Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Cristiano Ronaldo zai iya lashe manyan kofuna biyu a bana?
A ranar 23 ga watan Afrilu ne ƙungiyar Al-Nassr ta lallasa ƙungiyar Al-Ahli ta Qatar da ci biyar da ɗaya a wasan gab da ƙarshe na gasa ta biyu ta zakarun Asia da ake kira AFC Champions League 2 ko kuma ACL2 ta bana.
Bayan lallasa Al-Ahli a filin wasa na Zabeel Stadium da ke Dubai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, yanzu Ronaldo zai fafata ne da ƙungiyar Gamba Osaka ta ƙasar Japan a wasan ƙarshe.
Za a buga wasan na ƙarshe na a ranar 17 ga watan Mayu, wanda idan Al-Nassr ta samu nasara, kofin zai zama ɗoriya a kan kofunan nahiya da Cristiano ya lashe a baya.
Bayan wannan kofin na nahiya, yanzu haka Al-Nassr ta yi ɗare-ɗare a saman teburin gasar cin kofin Saudiya.
Wannan wani lokaci ne mai matuƙar muhimmanci a wajen Ronaldo a tarihinsa na ƙwallon ƙafa
A watan Janairun 2023 ne Ronaldo ya koma gasar Saudi, amma tun lokacin ake masa yarfe cewa ya gaza jagorantar ƙungiyar ta lashe babbar gasar ƙasar, ballantan gasar nahiya.
Kofi ɗaya tilo da ya lashe shi ne na gasar Arab Club a shekarar 2023, amma kuma gasar ba ta cikin waɗanda FIFA ta amince da su.
Wannan ya sa duk da irin rawar da ya taka wajen ɗaga darajar ƙungiyar da ma gasar baki ɗaya, wasu na ganin lashin lashe gasa a matsayin babban tabo ga nasarorin da ya samu na zura ƙwallaye da sauran su.
Al-Nassr na hango nasara
Yanzu dai Al-Nassr na hango nasarori biyu a jere, duk da cewa akwai fargabar kada ta yi dakon banza.
Al-Nassr ce ta farko yanzu a teburin gasar ta Saudi bayan wasa 29, inda ta lashe wasa 25, ta yi canjaras 1, sannan ka doke ta wasa uku. Yanzu jimilla tana da maki 76 a gasar.
Ƙungiyar Al-Hilal ce ke biye mata a matakin ta biyu a gasar, inda take da maki 68 a wasa 28 da ta buga. Sai dai ita ba a doke ta a wasa ko ɗaya ba, amma ta yi canjaras guda 8.
Kenan yanzu akwai maki 8 a tsakanin ƙungiyoyin biyu, duk da cewa Al-Hilal na da kwantan wasa ɗaya.
Idan ta samu nasara a wasan, zai zama tana da maki 71. Ke nan tazarar da ke tsakanin ƙungiyoyin biyu za ta koma maki 5.
A gasar Saudiya, tsarin gida da waje ake yi, kuma akwai ƙungiyoyi 18 da ke fafatawa.
Don haka kowace ƙungiya za ta fafata da sauran ƙungiyoyin guda 17. Kenan jimilla ana buga wasa 34.
Yanzu akwai sauran wasa biyar. Idan Al-Nassr ta ci gaba da samun nasara wasanni, misali ta samu nasara wasa uku ta yi canjaras a biyu, ko da Al-Hilal ta samu a nasara a duka sauran wasanninta, Al-Nassr ce da nasara.
Sai dai akwai wasa tsakanin Al-Nassr da Al-Hilal, wanda shi ne ake tunanin zai zama wasan raba-gardama a gasar.
Kofuna da Ronaldo ya lashe a baya
Ronaldo ya yi ƙoƙarin tun bayan komawarsa ƙungiyar Al-Nassr, inda ya zura ƙwallo 14 a kakar wasa ta 2022-23 a babbar gasar Saudiyya ta Saudi Pro League, bayan zuwa ƙungiyar a tsakiyar kaka.
Al-Nassr ta kammala a matsayi na biyu a kakar wasanni biyu na farko bayan isar sa, sai kuma ta ƙare a ta uku a kakar da ta gabata da maki 13 a bayan Al-Ittahad.
Haka nan Al-Nassr ta sha kashi a hannun Al-Hilal a wasan ƙarshe na Kofin Sarki – a gasar 2023-2024, a bugun fenariti.
Sporting CP
- Supertaça Cândido de Oliveira: 2002
Manchester United
- Gasar Premier : 2006–07, 2007–08, 2008–09
- FA Cup: 2003–04
- Football League Cup: 2005–06, 2008–09
- FA Community Shield: 2007
- UEFA Champions League: 2007–08
- FIFA Club World Cup: 2008
Real Madrid
- La Liga: 2011–12, 2016–17
- Copa del Rey: 2010–11, 2013–14
- Supercopa de España: 2012, 2017
- Zakarun turai wato Champions League: 2013–14, 2015–16, 2016–17, 2017–18
- UEFA Super Cup: 2014, 2017
- Gasar kofin FIFA Club: 2014, 2016, 2017
Juventus
- Serie A: 2018–19, 2019–20
- Coppa Italia: 2020–21
- Supercoppa Italiana: 2018, 2020
Al-Nassr
- Arab Club Champions Cup: 2023
Portugal
- UEFA European Championship: 2016
- UEFA Nations League: 2018–19, 2024–25