Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Messi, En-Nesyri, Wan-Bissaka, Hazard, Mbappe

Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi mai shekara 33 har yanzu bai tuntubi kowa ba a Paris St-Germain or Manchester City. A karshen kakar wasa ta bana kwantiraginsa za ta kare, lokacin da zai iya barin kungiyar ko kuma ya yi zamansa. (Goal)

Ana sa ran West Ham za ta sake kokarin dauko Youssef En-Nesyri, dan wasan gaba na Sevilla da kasar Moroko mai shekara 23 a cikin kakar wasa ta bana. (Star)

Kylian Mbappe na son komawa Real Madrid, inji Jese Rodriguez, wanda tsohon abokin wasansa ne a Paris St-Germain. (Marca)

Tsohon dan wasan Manchester United Fabio da Silva ya sanar da tsohuwar kungiyar tasa ta dauko wani dan wasan baya domin ba Aaron Wan-Bissaka, dan wasa mai shekara 23 abin da zai ja hankalinsa ya kara kokari. (Manchester Evening News)

Dan wasan baya na kasar Serbia Aleksandar Kolarov, mai shekara 35 da Matteo Darmian mai shekara 31 za su bar Inter Milan a ckin kakar wasan nan ta bana. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Dimitar Berbatov, tsohon dan wasan Bulgaria ya ba Real Madrid shawara ta sayar da Eden Hazard, dan wasan tsakiya mai shekara 30 wanda dan kasar Belgium ne. (Betfair via Marca)

Za a bar kungiyoyin gasar firimiya shida su rika buga wasa a Gasar Zakarun Turai daga 2024, inji wata shawara da hukumar kwallo ta nahiyar Turai UEFA ta fitar. (Telegraph - subscription only)

Cikin shawarwarin, za a bar manyan kungiyoyin kwallon kafa naTurai su buga wasanni a Gasar Zakarun Turan ko da kuwa ba su sami shiga kungiyoyi hudu na saman teburi a kasarsu ba. (The Times - subscription only)

Dan wasan gefe na West Brom Kyle Edwards, mai shekara 22 na cikin 'yan wasan da kungiyar Luton Town ta so saya a ranar da aka rufe kasuwar 'yan wasa - amma sai ya yi wa kungiyar da ke buga wasanta a matakin rukuni na biyu wato Championship tsada. (Birmingham Mail)

Dan wasan Barcelona na tsakiya Sergio Roberto, mai shekara 28 na iya shafe mako shida yana jinya bayan da ya sami rauni a kafarsa. Wannan na nufin ba zai buga wasan da kungiyar za ta yi da Paris St-Germain ba ta Gasar Zakarun Turai. (TV3 via Mundo Deportivo - in Spanish)