Wace riba Amurka da Iran suka samu daga yarjejeniyar da suka ƙulla?

    • Marubuci, Amir Azimi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior News Editor - Persian Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Fiye da kwana 100 tun bayan da Amurka da Isra'ila suka fara jefa bama-bamai kan Iran, yanzu an kawo ƙarshen yaƙin a hukumance, inda duka ɓangorin ke iƙirarin samun nasara - wata alama da ke nuna yadda kowannensu ke ɗaukar nasara.

Yarjejeniyar ta kawo ƙarshen yaƙin a hukumance, amma yanzu za a fara tattauna batutuwa masu tsauri.

Kowanensu ya yi iƙirarin samun nasara, amma masu sharhi na ganin babu ko ɗaya daga ciki da ya samu cikakkiyar nasara, haka ma masu suka a cikin gida na ganin an yi sassauci sosai.

Ga Iran, yarjejeniya da Amurka wani abu mai muhimmanci na dakatar da wuta: la'akari da abin da wasu ke ganin ba za ta iya jure wa yaƙin ba, idan ba ta miƙa wuya ba, amma hakan ya sa ta zama kamar jan wuya.

Da farkon yaƙin, Babban burin Iran ba shi ne cin galaba kan Amurka da Isra'ila ba ta fuskar soji.

Burinta shi ne gama yaƙin ba tare da rusa mata tsarin mulkinta na Jamhuriyar Musulunci ba, kuma har yanzu tsarin shugabancinta na aiki yadda yake a baya, kuma tarin shiga tsakaninta na nan daram.

Yarjejeniyar da aka cimma ya nuna Iran ta cimma waɗannan duka.

Takardun yarjejeniyar da shugaba Trump da takwaransa na Iran suka sanya wa hannu a wurare daban-daban, sun amince da kwana 60 domin kammala cimma yarjejeniya kan batun shirin nukiliyar Iran.

Haka kuma yarjejeniyar ta amince da dakatar da faɗa nan take, a duka ɓangarori ciki har da Lebanon tare da martana ƴancin kowane ɓangare da kuma sake buɗe mashigar Hormuz tare da janye rufewar da aka yi wa tasoshin ruwan Iran

Sharuɗan Iran na da muhimmanci, amma a ƙayyade suke. Tehran ta amince ta taimaka wajen wucewar jiragen ƴan kasuwa ta mashigar Hormuz, wani abu da ke faruwa gabanin fara yaƙin, ta kuma jaddada cewa ba za ta ƙera makamin nukiliya ba, za kuma ta shiga tattaunawa kan makomar sinadarin uranium dinta da aka inganta.

A nata ɓanagare sharuɗa Amurka na da faɗi. Yarjejeniyar ta nuna cewa Amurka za ta fara janye rufewar da suka yi wa tasoshin ruwan Iran, tare da aiwatar da sassauci kan takunkuman fitar da man Iran, da kuma sakin kadarorin Iran da aka kama aƙasashen waje, da kuma ƙoƙarin ɗage duka takunkuman da aka sanya wa Iran.

Sannan Amurkan za ta yi aiki da ƙawayenta na yankin domin samar da asusun aƙalla dala biliyan 300 domin sake gina wuraren da aka lalata a Iran.

Wannan ya sa aka rufe bakin masu sukar yarjejeniyar daga Iran. Yarjejeniyar ta sa shugabannin Iran na kallonta a matsayin nasara.

An mutunta ƴancin Iran, an janye toshewar da aka yi wa tasoshin ruwanta, ana ƙoƙarin sassauta takunkumai sannan ga batun tara asusun sake gina wuraren da aka lalata.

Kuma da alama shirun da ƙasar ta yi kamar ta gamsu ne, ko a martanin jagoran addinin ƙasar ma, Mojtaba Khamenei, za a iya fahimtar hakan.

Ya amince a ci gaba da yarjejeniyar, inda aka bayyana cewa majalisar tsaron ƙasar ta amince da ita.

Batutuwa mafiya wahala an jingine su, ba a warware su ba.

Makomar yawan sinadarin uranium da ka inganta, da kuma kamfanonin inganta sinadarin da batun sake gina cibiyoyin nukiliyar da aka lalata yanzu za a tattaunawa cikin matsin lamba.

Wannan kuma zai iya haifar da matsalar ga tsarin shugabancin Iran. Kafofin yaɗa labaran ƙasar da Rundunar juyin juya hali da kuma jiga-jigan ƙasar masu tsattsauran ra'ayi sun shafe makonni suna yaɗa cewa Iran ta yi galaba a kan Amurka da Isra'ila.

Trump na kallon yarjejeniyar a matsayin 'babbar nasara'

Donald Trump ya ayyana yarjejeniyar a matsayin 'babbar nasara' ga Amurka wanda ya ƙunshi babban burinsa a yaƙin wata hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Wata 'nasarar' kuma ita ce sake buɗe mashigar Hormuz, wadda ɗaya ce daga cikin ginshinƙan hanyoyin tattalin arzikin duniya.

Yayin da ake ci gaba da yaƙin mashigar ta kasance a rufe, kuma alƙaluma sun nuna cewa Amurkawa na ci gaba da jin raɗaɗin tsadar man fetur don haka yaƙin yana yin tasiri a cikin gida.

Rashin gamsuwa da yadda tsarin tattalin arzikin Amurka ke tafiya shi ne babban dalilin da ya sa suka sake zaɓen Trump a 2024, kuma yaƙin na cutar da tattalin arzkin ƙasar, wadda kuma yake shafar farin jinin Trump a hukumance.

Kuma yayin da jam'iyyarsa za ta fuskanci zaɓen rabin wa'adi a watan Nuwamba, wanda kuma ke tunanin zai zi a mawuyacin lokaci ga ƴan jam'iyyar Republican, da dama daga cikin ƴanjam'iyyar ba sa jin daɗin yaƙin saboda zai iya shafar farin jinin jam'iyyar.

Yayin da wannan ke zuciyarsa, yarjejeniyar ta bai wa Trumo damar numfasawa, tare da farfaɗo da fatan abokan siyasarsa, kuma ya samu damar bayyana kansa a matsayin wanda ya kawo ƙarshen yaƙin.

To sai dai masu sukar yarjejeniyar - ciki har da ƴan Republican sun zargi Trump da alƙawarin fitar da kuɗi masu yawa a cikin yarjejeniyar.

Babban abin da ake fi ce-ce-ku-ce a kai shi ne alƙawarin asusun dala biliyan 300 domin sake gina wuraren da aka lalata a Iran.

Kodayake wasu jami'an gwamnatinsa sun kare batun da cewa Amurka ba za ta bayar da ko sisi cikin kuɗin ba.

To amma Trump ya sake fayyacewa ƙarara cewa ba Amurka ce kawai za ta bayar da kuɗin ba.

Haka ma a farkon yaƙin Trump ya sha alwashin cewa sojojin Amurka za su 'lalata makaman linzamin Iran da cibiyoyin ƙera su''

Sannan kuma yarjejeniyar ba ta taɓo batun alaƙar Iran da ƙungiyoyin da ke mara wa baya ba, duk kuwa da alƙawarin da Trump ya yi cewa Amurka za ta tabbatar ''gwamnatin Iran ba ta ci gaba da da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ba ta hanyar ba su makamai da kuɗaɗe da kuma sojoji''.

A yanzu Gwamnatinsa da alama ta janye wannan ƙuduri, inda mataimakin Trump, JD Vance ya shaida wa masu aiko da rahotonni cewa Am urak na ''sa ran'' Hezbollah za ta dakatar da harba makamai zuwa cikin isra'ila.

Wannan kawai zai sa tauye yarjejeniyar tsakanin ƴan Republican, waɗanda ke kallon kishin Amurka ga tsaron Isra'ila a matsayin wani ginshiki a siyasar Amurka.