Me ƙoƙarin jihar Kano a jarrabawar NECO ke nufi?

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT
Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta kasance ta ɗaya a saman teburin jadawalin sakamakon jarrabawar Kammala Makarantar Sakandare ta Shekarar 2026 NECO, Inda jihar Legas da Oyo ke biye mata.
Wannan na zuwa ne bayan sakin sakamakon jarrabawar na 2026 da Hukumar da ke shiryata ta yi waddda ta ce an gudanar da ita a dukkan jihohi talatin da shida 36 na Tarayyar Najeriya da Babban Birnin Abuja, daga ranar Litinin 15 ga Yuni zuwa Alhamis 23 ga Yuli, 2026.
A shekarar 2025 Jihar Kanon ce ta kasance ta 29 cikin jadawalin Sakamakon NECO tsakanin jihohin ƙasar 36 har da Abuja babban birninta, Inda sakamakon jarrabawar ya bar baya da ƙura, inda Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya yi iƙirarin jihar ce ta ɗaya wajen samun sakamako mai kyau, sai dai bayan an saki teburin sakamakon a hukumance sai aka ga sabanin haka.
A yayin jawabinsa ga manema labarai shugaban hukumar NECO Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ya ce, "yawan ɗaliban da suka yi rajistar jarabawar ya kai 1,378,048, wanda ya ƙunshi maza 682,352 da mata 695,696. Wadanda suka zauna rubuta ta sun kai 1,371,992, wanda ya ƙunshi maza 678,903 da mata 693,089.
"Ya kuma ce an samu ƙarin mutanen da ke da buƙata ta musamman yayin rubuta jarrabawar waɗanda suka kai 1,334.
Kazalika yawan waɗanda aka samu da laifukan satar amsar jarrabarwar a 2026 ya kai 1,406, idan aka kwatanta da 3,878 a shekarar 2025, wanda ke nuna raguwar 64.74%.
Me hakan ke nufi?
Dr Aliyu Tilde mai sharhi kan harkokin ilimi a Najeriya, kuma tsohon kwmaishinan ilimi na jihar Bauchi ya ce "dole a yaba wa jihar Kano wadda a baya ƙoƙarinta ya gaza hakan".
"Duk da cewa jihar Kano tana cikin jihohin da suka fi samar da ɗaliban da suke zama rubuta jarrabawar, gaza samun nasarar ɗalibanta zai zame mata abun kunya, a don haka nasararta dole ta zama abar yabawa" in ji Dr Tilde.
A cewarsa Bahaushe na da Karin magana da ta yi daidai da irin wannan hali da yake cewa "yabon gwani ya zama dole".
"Babu mamaki dan Jihar Kano ta zama ta ɗaya a wannan jadawali, saboda tun a shekarun 1970 ta yi fice wajen samar da mutanen da suka yi fice a fannin ilimi, kuma suka halarci jami'o'i daban-daban na duniya.
"A kimiyyance za a ce Kano ba ta yi ƙoƙari ba, saboda idan ka kwatanta ta da jihar Kebbi da ta bayar da dalibai 3,000 da Kano da ta bayar da dalibai 74,000 babu shakka Kano za ta fi samun yawan waɗanda suka yi nasara, amma dole a yaba mata idan ta kai ga nasarar", inji Tilde.
Sai dai masanin ya ce za a kammala yabawa Kano ne kawai idan NECO ta fitar da cikakken jadawalin ƙoƙarin jihohin Najeriya a lokacin jarrabawar.
A bisa al'ada Hukumar Shirya Jarrabwar NECO tana fitar da irin wannan jadawalin ne ba da daɗewa ba bayan ta fitar da sakamakon daliban baki daya.
Taƙaddama kan sakamakon

Asalin hoton, NECO X
A 2025 sakamakon NECO da aka fitar ya matuƙar barin baya da ƙura saboda kuskure ko kuma bayanan da aka fitar ba bisa daidai ba.
An ta yaɗa cewa Kano ce ke kan gaba a samun sakamakon jarrabawar, wanda hakan ya sa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya yi iƙirarin jiharsa ce kan gaba.
Bayan fitar da sakamakon a hukumance sai aka ce ita ce ta 29 a cikin jerin jihohin 36 har da Abuja.
Wannan ya ɗiga ayar tambaya kan bayanan farkon da ake samu a lokutan fitar da sakamakon
Sai dai Dr Tilde ya ce ko da Kano ta fi yawan daliban da suka ci Jarrabawar a wajen kasaftawa ta fuskar kaso za ta iya komawa ba ta farko ba.
"Jihar da ɗalibanta suke dubu hudu, 4,000 sai dubu uku da 800 suka ci, ta fuskar kaso tana da kashi 95%, ita kuma Kano ta je da dalibai 74,000 dubu 60,000 suka ci kasonta zai zama 81%.
"To idan aka bi ta fuskar kaso za a ga Kano ba ta yi rawar gani amma wasu za sau iya shan kanta," in ji Tilde.
Ta ya za a magance faɗuwar NECO a arewacin Najeriya?
Daliban da suka ci kiredit biyar ko sama da haka, ba tare da cin darasin Turanci da Lissafi ba, sun kai 1,162,118, wanda ke wakiltar 84.70%, in ji Farfesa Wushishi.
Wannan batu ne da ko da yaushe yake jan hankalin masana fannin ilimi in ji Dr Tilde, inda ya ƙara da cewa lokaci ya yi da ya kamata mutanen arewa su fuskanci gaskiya.
"Da za ka je ka duba yawan waɗanda suka faɗi Turanci da Lissafin sai ka tarar da mutanen arewa ne mafiya yawa.
"Ba mu ɗauki Turanci a matsayin yaren da za mu riƙa yi a gida da tsakanin abokai da 'yan uwa ba. Mun ɗauki Turanci a matsayin yaren makaranta a yi shi a can a bar shi a wajen, ko kuma yaren wajen aiki.
"Su kuma mutanen kudanci shi ne babban yarensu da suke mu'amala ta ko ina da shi,'' in ji Tilde.

























