Yadda za ku kauce wa kamuwa daga ciwon idon Apollo

wata mata

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da ake samun rahotonnin ɓarkewar cutar ciwon ido ta Apollo, likitoci sun fara gargaɗin ɗaukar matakan kauce wa ciwon.

Apollo na haddasa kumburi da jajayen idanu tare da saurin yaɗuwa tsakanin mutane.

Ciwon na haifar da damuwa musamman a wuraren taruwar jama'a kamar makarantu da kasuwanni da ofisoshi, inda mutane ke yawan mu'amala da juna.

Apollo, wadda ake ganin a matsayin ciwo mai saurin yaɗuwa, na iya shafar mutane ba tare da la'akari da shekaru ko jinsi ba.

Masana lafiya na cewa ko da yake ba kasafai cutar ke haifar da matsaloli masu tsanani ba, tana iya janyo rashin jin daɗi da kuma katse harkokin yau da kullum na masu kamuwa da ita.

Me ke haddasa ciwon?

Dr Amina Hassan Wali, ƙwararriyar likitar idanu, shugabar Cibiyar kula da lafiyar Idanu ta Najeriya ta ce ƙwayar cutar Adenoviruses ce ke haifar da ciwon.

Ta ƙara da cewa ƙwayar cutar na yaɗuwa ne cikin sauri, musamman lokacin da yanayi ya yi sanyi, kamar damina ko hunturu.

Ta ƙara da cewa wata hanyar kamuwa da ciwon shi ne taɓa jikin mai ɗauke da ita.

Sauran abubuwan da ke haddasa yaɗuwar cutar sun haɗa da:

  • Taɓa ruwan ido ko kwantsar wanda ya kamu ciwon, sannan a taɓa ido ba tare da wanke hannu ba.
  • Musayar kayayyakin mutum kamar tawul, handkerchief, matashin kai, kayan shafa ko wasu abubuwan da suka taɓa fuska ko ido
  • Taɓa abubuwan da suka gurɓata da ƙwayar cutar, kamar ƙofar gida, teburi, waya ko wasu abubuwan da mai ciwon ya taɓa, sannan mutum ya shafi idonsa
  • Kusanci da mai ciwon lokacin tari ko atishawa, domin wasu ƙwayoyin da ke haddasa Apollo na iya yaɗuwa ta ɗigon numfashi
  • Rashin tsaftar hannu, musamman bayan gaisawa ko mu'amala da wanda ya kamu da cutar.

Mene ne alamominta?

Mata

Asalin hoton, Getty Images

Dr Amina Hassan Wali ta bayyana wasu daga cikin fitattun alamomin cutar da ta ce sun haɗa da

  • Ƙaiƙayin idanu
  • Raɗaɗi kamar an watsa ƙasa
  • Kumburin idanu
  • Sauyawar launin idanu zuwa ja
  • Samun ƙwansa
  • Zazzaɓi
  • Mura
  • Raɗaɗin maƙogoro
  • kwantsa a ido

Sai dai likitar idanun ta ce manyan alamomin ciwon su ne kumburin idanu da sauyawar launin ido zuwa ja.

Dr Amina ta bayar da shawarar gaggauta zuwa asibiti domin magani, don guje wa illar cutar.

''Idan ba a yi hankali ba, ciwon Apollo na haifar da ciwon hakiya, wanda ke rage ƙarfin ganin mutum'', in ji ta.

Ta gargaɗi masu amfani da maganguna barkatai, da cewa shi ido ba abin da za a yi sakaci da shi ba ne.

''Yawan amfani da magunguna barkatai a idanu ba tare da shawarar likita ba, na janyo makanta, don haka a guji sayen maganin ciwon ido da ka'', kamar yadda ta bayyana.

Matakan kauce mata

Dr Amina ta ce akwai matakan da ya kamata mutane su ɗauka don guje wa kamuwa ciwon na Apollo.

Matakan da likitar idanun ta lissafo sun haɗa da:

  • Kauce wa taɓa jikin mai ɗauke da ciwon
  • Gaggauta wanke hannu bayan taɓa jikin mai ɗauke da ciwon.
  • Mai ɗauke da ciwon ya guje wa shiga cikin mutane