Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me zamu iya tunawa game da rangadin Fafaroma Leo XIV a Afrika?
- Marubuci, Ousmane Badiane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist BBC Afrique
- Marubuci, Paul Njie
- Lokacin karatu: Minti 5
A ranar Alhams ne, Fafaroma Leo ya bar ƙasar Equatorial Guinea zuwa birnin Rum bayan kammala rangadin kwanaki 11 a ƙasashen Algeria da Kamaru da Angola da kuma Equatorial Guinea.
Tafiyar kilomita 18,000, kwanaki 11 ita ce ziyarar Fafaroma ta farko a Afirika wadda fadar Vatican ta shirya da nufin yaɗa manufofin ɗariƙar Katolika a nahiyar Afrika.
Cocin ta yi iƙirarin ta na da mabiya ɗariƙar Katolika da yawansu ya kusan biliya 1.4 a duniya kuma da dama daga cikin mabiyanta ƴan Afrika ne.
A biranen Algiers da Yaoundé da Luanda da kuma Malabo, Fafaroma ya jaddada muhimmancin inganta dimukuraɗiyya da yaƙi da cin hanci da kuma mutunta ƴan Adam.
Ya gabatar da jawabai kai tsaye ga masu riƙe da muƙaman siyasa ya kuma taɓo batutuwan da suka haɗa da rashin daidaito da dimukuraɗiyya da kuma cin hanci.
Ziyarar Fafaroma Leo XIV a Afrika ta bayyana matsayin Cocin Katolika a nahiyar: Ta fidda yadda ɗariƙar ta ke tattaunawa da ɓangarori daban daban game da zaman lafiya da shugabanci na nagari tsakanin mabiya ɗariƙar Katolika.
Farfesa Magloire Kouakouvi masanin ilimin zamantakewa kuma ƙwararre a harkokin zaman lafiya a Cocin Katolika ya ce rangadin ci gaba ga ayyukan yaɗa manufofin Cocin.
Algeria: Tattaunawa da mabiya wasu addinai
Yayin rangadin Fafaroma ya fara sauka a ƙasar Algeria, ƙasar da mafiya yawan al'ummarta mabiya addinin Islama ne, an karrama Fafaroma inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin mabiya addinai.
A lokacin da ya gana da shugabannin addinin Islama da wakilan yankunan mabiya addinin Kirista ya buƙaci ɓangarorin biyu su yi watsi da tarihin banbanci a tsakaninsu su yi mu'amala da juna cikin girmamawa.
Da ya ke gabatar da jawabi ya yabawa sufayen Tibhirine da kuma wadanda wariyar launin fata ta shafa. Ya ja hankalin al'umma game da muhimmancin zaman lafiya mai ɗorewa.
Kamaru: Matasa da dimukuraɗiyya da kuma rabuwar kai
A Kamaru, Fafaroma ya ce matasa na da matsayi a zuciyarsa a lokacin da ake fuskantar rikicin siyasa, don haka sai ya nemi matasan su kasance wakilan zaman lafiya don kawo ƙarshen rikici.
Dubban matasa sun gudanar da wani buki da ya nuna matsayin Cocin yankunan su.
A Yaounde babban birnin ƙasar, Fafaroma ya yi Allah wadai da dukkan tsarin ci gaban da ba a sanya matasa a ciki, ya kuma yi kira da sanya matasa a siyasa.
Angola: Arziƙi da cin hanci da kuma adalci
ƙasa ta uku da ya ziyarta yayin rangadin nasa ita ce Angola.
A Luanda da kewayenta Fafaroma ya samu dandazon mabiya da yawansu ya kai 130,000 waɗanda ya jagoranta wajen gabatar da addu'o'i, lamarin da ya ƙara tabbatar da karɓuwar mabiya ɗariƙar Katolika a Kudancin Afrika.
A Cocin Muxima kuwa, wani yanki da ake kaiwa ziyara mai tarihin cinikin bayi, Fafaroma ya yi jawabi inda ya taɓo tarihin yadda aka azabtar da mutane da sunan bauta.
A Angola ƙasa mai arziƙin ma'adinai amma kuma al'ummar ƙasar ke fama da banbanci Fafaroma ya taɓo batun tattalin arziƙi da daidaito tsakanin al'umma.
Fafaroma ya soki yadda ake rikici kan dukiyar da ba wanda ya ke mora inda ya ɗora alhakin lamarin kan cin hanci da rashin shugabanci nagari.
Ya kuma taɓo yadda rikici a faɗin duniya ya ke laƙume biliyoyin kuɗaɗe.
Equatorial Guinea: Fafaroma ya yi kira a yi adalci tsakanin al'umma
Ƙasa ta ƙarshe a rangadin Fafaroma ita ce Equatorial Guinea.
Ranar Alhamis ya gabatar da taron addu'ar ƙarshe a rangadin sa a Afrika, dubban mutane ne suka yi dandazo a filin wasannain motsa jiki na Malabo babban birnin ƙasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo.
A ƙasar wadda ta yi ƙaurin suna wajen rashin ingancin dimukuraɗiyya Leo Leo XIV ya yi gargaɗi game da take haƙƙin marassa ƙarfi inda ya nemi hukumomi su raba arzikin ƙasar tsakanin al'umma gabaɗaya maimakon wasu tsiraru su kwashe arziƙin ƙasar.
Equatorial Guinea ƙasa ce mai arziƙin mai amma kusan rabin al'ummar ƙasar na fama da talauci kamar yadda bankin du niya ya bayyana.
Ƙungiyoyin Kare Haƙƙin Ƴan Adam sun zargi gwamnati da karkatar da kuɗaɗen shiga ga masu riƙe da manyan muƙamai maimakon al'umar ƙasar.
"Ɓillar rikicin ƙungiyoyin ƴan bindiga ta sanya ƴan ƙasashen ƙetare na kwashe arziƙin ma'adinan ƙasar," in ji Fafaroma.
Ya bayar da misali da ƙarancin filaye da ƙarancin abinci da rashin ayyuka a matsayin matsalolin da suka hana ƙasar ci gaba.
Lokacin da ya ziyarci wata kurkuku ya nemi mahukuntan ƙasar ta Equatorial Guinea su guji amfani da shari'a wajen horo kawai maimakon haka su yi amfani da ita wajen kare al'umma, ya kuma bayyana rashin jin daɗi game da yadda ake azabtar da fursinoni.
Ziyarar Fafaroma a Afrika ta bayyana matsayi da son zaman lafiya da kuma adalci irin na shugabannin Coci, ta kuma nuna yadda Fadar Vatican ta ke amfani da addini wajen sukar rashin adalci da kuma yadda ta ke kiran ƙasashen duniya su gina ƙasashen su da al'umma.