An kai gawar Khamenei birnin Najaf a Iraqi
Ana ci gaba da gudanar da jana'izar tsohon jagoran addinin Iran Ali Khamenei a birnin Najaf na Iraqi, ɗaya cikin wurare masu tsarki ga mabiya shi'a.
Dandazon masu makoki na biye da gawarsa yayin da ake ci gaba da zagayawa bisa titunan birnin inda aka nufi masallacin Imam Ali da gawar.
Wasu daga cikin masu makokin ke furta kalaman adawa da Amurka wasu kuma na dauke da tutar mayaƙan Iraki masu samun goyon bayan Iran.
Kammala wannan ziyara a Iraq na daga cikin shirye-shiryen jana'izar da aka tsara kafin a kai gawar zuwa Mashhad, mahaifar Khamenei, inda ake sa ran za a binne shi.