Sabbin hare-haren Iran kan Isra'ila: Wane saƙo hakan ke aikawa?

    • Marubuci, Amir Azimi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian editor
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Lokacin da Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka kan Isra’ila a tskar dare, a matsayin maryani kan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kan Hezbollah a Lebanon, nan take ba a ga cikakken tasirin harin ba. Sai dai tasirin siyasar lamarin shi ne abin da ya fi girma.

A tsawon shekaru, Iran kan kafa hujjar kai hare-hare kan Isra’ila a matsayin martani kan harin da Isra’ila ke kaiwa kanta ko kwamandojinta ko kuma wasu kadarori nata.

To amma wannan karo abin ya sha bamban. Iran ta dauki matakin ne sanadiyyar wani hari da Iran ta ce Isra’ila ta kai kan wani gini mallakin Hezbollah a kudancin birnin Beirut.

A ranar Litinin, rundunar sojin Iran ta ce za ta daina kai hari kan Isra’ila, to amma matakin kai harin tun farko ya haifar da tambayoyi: me ya sashigabannin Iran suka ga davewar daukar wannan mataki a wannan lokaci, ganin cewa za a oya fadawa cikin hadarin sake tsokano Isra’ila da kuma yiwuwar lalata yarjejeniyar tsagaita wura mai rawa da aka cimma da Amurka?

Yana iya yiwuwa amsar na tattare da abin da shigabannin Iran suka lura da shi bayan makonnin da aka kwashe ana yaki.

Ta wani fannin za a iya cewa Jamhuriyar ta Musulunci ta raunanan bayan yakin sai dai ta nuna jarumta ta hanyar nuna juriya.

Duk da tsananin matsi daga dakarun Amurka da na Isra’ila, da rakunkuman tattalin arziki, da toshe tashihin jiragen ruwan Iran, kasar ba ta rushe ba. Har yanzu ba a kawar da gwamnatin kasar ba, rundunar tsaronta na nan da karfinta sannan babu wata zanga-zanga da ta yi tasiri duk da shaci-fadi da aka sha ji daga ‘bangaren adawa.

Akwai yiwuwar abin da ya faru ya sauya lissafin kasar ta Iran.

A maimakon kasar ta ga kanta a matsayin mai rauni, kuma mai kokarin sake fadawa cikin rikici, da alama yanzu Iran na kallon kanta a matsayin wadda ta turje wa mafi munin barazana kuma a saboda haka yanzu tana iya shata layi.

Saboda haka nan harin da Iran ta kai kan Isra’ila zai iya zama ba mataki ne na ramuwa ba sai dai mataki ne na kandagarki. Hakan na iya nuna cewa Iran na nufin ba za ta amince da duk wani hari kan kawayenta ba a yankin.

Wannan sako zai zamo mai muhimmanci ga Hezbollah, da ‘yan bindiga a Iraq da sairan kungiyoyi masu alaka da kasar ta Iran.

Wani abu da ke kara wa Iran daraja a koda yaushe shi ne sanin cewa ba ta amincewa a taba kawayenta. Rashin daukar martani daga gare ta bayan ta fitar da garbadi a bayyane zai iya yin illa ga wannan martabar tata.

Haka nan ta wani fannin za a iya kallon wannan harin a matsayin ba a kan Isra’ila kawai ba, tamkar hari ne ka Amurka da kuma kawayen Irmsr’ila a fadin yankin, wadanda suka sanya ido domin ganin ko da gaske Iran za ta aiwatar da barazanar da ta yi.

Haka nan lokacin da Iran din ta yi amfani da shi wajen kai harin shi ma yana da duare kai.

A baya-bayan nan shigaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa da alama an kusa cimma yarjejeniya. Tunanin da kowa zai yi shi ne ewa Itmea za ta kauce wa duk wani abu da zai yi zagon kasa ga turbar diflosiyya da aka biyo.

To amma da alama Iran ba ta kallon lamarin ta wannan fannin.

Shugabannin Iran za au iya yin tunanin cewa sake nuna cewa har yanzu suna da karfi zai kara musu karfin fada a ji a teburin tattaunawa, a maimakon raunanawa.

Daga bangaren Iran, za ta ga cewa nuna cewa a shirye take ta yi amfani da kargin soji zai tunantar da Amurka da Isra’ila cewa Iran din na da zabi daban-daban.

Ba lallai ne cewa hakan na nufin Iran na son yarjejeniyar tsgaita wutar ta watse ba. Iran ta dauki matakin ne domin yin kurari da kuma aika sako a siyasance, sai dai ba lallai ba ne hakan ya hana sake rincabewar yaki ba.

Babu tabbas ko wannan lissafi nata zai yi daidai.

Martanin al’ummar Iran ya yi daidai da muhawarar da ake tafkawa.

Wasu na ganin cewa matakin da Iran ta dauka ya yi daidai. Wani mai bibiyar kafar yada labarai ta BBC Persia ya ce: “Matakin da Iran ta dauka na shigar wa Lebanon abu ne da ya dace.

“Tun bayan dokar makamashin nukiliya da aka yi da Iran, kasar ba ta taba karya dokokin duniya ba, sai dai wannan hare-hare na nuna daya bangaren, wato karya yarjejeniyar tsagaita wuta.”

Wannan kuma na nuna ayar tambaya kan ko mene ne Iran ke neman?: “An kwashe wata biyu ana fada (ana jefa bama-bamai) a kudancin Iran, amma babu wani kwakkwaran martani, hakan na almata cewa tamkar kudancin Lebanon ya fi kudancin Iran amfani.”

Amma wasu da dama na fargabar cewa me wannan takalar fada zai haifar. “A gaskiya zuciyata ta yi dukan uku-uku lokacin da aka sake fara yakin.” Kamar yadda wani mutum ya shaida wa shashen harshen Persia na BBC.

Wani abin kuma shi ne kila sake kai wannan harin na nuna rashin gamsuwa da yadda tattaunawa kan yarjejeniyar ke gudana. Idan Iran na ganin cewa ana neman ta sadaukar da abubuwa da dama ba tare da wani alfanu mai girma ba, wannan na iya zama neman kara tayar da kura kafin zagaye na gaba na tattaunawar.

Ko ma dai mene me, wannan harin na nuna cewa shugabancin Iran na kara samun karfi fiye da yadda ake zato daga waje.

Babbar ta bayar ita ba wai ko Iran za ta iya jure wa sabbin hare-haren Isra’ima kawai ba, shin za ta iya yin hakan yayin da take ci gaba da bin tafarki diflomasiyya.

Idan har haka ne, akwai yiwuwar Iran na yunkurin samar da sabon tsari ne a yankin: wanda zai sa ta koma kan teburin tattaunawa da karfinta tare da shat nata sharuddan.

Duk da hadarin wannan hanya, hakan zai saiya yadda Jamhuriyar ta Musulunci ke kallon tsaron yankin da kuma matayinta a Gabas ta Tsakiya.