Yadda Anthony Joshua ya doke Prenga a Saudiyya

Close-up view of a bare-chested Anthony Joshua celebrating with his mouth wide open, looking happy, after his win in Jeddah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Anthony Joshua ya yi nasara a karawa shida cikin bakwai da ya yi a baya-bayan nan
    • Marubuci, Charlotte Coates
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Dan damben Birtaniya kuma dan asalin Najeriya Anthony Joshua ya sake dabbaka sunansa a fagen damben duniya a karawar da ya yi a daren ranar Asabar mai cike da takaddama da kuma sosa zuciya.

Hakan na zuwa ne yayin da ake tunkarar wani mashahurin karon-batta da ake sa ran za a yi tsakanin Joshua da Tyson Fury nan gaba a wannan shekara.

Yanzu Joshua, mai shekara 36 ya kara wani kambi a cikin tarihinsa na damben boksin 30-4, sai dai ya kusa shan mamaki mafi girma a tarihin sana’ar tasa lokacin da abokin karawarsa Kristian Prenga dan kasar Albania ya kai shi kasa har sau biyu a zagaye na farko.

Sai dai Joshua ya dawo da karfinsa a zagaye na biyu, inda ya rika saukar wa Prenga munanan naushi naushi yana kai shi kasa, lamarin da ya ba shi nasara a karawar da aka yi a birnin Jiddah na kasar Saudiyya.

Sashen wasannin motsa jiki na BBC ya zabo muku wasu kayatattun hotunan damben da aka gwabza a a daren, wanda aka yi wata bakwai bayan hatsarin mota da Joshua ya yi a Najeriya, lamarin da ya kashe aminansa biyu da ke tare da shi.

Anthony Joshua walking to the ring

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Anthony Joshua ya shigo cikin dandali ne tare da wata tawagar mutane masu mara masa baya
A close-up view of Anthony Joshua's camouflage walk-on outfit, featuring the names Latz and Sina - representing the friends who died in a car crash in December - alongside names of boxing governing bodies

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A rigar da ya saka gabanin damben, Joshua ya karrama abokansa Sina Ghami da Latif 'Latz' Ayodele, wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin mota da suka yi tare da shi a watan Disamba
Anthony Joshua on the canvas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Joshua ya taba kasa sau biyu bayan Prenga ya masa wasu munanan naushi a minti 20 na farkon karawar
Anthony Joshua smiles when being given the referee's count for the second time in round one

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Joshua ya yi murmushi lokacin da alkalin wasa ya rika kirga masa lokaci bayan da aka kai shi kasa a karo na biyu
Anthony Joshua punching Kristian Prenga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayan dawowa da karfinsa, Joshua ya saukar wa Prenga wani mummunan naushi da hannun dama, lamarin da ya kai Prenga kasa shame-shame
Kristian Prenga is grounded, with his back against a rope and his head partway outside the boxing ring

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Prenga ya rika fafutikar yadda zai fito daga tsakanin zare da zare bayan ya zama mutum na 27 da Joshua ya doke ta hanyar yi musu dukan ‘in ka girma ka rama’
Anthony Joshua tells everyone to calm down after he knocks Kristian Prenga out in the second round

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Joshua ya ce wa ‘yan kallo ‘kada kowa ya tayar da hankalinsa’ bayan ya doke Prenga a zagaye na biyu
Oleksandr Usyk hugs Anthony Joshua after the fight

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Joshua da dan’uwan sana’arsa Oleksandr Usyk sun rungume juna bayan nasarar
Anthony Joshua with his hands raised

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Joshua ya daga hannuwansa sama yana amsa kirarin da ake masa da kuma sowar magoya baya a birnin Jiddah
Anthony Joshua looks up, with a boxing glove raised, after his victory

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Joshua ya kalli sama bayan kammala aiki