Shari'o'i nawa ake yi wa Nasir El-Rufai?

Asalin hoton, El-Rufai/X
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
An shafe kusan kwanaki 150 ana tsare da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a hannun hukumomi kan wasu shari'o'i da ake masa.
Daga cikin shari'o'in akwai waɗanda suke da alaƙa da rashawa da kuma waɗanda suka shafi tsaron ƙasa.
Hukumar DSS da ICPC dukkansu sun gurfanar da El-Rufai gaban kotu, tun bayan da suka kama shi a ranar 17 ga watan Fabrairun 2026.
Tsohon gwamnan ya sha musanta zarge-zargen.
Sai dai abin da yake ɗaure wa wasu kai shi ne yadda ake gabatar da shi kotuna daban-daban tare da bayar da belinshi a wasu lokutan amma kuma sai a sake gabatar da shi a kotu washegari.
To shin shari'o'i nawa ake yi wa tsohon gwamnan jihar Kadunan?
Yadda aka fara kama El-Rufai
Hukumar EFCC ce ta fara kama El-Rufai, kafin daga bisani ta miƙa shi zuwa ga takwararta ta ICPC da ke yaƙi da almundahana da laifukan da suka jiɓanci haka a ƙasar.
A ranar 1 ga watan Afrilun 2026 ne aka miƙa shi zuwa ga hukumar DSS bayan fara sauraron shari'arsa a wata kotu da ke Kaduna.
Kotuna biyu ne ke sauraron shari'ar El-Rufai - ta jiha da ta tarayya - kan laifuka da suka shafi zargin almubazzaranci da dukiyar jihar da kuma waɗanda suka shafi tsaron ƙasa.
Lauyan da ke kare Nasir El-Rufai, Ukpon Akpan ya buƙaci kotun da ta bayar da belin tsohon gwamnan, yana mai cewa hakan na cikin haƙƙinsa a kundin tsarin mulki.
A ranar 14 ga watan Afrilu, kotun tarayya ta bai wa El-Rufai beli kan Naira miliyan 200, inda ta umarci ya cigaba da zama a hannun hukuma har sai ya cika sharuɗɗan belin. To sai dai babbar kotun jihar Kaduna ta yi watsi da buƙatar bayar da belin.
Har yanzu kuma hukumomi na ci gaba da tsare shi a wajenta. Ko da yake dai an taɓa sakin shi na kwanaki biyu domin halartar jana'izar mahaifiyarsa.
Shari'ar ICPC

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wata sanarwar da ICPC ta fitar kan gurfanar da shi a gaban kuliya, hukumar ta ce tana tuhumar tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da zarge-zarge da dama da suka haɗa da:
- Karkatar da kadarorin gwamnati ba bisa ƙa'ida.
- Mallakar kadarorin jama'a ba bisa ƙa'ida ba.
- Halasta kuɗaɗen haram.
Sai dai a ranar Alhamis ɗin ta gabata, hukumar ICPC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai, da wasu shida kan tuhume-tuhume 11 da suka shafi zargin cin hanci da sauran laifuka a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna.
A cikin ƙarar da aka yi wa kwaskwarima, ICPC ta ambaci El-Rufai a matsayin wanda ake tuhuma na farko, da kuma tsohon babban mai ba gwamnan shawara na musamman, Jimi Adebisi Lawal, da wasu kamfanoni biyar.
Kamfanonin su ne; Singularity Network Security Limited, Solar Life Nigeria Limited Knowledge Investment Nigeria Limited, Intercellular Nigeria Limited da Noble Coast Resources Limited.
ICPC ta zargi El-Rufai da bayar da kwangilar sanya na'urar CCTV a birnin Kaduna a lokacin da yake gwamna kuma an bayar da kwangilar ne kan kuɗin da ya kai N8.68bn, ga kamfanin Singularity Network Security Limited.
ICPC ta ce kamfanin ba shi da isasshen ƙarewa da cancantar gudanar da aikin, kuma matakin ya saɓa wa dokokin saye da sayarwa na gwamnati.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa an riƙa tura kuɗaɗen da aka samu daga wannan aiki zuwa ga wasu kamfanoni da mutane daban-daban.
Akwai Bashir El-Rufai, babban ɗan uwan tsohon gwamnan, a ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen, inda hukumar ta ce tana nemansa ruwa a jallo.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya musanta zarge-zargen da aka yi masa ciki har da binciken da hukumar ICPC ta gudanar a gidansa wanda ya bayyana da "haramtacce".
Shari'a kan tatsar bayanai
Daya daga cikin manyan shari'o'in da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ke fuskanta ita ce wadda Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
A ranar 23 ga Afrilu, DSS ta gurfanar da El-Rufai bisa zargin saurarar wayar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ba tare da izini ba.
Hukumar ta shigar da tuhume-tuhume guda biyar a kansa a cikin ƙarar.
A ranar 18 ga Mayu, Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta ba shi beli, amma ya kasa cika sharuɗɗan belin. Tun daga lokacin ya ci gaba da zama a tsare.
A zaman kotun na baya-bayan nan, Babbar Kotun Tarayya ta ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 22 ga Satumba, 2026, domin ci gaba da shari'ar.
Ya shafe fiye da kwanaki 126 a tsare, kuma idan ya ci gaba da zama a tsare har zuwa ranar da aka ɗage shari'ar, adadin kwanakin da aka tsare shi za su kai 217.
A zaman kotun, DSS ta tabbatar da kammala gabatar da shaidunta bayan kiran shaidu biyu kacal. Shaidun su ne wani jami'in DSS da ya ba da shaida a watan da ya gabata, da kuma lauya kuma ɗan gwagwarmaya, Deji Adeyanju.
Lauyan masu gabatar da ƙara, Oluwole Aladedoye (SAN), ya sanar da kotu cewa sun kammala gabatar da dukkan shaidunsu.
Sai dai lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, ya ce ɓangaren su zai gabatar da buƙatar cewa babu hujjojin da za su sa a ci gaba da shari'ar.
Me ya sa ake ci gaba da tsare El-Rufai?
Babbar kotun jihar, a wasu bayanan hukuncin da ta yi a ranar 21 ga watan Afrilu, 2026, mai shari'a Darius Khobo ya ce buƙatar belin El-Rufai na cikin wata takarda mai sakin layi 24 da Muhammed Bala Aliyu ya gabatar.
El-Rufai a cikin buƙatar ya ce, laifukan da ake tuhumarsa ba manyan laifukan ƙasa ba ne, kuma a matsayinsa na tsohon gwamna, mazauninsa ba ɓoyayye ba ne kuma za a iya ganinsa a duk lokacin da ake buƙata.
Ya ƙara da cewa, ya dawo Najeriya a ƙashin kansa daga Masar saboda mutunta dokokin ƙasa, kuma yanayin lafiyarsa na buƙatar kulawar likitoci.
Sai dai alƙalin ya zayyano cewa ICPC ta ƙalubalanci buƙatar, inda ya ce zarge-zargen da ake yi wa El-Rufai sun shafi laifukan "zagon ƙasa ga tattalin arziki" kuma tana fargabar wanda ake zargin "zai riƙa katsalandan ga binciken da ake masa da ma sauran mutanen da ake ƙarar"
ICPC ta ba da misali da yadda El-Rufai ya yi tutsu a lokacin da aka samu sa'insa tsakaninsa da jami'ai a filin jirgin saman Abuja a watan Fabrairu, inda ta ƙara da cewa tsohon gwamnan "zai iya tsere wa kamu saboda matsayinsa a cikin al'umma"
Bugu da ƙari, "babu wasu sahihan hujjojin da aka gabatar da suke tabbatar da rashin lafiyarsa," in ji ICPC.
Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya shaida wa kotun cewa wanda ya ke karewa yana buƙatar belin ne "saboda ƴancinsa na ɗan ƙasa," buƙatar da lauyan ICPC Osuobeni Akponimisingha, ya ƙalubalanta.
A wane hali El-Rufai ke ciki?
Ci gaba da tsare Nasir El-Rufai ya janyo ce-ce-ku-ce, inda iyalansa ke ƙorafi kan lafiyarsa da suka ce tana cikin wani hali.
Ƴan'uwansa sun yi zargin cewa likitocinsa na fargabar ya fara samun matsalar cutar sankarar mafitsara, duk da cewa ana kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.
Iyalan El-Rufai sun kuma ce sun cika dukkan sharuɗɗan belinsa, sai dai sharadin samun babban ma'aikacin gwamnatin tarayya mai matsayi na 17 da ke da gida a Maitama ko Asokoro ne ya gagare su.
Ita ma ƙungiyar lauyoyin Najeriya, NBA, ta soki irin waɗannan tsauraran sharuɗɗan beli.
Shugaban ƙungiyar, Afam Osigwe, ya ce a wasu lokuta ana sanya sharuɗɗan ne da nufin hana wanda ake tuhuma samun beli, abin da ya ce ya sa tsarin beli ya zama tamkar hukunci.










