Yadda sabuwar fasaha ta gano sabbin duniyoyi a sararin samaniya

A image which looks like gold glitter and white sparkles is actually an open star cluster

Asalin hoton, ESA/Euclid/Euclid Consortium/NASA, CFHT, image processing by J.-C. Cuillandre and E. Bertin (CEA Paris-Saclay)

Bayanan hoto, Na'urar hangen nesa ta Euclid ta ɗauki wannan hoto mai nisan shekara 8,700 a tafiyar haske.
    • Marubuci, Sophie Abdulla
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Turai (Esa) ta fitar da wani hoto mafi girma, mai cike da bayanin haske da aka taɓa ɗauka na shurin taurari da duniyoyi na Milky Way.

Sama da taurari miliyan 60, da kuma duniyoyi da curin taurari, aka ɗauka ta hanyar na'urar hangen nesa ta Euclid.

Hoto ne da ba a taɓa son ɗauka ba.

An fitar da hoton ne domin nazarin sararin samaniya mai duhu wanda ba a iya gani.

Masana kimiyya sun nuna na'urar da aka ɗauki hoton da ita bisa buƙatar masu bincike don duba tsakiyar sashen taurarinmu na galaxy - wanda aka fi sani da 'galactic bulge'.

Na'urar ta Euclid na da sabbin fasahohin da ke ba ta damar ɗaukar hoto da kyau da kuma samo bayanan da ake buƙata game da ɗaiɗaikun taurarin da ke cunkushe a cikin galaxy.

Hoton ya samar da kalar yankuna tara, da kowanensu ya fi girman wata - lamarin da ya ƙara fito da bayanai masu yawa game da curin taurarin da kuma duniyoyi.

"A ƙididdiga ya kamata ka iya samun wasu duniyoyin da ba sa cikin rukunin duniyoyinmu na Solar System'', a cewar Xavier Dupac, mai amfani da na'urar hangen nesa ta Euclid.

A cewar hukumar kula da sararin samaniyar Amurka daga aukar hoton zuwa yanzu an gano duniyoyi 6,000 a wajen da'irar duniyoyinmu.

Wannan sabo hoto zai bai wa masana kimiyya su auna yawan duniyoyin da ke wajen da'irar duniyoyin Solar System, wanda zai bayar da muhimman bayanai, ciki har da bayanin ko za a iya rayuwa a cikinsu.

Haka kuma hoton zai taimaka wa masu ilimin taurari su gano sabbin duniyoyi ta hanyar amfani da sabuwar dabarar gano tauraro ta hanyar haskensa a jikin wani da aka fi sani da microlensing.

A wide view of the galactic bulge, which is the largest high-resolution photo ever taken of our Milky Way galaxy's centre in visible light

Asalin hoton, ESA/Euclid/Euclid Consortium/NASA, CFHT, image processing by J.-C. Cuillandre and E. Bertin (CEA Paris-Saclay)

Goyon hansken wasu taurarin

Abin da masana kimiyya ke nufi da microlensing shi ne wani tauraro ya goyi wani ta yadda ba za iya hango ɗayan ba.

Idan hakan ta faru tauraron da ke kusa da mu, zai zama kamar wani gilashi da ke ɗaukar hasken tauraron da ke bayansa.

Idan duniya tana zagaye tauraron da ke kusa da mu, nauyinta boye wannan haske. Irain waɗannan ƙarin bayanan su ke taimaka wa masana ilimin taurari gano wasu duniyoyin da ke wajen da'irar duniyoyinmu.

"Idan ka yi sa'a, za ka iya gano wasu duniyoyin,'' in ji Dupac.

An image which looks like gold glitter is actually a tightly packed area of stars

Asalin hoton, ESA/Euclid/Euclid Consortium/NASA, CFHT, image processing by J.-C. Cuillandre and E. Bertin (CEA Paris-Saclay)

Bayanan hoto, Wannan hoton ya nuna cunkushewar taurari masu tsananin haske.

To sai dai ba a iya gano sabbin duniyoyin da ke wajen duniyoyinmu ta hanyar hoton da aka ɗauka da na'urar Euclid kawai, akwai buƙatar ƙarin aiki.

Akwai buƙatar amfani da na'urar hangen nesa na tsawon fiye da kwana 20 domin gano tauraron da ya ɓuya a bayan wani.

To amma idan na'urar hangen nesa ta gano taurari biyu da ke goye da juna a wani wuri, zai taimaka wajen tabbatar da wanzuwar sabbin duniyoyin.

Valeria Pettorino ta shaida wa BBC cewa ta yi imanin wannan hoton zai taimaka wajen gano ƙarin ''dubban duniyoyi''.

Yiwuwar rayuwa a sabbin duniyoyi

A nebula image which shows clouds of ionised gas

Asalin hoton, ESA/Euclid/Euclid Consortium/NASA, CFHT, image processing by J.-C. Cuillandre and E. Bertin (CEA Paris-Saclay)

Bayanan sun buɗe ƙofa ga masana kimiyya domin su lissafa yawan duniyoyi.

Pettorino ta yi bayanin yadda tsawon lokaci ake samun ƙaruwar rabuwa tsakanin taurari biyu.

Ta ce idan tauraron da ya ki kusanci da mu, auna ƙafin zagayen wannan tauraron da kuma haskensa zai taimaka wa masu ilimin taurari wajen tantancewa girman wannan duniyar.

Zai taimaka wajen samar da ƙarin bayani game da duniyoyin da aka gano a baya.

An image which looks like gold glitter obscured by a dark shadow in the middle is actually showing a dark nebula

Asalin hoton, ESA/Euclid/Euclid Consortium/NASA, CFHT, image processing by J.-C. Cuillandre and E. Bertin (CEA Paris-Saclay)

Bayanan hoto, Wannan hoton da ka ɗauka ta na'urar hangen nesa ta Euclid ya nuna miliyoyin taurari da ke ɗauke da haske mai yawa.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shekaru 20 da suka gabata, wata tawagar masana da Beaulieu ya jagoranta ta gano sabuwar duniya a wajen da'ira duniyoyinmu. ''Duniya cike da daskararriyar ƙanƙara, mai kama da wani bigire da aka fafata yaƙi a cikinsa,'' in ji shi.

"Bayan wannan lokaci, Na yi murna cewa na'urar Euclid za ta ba mu damar auna yawan taurarin da aka gano''.

Sani yawan duniyoyin zai taimaka wajen fahimtar abubuwa masu yawa, kamar sanin yiyuwar rayuwa a cikinsu, a cewar Dupac.

"A taƙaice - kamar dai yadda muke gani a da'irar duniyoyinmu - akwai duniyoyi masu yawa waɗanda na gas ko ƙanƙara ne.. da ƙananan duniyoyin da ke kusa da duniyoyin duwatsu,'' in ji shi.

"Idan kana son yanayi mai kyau domin inganta rayuwa, to za ka iya zuwa duniyar duwatsu.''

Dupac ya ce "Za ka iya samun ƙarin bayanai daga na'urorin hangen nesa da ka ƙera da yanayin duka duniyoyin, domin gano wadda za a iya rayuwa a cikinta.

Za kuma a iya amfani da waɗannan bayanan domin faɗaɗa binciken kimiyya tsananin halittun sararin samaniya.