Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 26/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 26/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Kalli bidiyon yadda aka kuɓutar da Trump a lokacin harin

    Shugaba Trump na tsaka da tattaunawa da manyan baƙi lokacin da maharin ya buɗe wuta.

    Nan da nan jami'an tsrao suka yi nasarar kuɓutar da shi tare da fitar da shi daga ɗakin taron.

  2. Labarai da dumi-dumi, 'Wanda ake zargi ya ce jami'an Trump ya yi niyyar kai wa hari'

    Kafar yaɗa labarai ta CBS, ƙawar hulɗar BBC a Amurka, ta ce mutumin da ake zargi da kai harin Washington ya faɗa wa hukumomi cewa wasu jami'ai masu alaƙa da Trump ya yi niyyar kai wa hari.

    CBS ta ambato wasu majiyoyi biyu da ba ta ambaci sunansu ba na cewa an ji ƙarar harbin bindiga a ɗakin taron har sau biyar zuwa takwas.

    Tuni dai jami'an tsaro suka samu nasarar kuɓutar da Trump da mai ɗakinsa da sauran manyan baƙi daga wurin da lamarin ya faru.

  3. Hotunan yadda yansanda suka cika birnin Carlifonia domin bincikar gidan maharin

  4. Abin da muka sani kan mutumin da ake zargi da kai wa Trump hari

    Jami'an tsaron FBI sun fara fitar da bayanai kan mutumin da ake zargi kai da buɗe wuta a ɗakin taron da Shagaba Trump na Amurka ke halartar taro a birnin Washinton.

    Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce jami'an tsaron sun fitar da bayanai game da mutumin mai shekara 31.

    Ƴansandan sun bayyana sunansa da Cole Tomas Allen, wanda ke zaune a Torrance da ke birnin California a jihar Los Angeles.

    Kafar yaɗa labarai ta CBS, abokiyar hulɗar BBC ta ce Allen na aiki ne a matsayin mai koyarwa a Torrance bayan kammala karatunsa a cibiyar fasaha ta California.

    Ƴansanda sun kuma ce Allen ya sauka a otal ɗin da lamarin ya faru a matsayin baƙo, kuma yana ɗauke da makamai masu yawa, ciki har da bindigogi da wuƙaƙe.

    Tuni dai ƴansanda suka bazama gidansa da ke California domin bincikarsa.

  5. An fitar da Trump daga ɗakin taro bayan wani ɗanbindiga ya buɗe wuta

    Jami'an tsaron FBI sun samu nararar fitar da shugaban Amurka, Donald Trump daga wani taron cin abincin dare na ƙungiyar masu aiko da rahotonni daga fadar shugaban ƙasar da ake yi kowace shekara a birnin Washintong bayan da wani mutum ya buɗe wuta a wurin taron.

    Da yake jawabi daga fadarsa jim kaɗa bayan faruwar lamarin, Mista Trump ya ce wani mutum ne ɗauke da makamai ya yi yunƙurin kutsawa wurin da taron ke gudana.

    Lamarin ya faru ne lokacin da baƙi suka kammala cin abinci zagaye na farko, inda ka ji ƙarar harbin bindiga, a harabar ɗakin taron da ke Hotel ɗin Hilton a birnin.

    Jami'an tsaron FBI sun yi gaggawar kai wa Trump da mai ɗakinsa ɗauki inda suka yi nasarar fitar da su cikin kariya.

    Bayanai sun ce ɗaya daga cikin harsasan da aka harba ya samu wani jami'in tsaron da ke sanye da rigar kariya, wanda yanzu haka ke asibiti.

    Tuni dai aka kama mutumin da ake zargi da kai harin.

    Wannan ne dai karo na uku da ake yunƙurin kai wa Shugaba Trump harin bindiga a cikin shekaru ƙalilan.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.