Harin Rasha ya kashe mutum 13 a babban birnin Ukraine
Hukumomin Ukraine sun ce harin makami mai linzami da Rasha ta kai Kyiv, babban birnin ƙasar ya kashe aƙalla mutum 13 tare da jikkata sama da 40.
Rahotanni sun ce makamai masu linzami 20 ne na Rasha ta yi amfani da su wajen kai harin kan gidaje da wuraren ajiye kaya da wani asibitin yara.
Yayin da hukumomin ke ci gaba da yin ƙoƙarin ganin an mayar da wutar lantarki a wasu sassan birnin inda wasu mutane da dama suka maƙale a wurin da suke fakewa a birnin.


