Ko Iran ta yi nasara a yarjejeniyar da ta ƙulla da Amurka?

    • Marubuci, Amir Azimi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior News Editor – Persian Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shugabanin Iran na ƙoƙarin gabatar da yarjejeniyar fahimtar juna da ta ƙulla da Amurka, a matsayin wata gagarumar nasara ba miƙa wuya ba. Amma wannan ba abu ne da zo musu da sauƙi ba..

A yanzu dai ƙasar ta na ƙoƙarin farfaɗowa daga mummunan yaƙi da ya yi ma ta matuƙar ɓarna yayin da tattalin arzikin ƙasar ke fuskantar matsananciyar matsin lamba, kuma wani ɓangaren masu goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kwashe tsawon watanni suna yin Allah wadai da duk wani matakin sasantawa da Washington.

Haka kuma akwai ƴan ƙasar Iran a ciki da wajen ƙasar, waɗanda ke ganin rikicin matsayin wata dama ce ta sauya gwamnatin ba wai lokaci na diflomasiyya ba.

Wannan shi ne rabe-raben siyasar da gwamnatin ke fuskanta kuma a cikin wannan halin ta ke neman ta tallata yarjejeniyar.

Manyan jami'an Iran na tallata yarjejeniyar a matsayin nasara. Mohammad Bagher Qalibaf, shugaban majalisar dokokin ƙasar Iran kuma jigo a tattaunawar, ya ce Iran ta ɗauki dogon lokaci zuwa kai wa ga nasara ta ƙarshe.

Shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana yarjejeniyar da cewa za ta iya kawo sauyi, yana mai cewa idan har aka aiwatar da ita yadda ya kamata za ta iya magance yawancin matsalolin da Iran ke fuskanta da kuma haifar da wani yanayi na daban a Iran da kuma yankin gabas ta tsakiya baki ɗaya.

Matsayin Qalibaf yana da mahimmanci saboda ba a san shi da kasancewa mai matsakaicin ra'ayi irin na Pezeshkian ba; Goyon bayan da ya nuna wa yarjejeniyar a bainar jama'a ya nuna cewa yarjejeniyar tana samun goyon baya daga ɓangarorin gwamnati da ake yi wa ganin masu tsaurin ra'ayi, har ma daga cikin rundunar kare juyin juya halin Musulunci na Jamhuriyar Musuluncin.

Shugabannin suna kuma neman gabatar da yarjejeniyar a matsayin nasara domin a cewar Tehran, Amurka da Isra'ila sun gaza cimma manyan manufofinsu.

Ba su tilastawa Iran miƙa wuya ba, ba su kawar da Jamhuriyar Musulunci daga kan karagar mulki ba, ba su kawo ƙarshen shirin nukiliyar Iran ta hanyar soja ba, ba su kuma wargaza alaƙar Iran da Hezbollah ba.

A madadin haka, har yanzu Iran tana kan teburin tattaunawa, tare da shigar da Lebanon cikin tsarin ana kuma tatauna batun sassauta takunkumai.

Amma akwai wasu a cikin Iran da ke jayayya da wannan batu.

An bayar da rahoton cewa, wani ɗan majalisar mai rajin ra'ayin riƙau, mataimakin shugaban kwamitin tsaron ƙasa, ya bayyana daftarin yarjejeniyar a matsayin wata takarda da za ta mayar da Iran ta zama ƙarƙashin mulkin Amurka.

Ya kuma zargi masu shiga tsakani da yin watsi da umarnin jagoran addinin ƙasar na kada a sake buɗe mashigar Hormuz ga zirga-zirgar jiragen ruwan dakon kaya.

Wannan suka na da muhimmanci domin ba ta fito ne daga cikin gwamnatin. Ya fito ne daga ɗaya daga cikin cibiyoyin da ke sanya ido kan tsaron ƙasa.

Tsawon watanni, muryoyin masu tsattsauran ra'ayi a cikin majalisar dokoki da kafofin yaɗa labarai masu alaƙa da gwamnati da kuma taron masu goyon bayan gwamnati suna jayayya cewa ba za a iya amincewa da Amurka ba.

Sun yi nuni da cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da harkokin diflomasiyya jim kaɗan kafin a fara yaƙin, sun kuma ce gwamnatin Trump ta fake da batun tattaunawar ne yayin da Isra'ila da Amurka ke shirin ɗaukar matakin soji. A ganin su, duk wata yarjejeniya da Washington tana yanayi da miƙa wuya ce.

Amma duk da haka wasu daga cikin waɗannan muryoyin sun fara yin shuru yanzu. Hakan na iya nuna cewa an ba da izinin ci gaba da yarjejeniyar ne daga manyan matakan gwamnati. Ba yana nufin akwai cikakken haɗin kai ba.

Yana iya nuni da cewa, a yanzu, masu riƙe da madafun iko sun yanke hukunci cewa rashin amincewa da yarjejeniyar na iya haifar da mummunan sakamako.

Matsin tattalin arziki shine babban dalilin wannan lissafin.

Shugabannin Iran na iya gabatar da yarjejeniyar a matsayin sakamakon amfani da ƙarfin soja, gami da matsin lamba da ke tattare da rufe mashigar Hormuz da hare-hare kan cibiyoyin makamashin Amurka da ke yankin. Amma kuma tattalin arzikin ya tursasawa Tehran.

Yaƙin da takunkumai da hana zirga-zirgar jiragen ruwa, da tsuke kasuwannin man fetur da tsadar kayayyaki, da hauhawar farashin kayayyaki duk sun takurawa ƙasar da talakawan Iran.

Ga iyalai da yawa, tambayar ba ita ce ko yarjejeniyar ta yi kama da nasara ba, amma ko ta rage farashin kayayyaki kuma ko ta rage fargabar sake ɓarkewar yaƙin.

Mataimakin shugaban ƙasar Amurka JD Vance ya ce Iran ba za ta karɓi kuɗaɗen Amurkawa masu biyan haraji ba amma za ta iya samun damar samun biliyoyin daloli idan ta cika alƙawuran da ta ɗauka kuma aka sassauta mata takunkumai. Hakan ya bai wa Tehran damar gabatar da yarjejeniyar a matsayin hanyar sa samun hannun jari da sake gina ta maimakon dogaro da Amurka.

Duk da haka, haɗarin a bayyane yake. Ba a fitar da cikakkun bayanai kan yarjejeniyar ba, kuma ana sa ran za a fara tattaunawa a ƙasar Switzerland ranar Juma'a.

Batutuwan da suka fi ɗaukar hankali da suka haɗa da makomar sinadarin Uranium da Iran ke da shi, da matakin inganta sinadarin da aka amince da shi, da sassauta takunkumai, da Hormuz da kuma Labanon, za su kasance kan gaba tattaunawar.

Akwai kuma rashin tabbas game da Isra'ila. Firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya yi watsi da rahotannin da ke cewa Isra'ila za ta janye daga kudancin Lebanon, yana mai cewa sojojin Isra'ila za su ci gaba da zama a Labanon na tsawon lokacin da ya dace.

Shi kuwa Donald Trump, ya fito fili ya soki lamirin Isra'ila a Lebanon, yana mai cewa an kashe mutane da yawa. Ya kuma ce bai ji dadin harin da Isra'ila ta kai a Beirut jim kaɗan kafin cimma yarjejeniyar tsakanin Iran da Amurka ba, yayin da ya ce dangantakarsa da Natanyahu ta ci gaba da kasancewa mai aminci.

Ga Tehran, wannan takun saƙa tsakanin Washington da Isra'ila na da matuƙar muhimmanci. Ana iya gabatar da shi a matsayin shaida cewa matsin lambar da Iran ke yi ya dagula ƴancin da Isra'ila ke ganin tana da ita na yin abin da ta ga dama. Amma kuma yana sanya yarjejeniyar ta na tangal-tangal.

Idan Isra'ila ta ci gaba da aiki a Lebanon, Iran za ta fuskanci matsin lamba don mayar da martani. Idan Washington ba za ta iya hana Isra'ila ba, za a iya jayayya da iƙirarin Teheran na cewa yarjejeniyar ta ƙunshi Labanon.

Martanin masu sauraron sashen Persia na BBC sun nuna cewa ba kowa ne ya amnice da batun cewa yarjejeniyar nasara ba ce ga Iran.

Ɗaya daga cikin masu sauraron tashar ya ce sun damu matuƙa game da wani harin da Isra'ila ta kai, amma ko da suka ji labarin yarjejeniyar, ba su amince da ita ba kuma sun damu kan ko za a tafiyar da ƙasar yadda ya kamata idan yarjejeniyar ta ɗore.

Wani ɗan ƙasar Iran mai adawa da gwamnatin ƙasar, wanda tun da farko ya goyi bayan matakin sojan Amurka, ya sanya alamar tambaya kan abin da harin na Amurka ya cimma, tun da ba zai haifar da sauye-sauyen siyasa a Iran ba: "Fatan mu shi ne tsarin mulki ya sauya. To amma baya ga ƙunci da hauhawar farashin kayayyaki, da ƙara taɓarɓarewar tattalin arziki, wane fa'ida yake da shi ga mutane?"

Wasu kuma sun mara wa gwamnatin baya. Ɗaya daga cikin masu sauraron ya bayyana Iran a matsayin wadda ta yi nasara, yana mai cewa yaƙin ya nuna cewa yana mai cewa ''bara'' da ''roƙo'' ba su za su sanya a cire takunkumai ba, amma ana iya cire su ne ta hanyar amfani da ƙarfi.

Wani kuma ya yi taka-tsan tsan wurin yin maraba da yarjejeniyar, ta bai wa mutane damar komawa bakin aiki da rayuwa cikin kwanciyar hankali. "Ina tsammanin na ɗan lokaci ne," in ji su, "amma muna buƙatar samun ƴan watanni da za mu sarara mu samu kwanciyar hankali."

Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman gabatar da yarjejeniyar a matsayin nasara saboda ba za ta iya tallata ta a matsayin abin da ya zame ma ta dole ba.

Amma ga Iraniyawa da dama, ba za a auna nasararta ta hanyar kirari ba. Za a auna ta ne kan mizanin ko yaƙin ya tsaya, da samun sauƙin farashi, ko idan za a samu sauƙin takunkumai, da kuma ko shugabanni na iya tafiyar da matakin yarjejeniyar na gaba ba tare da ƙara samun wani tashin hankali ba.