Abubuwa 6 da INEC ta haramta game da yaƙin neman zaɓe

Hoton wasu ƴanbangar siyasa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da aka ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a hukumance a Najeriya, ƙofar ta buɗe ga jam'iyyu da ƴantakara domin yaɗa manufofinsu.

Hukumar zaɓen ƙasar, INEC ce ta ware lokacin domin bai wa jam'iyyun siyasa da ƴantakara dmar tallata wa masu zaɓe manufofinsu da ƙudurce-ƙudurcensu.

INEC ta bai wa jam'iyyun tare da ƴantakarsu kimanin wata biyar domin kammala yaƙin neman zaɓen.

Yaƙin neman zaɓe, lokaci ne da aka fi samun rikici da musayar wayu tsakanin mabiya jam'iyyu daban-daban a Najeriya, inda a wasu lokutan ma ake sabun tashe-tashen hankula.

Don guje wa hakan hukumar zaɓen ta haramta wasu abubuwa game da yaƙin neman zaɓen a tsawon wannan lokaci.

Mun kuma tuntuɓi hukumar ta INEC don jin abubuwan da ta haramta a lokacin yaƙin neman zaɓen, inda kuma ta aike mana da kundin sabuwar dokar zaɓen domin ganin dokokin.

Amfani da harshe mai kaushi

Saabuwar dokar zaɓen ta Najeriya da aka sabunta a 2026 ta haramta amfani da harshe mai kaushi da kalaman tunzura a lokacin yaƙin neman zaɓe.

''Ba za a yi amfani da kalaman cin zarafi, kai tsaye ko a fakaice ba a yaƙin neman zaɓe, ta yadda za su iya ɓata ko tada hankalin mabiya addinai, ƙabilu, ko wasu rukunan al'umma'', kamar yadda sabuwar dokar ta nuna.

Haka kuma, ba za a yi amfani da kalamai na cin mutunci ko rashin ɗa'a ko ɓatanci, ko wasu maganganu marasa tushe ba, ko kuma kalaman da aka tsara ko kuma ake sa ran za su tunzura mutane su aikata tashin hankali ko su haddasa zazzafan martani a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Wuraren ibada

Dokar INEC ta 2026 ta ce ba za a yi amfani da wuraren ibada ko ofisoshin ƴan sanda da kuma ofisoshin gwamnati wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe ko gangami ko jerin gwano ba.

''Haka kuma, ba za a yi amfani da waɗannan wurare wajen tallata ko yaɗa manufofin jam'iyyun siyasa ko ƴan takara, ko kuma wajen kai musu hari ba'', kamar yadda dokar ta nuna.

Amfani da ƴanbori

A cewar sabuwar dokar ba wata jam'iyyar siyasa ko ɗan takara da zai yi amfani da ƴan bori ko masu tsafi a lokacin yaƙin neman zaɓe ko kuma don cimma wata manufar siyasa.

Amfani da ƙarfi

Ba wata jam'iyyar siyasa, ko ɗan takara da zai ɗauki nauyi ko ya kafa ko ma ya shirya, horaswa ko ya tanadi kayan aiki ga wani mutum ko wata ƙungiya domin a yi amfani da su wajen amfani da ƙarfi da barazana ko tilasta wa mutane don cimma wata manufar siyasa ko wata fa'ida ta siyasa.

''Haka kuma, ba za a yi wani abu da zai sa mutane su yi zaton cewa an shirya ko an horas ko an tanadi irin waɗannan mutane ko ƙungiyoyi ne domin aikata irin waɗannan ayyuka ba'', in ji dokar.

Ba wata jam'iyyar siyasa ko ɗantakara da zai riƙe ko amfani da wata ƙungiyar tsaro mai zaman kanta da ke ɗauke da makamai ko kafa rundunar sa-kai, ko ma da wane suna ake kiransu, domin ba da tsaro ko taimako ko goyon baya ga jam'iyyar siyasa ko ɗan takara a lokacin yaƙin neman zaɓe da gangami da jerin gwano ko lokacin zaɓe.

Yi wa mutane barazana

Babu wata jam'iyya ko ɗan takara ko ƙungiyar siyasa da za su yi wa kowa barazana kai tsaye ko a fakaice ta hanyar amfani da ƙarfi ko tashin hankali a lokacin yaƙin neman zaɓe domin tilasta wa mutumin su goyi bayan wata jam'iyyar siyasa ko ɗan takara, ko kuma ya daina goyon bayansu.

Saka lokaci ɗaya don zuwa wuri ɗaya

Haka kuma dokar ta haramta wa jam'iyyun siyasa biyu ko fiye da haka yin taron yaƙin neman zaɓe ko gangami a wuri kuma a lokaci guda, kamar yadda Zainab Aminu ɗaya daga cikin masu magana da yawun hukumar.

Zainab Aminu ta ƙara da cewa dole ne kowace jam'iyya idan za ta yi taro ko gangami a wani wuri ta sanar da hukumar ƴansanda.