Yadda aka azabtar da ni saboda zargin maita

    • Marubuci, Todah Opeyemi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 5

Lokacin Ovey Friday yana ɗan shekara 13, matar mahaifinsa ta zarge shi da maita, inda ta kai shi wajen wani boka a jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

A wajen bokan an azabtar da shi matuƙa.

Kafin wani maƙwabcinsu ya lura da abin da ke faruwa ya sanar da ƴansanda, an riga an yi wa yaron illa sosai, illar da ba za a iya magancewa ba.

"Bokan ya kawo garwashi, ya zuba a tafin hannuna, ya haɗa hannuwana da ƙafafuna ya ɗaure, sannan ya zuba barkono a kan garwashin sannan ya lulluɓe ni da bargo," kamar yadda Friday ya bayyana wa BBC.

An yi hakan ne a lokacin matashin na da shekara 19.

Dole sai da likitoci suka yi masa allurar kashe zafin ciwo mai sa bacci kafin suka yi masa aiki.

A lokacin da Friday ya farfaɗo sai ya ga an yanke masa hannunsa na hagu, a hannunsa na dama kuwa, ko dai shi ma an yanke yatsune ne ko kuma an yi masu illar da ba za ta gyaru ba.

"Na yi kuka, kamar raina zai fita," a cewar Friday a hirarsa da BBC.

Daga baya, matashin ya zama abin kallo ga mutane a kan tituna.

"Na so a ce sun san ni a lokacin da aka haife ni," in ji shi.

Bayan wasu shekaru, mutane suna ta ƙura masa ido a hanya ko kuma su riƙa tsokanarsa.

"Na so a ce sun san ni, a lokacin da aka haife ni," in ji shi.

Yadda masu buƙata ta musamman ke faɗi-tashin neman ilimi da aiki a Najeriya

Duk da yana cikin ƙunci, amma yana da ƙwarin gwiwar samun nasara.

Amma ya samu tsaiko shekaru biyu da suka gabata, bayan da ya kusa rasa damar rubuta jarabawar share fagen shiga jami'a a Najeriya wato JAMB.

Na'urar ba za ta iya tantance zanen yatsun mutum irinsa ba, ko kuma ɗaukatar hoton yatsun da suka samu matsala.

Sai dai ya samu sa'a, da taimakon magabatansa da wasu ƙungiyoyin sa kai, an ba shi damar yin amfani da yatsun kafarsa a matsayin alamun tantancewa.

A yanzu Friday yana karanta harshen turanci a wata jami'a a jihar Nasarawa da ke maƙotaka da birnin tarayyar ƙasar Abuja.

Shi ne mutum na farko a danginsu da ya shiga jami'a.

"Ba kowa ne ke da wanda za su tsaya masa ba," in ji shi. "Wasu za su dakata a haka ne kawai," in ji Friday.

Scarlett Eduoku, wata mai gabatar da shirye-shirye a wani gidan rediyo a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta fuskanci irin wannan ƙalubalen, inda ta ce na'urorin tantance fuska ba sa iya gane fuskarta.

Ta rasa idonta na hagu ne tana shekaru 18.

Ta sha wahala a lokacin da ta yi ƙoƙarin sabunta layinta daga 3G zuwa 5G daga inda take, inda hakan ya ƙi yiwuwa.

Sai da ta je har hedikwatar layin sadarwar wayarta da ke Kano.

Fiye da 'yan Najeriya miliyan 35, kusan kashi 15% na al'ummar ƙasar, ake ƙiyasin suna rayuwa da wani nau'i na naƙasa, a cewar babban sakataren hukumar naƙasassu ta kasa (NCPWD), Ayuba Burki-Gufwan.

Majalisar dokokin ƙasar ta zartar da wata doka a shekarar 2019, wadda ta haramta nuna wa nakasassu wariya tare da ba su damar yin aikin gwamnati.

Dokokin ne suka kai ga kafa hukumar NCPWD don tabbatar da ƴancinsu, amma duk da haka "lamarin na tafiyar hawainiya", kamar yadda Burki-Gufwan ya shaida wa BBC.

Sai dai ya ce yana da yaƙinin "sannu-sannu ba ta hana zuwa"

Burki-Gufwan ya ce ana samun wasu ci gaba - domin hukumar Jamb ta rage kuɗin jarabawar ga mutane masu naƙasa, kuma ta samar da wasu cibiyoyi na musamman ga masu buƙata ta musamman.

Ita ma jami'ar Tarayya ta Lafia, da ke Nasarawa ta rage kashi 75% na duk kuɗaden makaranta ga ɗalibai masu naƙasa.

"Daga wannan lokacin, jami'ar ta ga ƙarin masu shiga makarantar," in ji Burki-Gufwan, inda ya ƙara da cewa "kowane ɗalibi mai buƙata ta musamman na son ya ci gajiyar tsarin".

Wani malami da ke Legas Chukwuemeka Chimdiebere ya ce dole ne Najeriya ta ƙara ƙaimi wajen magance buƙatun naƙasassu.

"Ba da dama ga kowa ba wai alfarma ba ce, nauyi ne," Kamar yadda ya shaida wa BBC.

Wannan kuma a cewarsa ya wuce maganar yin ginin da za su iya hawa.

Akwai buƙatar samar da masu fassara a azuzuwa, da kayan karatu ga masu lalurar gani, da ƙwararrun malamai da kuma na'urorin zamani da za su yi wa kowa aiki.

"Yawancin masu buƙata ta musamman na fuskantar ƙalubale ne daga wasu tsare-tsare da ba su taimakonsu," in ji Chimdiebere.

Abiose Falade, mai shekaru 48, da ke birnin Ibadan, tana amfani da kujerar guragu inda ta ce "naƙasa wata jarabawa ce a rayuwa".

"Zai iya faruwa da kowa a farkon rayuwarsa ko nan gaba. Wani lokacin kuma mutum zai rayuwa a haka har karshen rayuwarsa. Amma kuma wannan halitta ce ta ubangiji."

Falade ba ta gane tana da bambanci da sauran mutane ba sai da ta fara makaranta lokacin da ta ke da shekaru 10 a duniya.

Ta ce: "Duniya ba ta buƙatar mutane masu naƙasa"

Ta ce har yanzu tana ganin: "Akwai wuraren da zan iya zuwa, akwai kuma inda ba zan iya zuwa ba."

"Idan zan fita, nakan je tare da wani saboda idan mutane suna kallo na ko nuna ni, ba zan maida hankali ba. Ya fi sauƙi a kan a ce ni kaɗai ce."

A yawancin biranen Najeriya, babu hanyoyin bi da kujerun guragu a ma'aikatu da sauran gine-gine gwamnati ko bankuna da asibitoci, kuma na wahalar da masu naƙasa wanda dole sai sun nemi taimako.

Abin damuwar ma shi ne, Najeriya na shigar da kujerun guragu da na'urorin jin magana a ƙasar daga ƙasashen ƙetare ne.

"Idan mutum 9 daga cikin mutane 10 masu lalurar naƙasa na buƙatar wata na'urar taimako, kuma ba mu iya ƙera ko ɗaya daga cikin irin wadannan a gida, to lallai akwai jan aiki a gabanmu," in ji Burki-Gufwan.

Maso hanƙoro na son ganin an ware kashi 1% na kasafin kuɗi wajen tallafa wa masu buƙata ta musamman a duk matakan gwamnati.

Opeyemi Ademola mai shekara 28, wanda mai kula da ayyuka ne a wani kamfani da ke Lagos na fama da lalurar da ba kowa ne zai iya ganewa ba sai wanda ya yi hulda da shi.

Yana fama da lalurar rashin ji yadda ya kamata, saboda haka a duk lokacin da ake taron ma'aikatan kamfani dole sai ya mayar da hankali sosai, kuma idan akwai hayaniya da yawa hakan na wahalar da shi.

"Mutane na ganin cewa idan ka iya magana rangaɗadau ba ka da wata matsala ta ji," in ji shi.

Abubuwa masu sauƙi kamar rubuta taƙaitaccen bayani game da abubuwan da aka tattauna a lokacin taron ma'aikata, da kuma rubuta abin da ake faɗa na bidiyo zai iya taimakawa sosai.