da ƙari, Fifa na bincike kan rikicin Argentina da aka samu wasu masu taimakawa kocinsu da hannu ciki, yayin wasansu na ƙarshe da Sifaniya.
Tana kuma bincike kan shahararren mai amfani da kafafen sada zumuntar nan ɗan Amurka Darren Jason Watkins Jr. da aka fi sani da IShowSpeed - yayin da aka kama magoya baya da yawa a wasanni daban-daban - ciki har da wasan kusa da na ƙarshe tsakanin Ingila da Argentina.
An shigo da jami'an kwastam da na masu kula da shigi da ficin filin wasa, wani abu da ya riƙa haifar da ruɗani.
Infantino ya kuma yi magana kan sukar da aka riƙa yi musu game da yadda alƙalan wasa suka yi busar gasar, musamman kan yadda aka samu tasirin siyasa da shugaba Amurka ya yi magana kan dan wasan gabanta Folarin Balogun da ya buga wasan matakin 'yan 16 - bayan an dakatar da shi wasa ɗaya.
A cikin jan kati 191 da aka bayar a gasar kofin duniya ɗaya ne kawai ya taɓa tsallake dakatarwa.
Uefa ta ce matakin "ya wuce na jan kati" inda ta bayyana shi a matsayin abin da ba a yi tsammani ba, da babu dalilin yinsa", a gefe daya kuma Hukumar Kwallon Kafa ta Norway za ta shigar da ƙara a hukumance kan karya dokar wasannin.
Bayan an kammala gasar da yamma Infantino ya yi taron manema labarai karon farko cikin shekaru uku - yayin da yake cewa masu suka su ci gaba da " shanawa da hutawa. Wataƙila idan aka sake haɗa wata gasar sai su haɗa su ci gaba da ƙorafi bayan nan zan haɗa na ba su amsa," in ji Infantino.











