Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane tasiri arewa maso yammacin Najeriya ke yi a zaɓen shugaban ƙasa?
Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ya daɗe yana taka muhimmiyar rawa wajen tantance wanda zai zama shugaban ƙasar, kasancewar shi ne yankin da ke da mafi yawan masu rajistar zaɓe a ƙasar.
Yankin ya ƙunshi jihohi bakwai, wato Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara, waɗanda ke samar da miliyoyin ƙuri'u a duk lokacin zaɓen shugaban ƙasa.
A cikin waɗannan jihohi, Kano, Kaduna da Katsina ne suka fi yawan masu rajistar zaɓe, lamarin da ya sa ƴan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyunsu ke mayar da hankali wajen neman goyon bayansu.
Sai dai ko har yanzu Arewa maso Yamma na da ƙarfin da zai iya karkata akalar zaɓen shugaban ƙasar Najeriya?
Me ya sa Arewa maso Yamma ke da muhimmanci?
Babban abin da ya sa Arewa maso Yamma ke da muhimmanci a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya shi ne yawan masu jama'a da yankin ke da su idan aka kwatanta da sauran shiyyoyin ƙasar, in ji Farfesa Kamilu Sani Fagge, mai sharhi kan lamuran siyasa.
Bisa bayanan Hukumar Zaɓe ta Najeriya (INEC), na rajistar masu zaɓe kafin zaɓen 2023, yanki ne da ke da mafi yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya, inda jimillar masu rajista ta haura miliyan 22.
Farfesa Fagge ya ce wannan ya sa duk ɗan takarar shugaban ƙasa da ke son samun nasara kan yi ƙoƙarin samun gagarumin goyon baya daga yankin, domin yawan ƙuri'un da ake kaɗawa daga yankin na iya yin tasiri sosai kan sakamakon zaɓe.
Baya ga yawan masu zaɓe, yankin na da wasu manyan jihohi da ke bayar da ƙuri'u masu yawa.
Sai dai masana siyasa na cewa muhimmancin Arewa maso Yamma ba ya ta'allaƙa ne kawai kan yawan masu zaɓe ba.
"Kusan ta fi kowane yanki yawan jihohi a ƙasar, kuma tana da manyan jihohin da yawan ƙuri'unsu, sun fi Kudu maso Kudu," in ji masanin.
A zaɓukan baya, kusan dukkan manyan ƴan takarar shugaban ƙasa sun riƙa gudanar da yaƙin neman zaɓe sosai a jihohin yankin, tare da yin alƙawuran da suka shafi tsaro, noma, tattalin arziki da samar da ayyukan yi, saboda muhimmancin ƙuri'un yankin wajen tantance wanda zai zama shugaban ƙasa.
Bambancin Arewa maso Yamma da sauran shiyyoyin Najeriya
Bayanan hukumar zabe ta INEC na rajistar masu zaɓe ta 2023 sun nuna cewa Arewa maso Yamma ce ke kan gaba da masu rajistar zaɓe 22,255,562, adadin da ya zarce na kowace shiyya a Najeriya.
Ga yadda jimillar masu zaɓe yake a shiyyoyin ƙasar:
- Arewa maso Yamma - 22,255,562
- Kudu maso Yamma - 17,958,966
- Arewa ta Tsakiya - 15,363,731
- Kudu maso Kudu - 12,674,248
- Arewa maso Gabas - 12,542,429
- Kudu maso Gabas - 10,907,606
Arewa maso Yamma kaɗai na da masu rajistar zaɓe sama da miliyan 22.2, adadin da ya zarta na yankin Kudu maso Gabas da kusan mutum miliyan 11.3, sannan ya zarce na Arewa maso Gabas da kusan miliyan 9.7.
Haka kuma, tazarar da ke tsakanin Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma, wadda ita ce ke biye da ita a yawan masu rajista, ta kai fiye da mutum miliyan 4.2.
Ko da yake hukumar INEC a baya-bayan nan ta fitar da sanarwar da ke nuna cewa an samu ƙarin masu rijista, domin hukumar ta fara sabunta bayanan masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
A cikin bayanan da INEC ta fitar ranar 26 ga Yunin 2026, hukumar ta ce ta samu ƙarin mutane 1,565,873 da suka kammala rajistar zaɓe a ƙarshen mako na bakwai na aikin sabunta rajistar masu zaɓe.
INEC ta bayyana cewa cikin wannan adadi, mutane 620,933 sun kammala rajistarsu a matakin farko ta intanet, yayin da 944,940 suka yi rajista kai tsaye a cibiyoyin hukumar.
Sai dai hukumar ta ce waɗannan alkaluman na wucin gadi ne, domin za a sake tantance su bayan kammala aikin sabunta rijistar.
A wannan alƙaluman ma, Kano ce take kan gaba wajen samun sabbin masu rajista, inda ta samu ƙarin mutane 118,207. Bayan Kano sai Lagos da ke da sabbin masu rajista 78,360, sannan Delta mai 76,395.
Jihohin da suka fi tasiri (Kano, Kaduna da Katsina)
Duk da yake dukkan jihohin Arewa maso Yamma na taka rawa a zaɓen shugaban ƙasa, akwai jihohi uku - Kano, Kaduna da Katsina - da suka fi jan hankali saboda yawan masu rajistar zaɓe da suke da su.
Su kaɗai ke da kusan rabin masu rajistar zaɓe na yankin.
A bayanan hukumar INEC na zaɓen 2023, jihar Kano ce ke da mafi yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya, da mutum 5,921,370. Bayan Kano sai Kaduna mai masu rajista 4,335,208, sannan Katsina mai 3,516,719.
Sauran jihohin yankin sun haɗa da Jigawa mai 2,351,298, Sokoto 2,172,056, Kebbi 2,032,041 da Zamfara 1,926,870.
Wannan na nufin Kano, Kaduna da Katsina kaɗai suna da fiye da masu rajistar zaɓe miliyan 13.7, adadin da ya zarce jimillar masu rajista na wasu shiyyoyin ƙasar baki ɗaya.
A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, jihar Kano ta ba jam'iyyar NNPP nasara, inda Rabiu Musa Kwankwaso ya samu kuri’a 997,279, yayin da Bola Tinubu na APC ya samu 517,341.
A Kaduna, Atiku Abubakar na PDP ne ya yi nasara da 554,360, Tinubu ya samu 399,293. A Katsina kuwa, Atiku ya samu 489,045, yayin da Tinubu ya samu 482,283, inda aka samu tazarar ƙuri'u ƙalilan.
Wannan ne ya sa ƴan takarar shugaban ƙasa ke yawan gudanar da manyan gangamin yaƙin neman zaɓe a waɗannan jihohi tare da neman goyon bayan manyan jagororin siyasa da na addini.
Dalilin da ya sa ake ganin duk ɗan takarar da ke neman zama shugaban ƙasa ba zai iya yin watsi da Kano, Kaduna da Katsina ba.
Abin da zai iya sauya yanayin kaɗa ƙuri'a a 2027
"A tsarin dimokraɗiyya, yawan al'umma na da tasiri sosai, saboda su ne ke fitowa su kaɗa ƙuri'a," in ji Farfesa Kamilu Fagge.
Ya ce idan har mutanen da suke da rijistar zaɓe za su fito su kaɗa ƙuri'arsu za a iya ganin sauyi, musamman yadda alƙiblarta ke sauya sakamakon zaɓe.
A zaɓen da shugaba Tinubu ya lashe a 2023, yankin Arewa maso Yamma ne ya fi bada ƙuri'u, "kuma zaɓukan baya ma haka ne".
Amma masanin ya ce saboda yawan tashe-tashen hankula da rashin tsaro a yankin za a iya samun ƙarancin fitowar jama'a.
Farfesa Fagge ya ce idan har ba a yi amfani da kuɗi ko wasu maguɗi ba, "za a ga sauyi sosai" a yawan ƙuri'un da za a kaɗa, kuma yankin zai iya zama wanda zai yanke hukunci a zaɓen 2027.
"Ƙuri'unsu ya isa ya sauya alƙiblar siyasar Najeriya," in ji Farfesa Fagge.
Ya ce idan har kuɗi ba su taka rawa wajen sayen ƙuri'a ba, ko kuma rashin tsaro ya hana mutane fitowa, jama'a za su iya nuna fushinsu ta hanyar kaɗa ƙuri'a ga jam'iyyar da ta musu ba daidai ba.