Tsawon wane lokaci Iran za ta iya ɗauka tana yaƙi?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Saeed Jafari
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian political analyst
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Wata bakwai bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Iran da Amurka, kuma duk da matsin tattalin arziƙi da na ababen more rayuwa kan ƙasar, alamu sun nuna cewa har yanzu mahukuntan ƙasar ba su matsu a kawo ƙarshen yaƙin ba.
Iran na ƙoƙarin ganin cewa ba Amurka ce za ta tantance lokacin da za a kawo ƙarshen yaƙin ba - kuma za ta so ta ga cewa Amurka ta tafka ƙarin hasara a fannin soji da tattalin arziƙi da kuma a siyasance, ta yadda zai kai ga cewa Amurka ta amince da wasu daga cikin buƙatunta.
To amma hakan ya dogara ne kan amsar wannan tambaya: har tsawon wane lokaci ne Iran za ta iya ɗauka tana wannan yaƙi?
Tsawon wane lokaci ƙarfin sojin Iran zai jure wa yaƙi?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Wasu daga cikin masana'antun ƙera makamai da kayan soji na Iran na daga cikin wuraren da aka kai wa hare-hare, sai dai babu alƙaluma da za su tabbatar da irin ɓarnar da aka yi wa ɓangaren.
A wani tantancewa da ƙungiyar Chatham House ta yi a baya-bayan nan, ta ce babu tabbas kan adadin makaman da suka saura a rumbun Iran.
Yawan hare-haren da Iran ke ƙaddamarwa da miyagun makamanta masu linzami na raguwa. To amma ba za a iya tantance ƙarfinta na kasancewa a cikin yaƙin ta hanyar yawan makaman da take harbawa ba: yana da sauki a maye gurbin jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da aka yi asara.
Zuwa yanzu ƙasar ta maye gurbin kwamandojinta da aka kashe sannan kuma dabarun gudanar da ayyukanta na soji na nan daram.
Mohammad Ghaedi, malamin harkokin asashen waje a Jami'ar George Washington ya shaida wa sashen harshen Persia na BBC cewa "Akwai yiwuwar Iran za ta iya ci gaba da kai hare-hare na tsawon lokaci - ko da ba da yawa ba - kuma za ta iya ci gaba da kawo cikas a zirga-zirga ta Mashigar Hormuz."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Haka nan shugabannin Iran sun yi amannar cewa tsawaita yaƙin zai cutar da Amurka.
Ƙoƙarin tare hare-haren Iran ta sama ya laƙume da dama daga cikin tarin makaman Amurka, kuma wasu masu sanya ido na Amurka na ganin cewa maye gurbin wadannan makamai abu ne da ke ɗaukar lokaci.
Mista Ghaedi ya kuma ce "tasirin da yaƙin ya yi wajen tashin farashin mai da kuma asiyasar Amurka ta cikin gida ya bai wa Iran ƙwarin gwiwar cewa za ta iya tilasta wa Amurka amincewa da wasu daga cikin sharuɗanta".
A cikin gida, goyon bayan da Donald Trump ke da shi tsakanin ƴan jam'iyyar Republican na da ƙarfi har yanzu, amma alƙaluman jin ra'ayi tsakanin Amurkawa na nuna yadda ƙarin mutane ke ganin rashin dacewar yaƙin tare kuma da nuna damuwa kan cewa shugaban zai gaza cimma manufarsa ta yin nasara a yaƙin.
Idan har hasashen Iran ya zama gaskiya, burin ƙasar ba shi ne ta yi galaba kan Amurka ba: amma tsawaita yaƙin da ƙara yawan hasarar da Amurka ke yi zai ƙasar matsi.
A halin yanzu alamu sun nuna cewa amfani da ƙarfin soji kawai ba zai tursasa wa Iran daina yaƙin ba.
Tsawon wane lokaci tattalin arziƙin Iran zai jure?

Asalin hoton, Getty Images
Tun kafin fara yaƙin, tattalin arziƙin Iran na fama da tashin farashi, rashin zuba jari, durƙushewar darajar kuɗin ƙasar da kuma rashin tabbas a ɓangarori da dama.
Hasashen Bankin Duniya ya nuna cewa tattalin arziƙin Iya tsuke da kashi 2.7% tsakanin shekara ta 2025 zuwa 2026, wanda makonnin ƙarshen zangon ne kawai suka fado cikin lokacin yaƙin.
Sannan kuma yaƙin ya ƙara janyo matsi. Alƙaluma daga hukumar ƙididdiga ta Iran sun nuna cewa tashin farashi a cikin wata 12 ya kai kashi 62%.
Matsin ya fi shafar kudancin ƙasar wanda yaƙin ya fi yi wa illa: tashin farashi ya zarce kashi 101% a Hormozgan, a misali.
A ɓangaren samun ayyukan yi, yaƙin ya haifar da asarar guraben ayyukan yi sama da miliyan ɗaya, lamarin da ya jefa kimanin mutum miliyan biyu ba tare da aikin yi ba, in ji ƙaramin ministan ƙwadago na ƙasar.
Asusun Lamuni na Duniya - IMF- shi ma ya yi ƙiyasin cewa tattalin arziƙin Iran zai tsuke da kimanin kashi 5.4% a shekarar 2026 sannan tashin farashi zai kai kimanin kashi 69%.
Lokacin da za kwashe ana yaƙin da tarnaƙin da hakan zai yi ga harkar kasuwancin mai zai yi matuƙar tasiri.
Sai dai ba lallai ne matsi na tattalin arziƙi ya sauya ra'ayin Iran ba.
Mista Ghaedi ya ce gwamnatocin masu mulkin kama-karya na iya rayuwa na tsawon lokaci ko da a cikin mummunan yanayi.
A nasa ra'ayin, hauhawar farashi, rashin ayyukan yi da sauran matsi na tattalin arziƙi za su iya haifar da rashin gamsuwa tsakanin al'umma, amma ba lallai ne su shafi tsare-tsaren soji na Iran ba sai dai idan an samu mummunar zanga-zanga ko kuma rabe-rabe a cikin gwamnatin.
Bambancin ra'ayi Tehran: Tsawon yaushe za a kwashe ana yaƙin?

Asalin hoton, Getty Images
Ra'ayi bai zo ɗaya kan abin da zai faru a gaba.
Shugaban majalisar dokokin Iran kuma jagoran masu tattaunawar cimma yarjejeniya na ƙasar Mohammad Bagher Ghalibaf, a baya ya yi gargadi kan cewa bai kamata Iran ta jefa kanta cikin tarkon "dogayen rikice-rikice" ba.
Amma ɗan majalisar Iran mai tsattsauran ra'ayi Amirhossein Sabeti ya ce ko da Amurka ta amince da dukkanin sharuɗɗan da Iran ta gindaya, yaƙi bai ƙare ba.
Wannan rashin jituwa bai zamo rarrabuwar kai ba tsakanin "masu goyon bayan yaƙi" da "masu adawa da yaƙi ba": Haka nan kuma Ghalibaf ya ce ba zai amince da duk wata yarjejeniya da ba za ta tabbatar da ƴancin Iran ba.
Rashin jituwar ta fi kama da rashin matsaya daya kan tsawon wane lokaci ne matsin da Iran ke sanyawa zai ba da muhimmiyar dama, da kuma lokacin da za a iya cewa hasarar ta sha gaban ribar.
Mene ne ra'ayin al'umma? Babu sahihin alƙaluma kan ra'ayin al'umma game da ci gaban yaƙin, kuma ra'ayoyin da ake bayyanawa a shafukan sada zumunta ba su wakilci dukkanin ra'ayoyin al'umma ba.
Amma wata tattaunawa da BBC ta yi da Hamidreza Azizi, masani kan Iran kuma malamin wucin-gadi a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Jamus, ya nuna cewa abu mafi hadari ga gwamnatin Iran shi ne tarzoma daga cikin gida.
Ya ce matsalar ita ce saboda mummunan tashin farashi da lalacewar tattalin arziƙi da kuma ƙarancin abubuwan more rayuwa.
Yaƙin da ke neman dabarun kawo ƙarshensa

Asalin hoton, Getty Images
Yin yaki mai tsawo zai kuma iya zama koma-baya ga Iran a yankin Gulf. A shekarun baya-bayan nan Iran ta yi kokarin gyara dangantakarta da kasashen Larabawa da na yankin Gulf, musamman Saudiyya.
Ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin soji da kadarori da kuma hanyoyin sufurin jirgin ruwa na wadannan kasashe zai iya mayar da hannun agogo baya.
Ya zuwa yanzu wadannan kasashe sun yi kokarin ganin ba su zake ba, kuma suna ta kokarin ganin an yi sulhu. To amma idan suka ga cewa suna ci gaba da shiga hadarin hare-hare daga Iran ko kungiyoyin da ke mara mata baya, za su yi kokarin karfafa alakar tsaron su da Amurka, kuma watakila ma su juya wa Iran baya.
Duk wani matsi da Amurka za ta fuskanta daga tsawaitar yaki zai iya zama galaba ga Iran a siyasance idan har za ta iya cin gajiyar hakan a teburin tattaunawa. Har yanzu babu tabbas kan ko wane irin tayi ne zai zamo karbabbe ga Iran da za ta amince a kawo karshen yakin, haka nan babu tabbas kan yadda za a iya cimma wannan yarjejeniya.
”Abin da Iran ta gaza cin gajiya game da tsawaitar yakin shi ne kyakkyawan tsarin yadda za ta ribaci damar da ta samu domin cimma yarjejeniya mai dorewa,” in ji Mista Azizi.
Iran ta nuna cewa za ta iya kawo cikas ga hanyoyin wadatuwar makamashi na duniya lamarin da ke cutar da Amurka da kawayenta.
To amma akwai rashin tabbas kan tsawon lokacin da za ta iya kwashewa tana fito-na-fito da Amurka da kuma kasashen yankin Gulf.
Ya zuwa yanzu babu wani matsi na soji ko tattalin arziki ko na siyasa da ya zamo cikas ga Iran wajen ci gaba da yakin. To amma gwargwadon tsawaitar yakin, gwargwadon matsin tattalin arziki da gwamnati za ta fuskanta a cikin gida, haka nan gwargwadon lalacewar alakar da ke tsakanin kasar da makwabtanta kuma haka nan zai kara zama mai wuta a cimma yarjejeniya.











