Premier League: Man City ta yi wasa 13 ba a doke ta ba a gasar

Ranar Laraba Manchester City ta yi nasara a gidan Bunley a wasan mako na 22 a gasar Premier League ta ƙsar Ingila.

Gabriel Jesus ne ya fara ci mata kwallo minti uku da fara tamaula, sannan Raheem Sterling ya kara na biyu saura minti bakwai su tafi hutun rabin lokaci.

City mai kwantan wasa daya tana nan a matakinta na daya da tazarar maki uku tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Kawo yanzu kungiyar ta Etihad ta yi wasa 13 a gasar Premier ba tare da an doke ta ba ciki har da ciki har da canjaras biyu.

Karawar da ta yi canjaras biyu a wasa 13 nan sun hada da wanda ta tashi ba ci a Old Trafford ranar 12 ga watan Disamba da wanda kwana uku tsakani ta yi kunnen doki 1-1 da West Brom a Etihad.

Rabonda City ta sha kasha a gasar Premier tun bayan da Tottenham ta doke ta 2-0 ranar 21 ga watan Nuwamba, inda Heung-Min Son da kuma Giovani Lo Celso ska ci kwallayen.

Manchester City za ta ziyarci Liverpool domin buga wasan mako na 23 a gasar Premier League a Anfield.

Ranar 8 ga watan Nuwamba kungiyoyin sun tashi karawa kunnen doki 1-1 a wasan farko da aka yi a Etihad