Shugaba Paul Biya na Kamaru ya koma gida bayan shafe watanni biyu a ƙetare

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Kamaru, Paul Biya ya koma ƙasarsa bayan shafe fiye da watanni biyu yana wani abin da aka bayyana a matsayin "zama na ƙashin kai" a birnin Geneva na ƙasar Switzerland.

Biya mai shekara 93 a duniya, wanda kuma shi ne shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya da ke kan mulki, ya isa babban birnin ƙasar Yaoundé da yammacin ranar Alhamis tare da matarsa Chantal Biya. Kafafen yaɗa labaran gwamnati sun watsa dawowarsa kai tsaye.

A filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Yaoundé Nsimalen, daruruwan magoya bayan jam'iyyar CPDM mai mulki sun taru domin tarbarsa.

Sanye da tufafin da aka yi wa ado da hotonsa, magoya bayan sun yi ta raye-raye da kiraye-kirayen nuna farin ciki.

Hotunan da aka nuna kai tsaye sun nuna shugaban yana ɗaga hannu ga magoya bayansa daga cikin motarsa, ba tare da ya tsayawa ya yi magana da su ba. Haka kuma an nuna wani ɗan gajeren lokaci yana gaisawa da wasu manyan jami'an gwamnati.

..

Asalin hoton, Getty Images

Biya ya bar ƙasar ne tun ranar 7 ga Yuni, domin wata tafiya zuwa ƙasashen waje wadda tawagarsa ta bayyana a lokacin cewa gajeriyar tafiya ce.

Sai dai tsawaita zamansa a ƙasashen waje ya haifar da rade-radin cewa yana fama da matsalar lafiya, duk da cewa gwamnati ta musanta rahotannin da ke cewa an kwantar da shi a asibiti.

A yayin zamansa a ƙasashen waje, ya ci gaba da rattaɓa hannu kan dokoki da umarni na gwamnati, ciki har da wani babban sauyi a shugabancin sojojin ƙasar da kuma amincewa da gwamnatin ta karɓo bashin kuɗi daga cibiyoyin hada-hadar kuɗi na duniya.

A tsawon sama da kwanaki 70 da ya shafe a Turai, jam'iyyun adawa da masu sukar gwamnati sun yi iƙirarin cewa rashin tabbas kan tsawon lokacin zamansa a ƙasashen waje ya isa ya sa Majalisar Tsarin Mulki ta ayyana kujerar shugaban ƙasa a matsayin wadda babu mai riƙe da ita.

Sai dai jam'iyyar CPDM mai mulki ta mayar da martani da cewa shugaban yana gudanar da aikinsa ne daga ƙasashen waje kuma babu wani tanadi a kundin tsarin mulkin ƙasar da ke iyakance tsawon lokacin da shugaban ƙasa zai iya kasancewa a wajen ƙasar.

..

Asalin hoton, Getty Images

Shugaba Biya, wanda ya shafe kusan shekara 44 yana mulki, ya sha fuskantar suka kan yawan tafiye-tafiyensa na ƙashin kai zuwa ƙasashen waje.

Dawowarsa gida na zuwa ne bayan babbar nasarar da ƙungiyar ƙwallon ƙafan mata ta ƙasar, Indomitable Lionesses, ta samu a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta Mata (WAFCON) da aka gudanar a Morocco.

'Yan wasan sun dawo gida da kofin WAFCON na farko a tarihin ƙasar ranar Litinin, kuma ana sa ran shugaban ƙasar zai karɓe su a hukumance.

Sai dai har yanzu ba a san ko Mista Biya zai dawo gida a yau ba da ƙungiyar matan ta sha kashi a wasan ƙarshe na ranar Lahadi.

Yaya mulkin Paul Biya zai kasance a Kamaru yayin da yake tunkarar shekara 100?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan samun nasara mai cike da ruɗani domin zarcewa kan wa'adin mulki na takwas, shugaba mafi tsufa a duniya, Paul Biya, mai shekara 92, zai ci gaba da shugabanci wataƙila har gab da cika shekara 100 a duniya - idan har zai iya tukarar rikice-rikicen da ƙasar ke fama da su kenan.

Tuni jam'iyya mai mulki a ƙasar ta yi maraba da wannan nasar, sannan kuma Biya ya yi alƙawarin yin mulki cikin adalci.

Sai dai gabani da kuma ma bayan sanar da sakamakon al'umma sun kasance suna zaman ɗarɗar, bayan da babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary ya ayyana cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen.

Sai dai sakamakon zaɓen ya nuna cewa Biya ya samu kashi 54%, Tchiroma kuma 35%, lamarin da ya zo wa mutane da dama da mamaki sannan kuma wasu murna ta koma ciki.

"Yanzu Biya ya samu nasara ce amma mai rauni, ganin cewa da yawa daga cikin al'ummar ƙasar ba su yi amannar cewa shi ne ya lashe zaɓen ba," in ji Murithi Mutiga, daraktan sashen Afirka na Ƙungiyar lura da rikice-rikice ta duniya.

"Muna kira ga Biya da ya gaggauta shirin sasantawa a cikin ƙasa domin daƙile yiwuwar yaɗuwar rikici."

Masanin siyasa da tattalin arziƙi a Jami'ar Oxford, Francois Conradie ya ce: "Muna tunanin rikici zai iya rincaɓewa kasancewar ƴan Kamaru da dama sun yi watsi da sakamakon da hukuma ta fitar, kuma ba ma tunanin cewa gwamnatin Biya za ta yi ƙarko."

Biya wanda ya yi ƙaurin suna wajen kwashe lokaci mai tsawo a ƙasar Switzerland a otal, da wuya a gan shi a bainar jama'a - rashin ganin sa da aka yi na tsawon wata shida a bara ya sanya aka riƙa raɗe-raɗin cewa ya mutu.

..

Asalin hoton, Reuters

To sai dai ɗan siyasar, wadda ake wa laƙabi da "zakin maza" ba ya nuna aniyar kaucewa daga mulki a yanzu.

Biya wanda wanda aka haifa a yankin kudancin Kamaru, kiristocin mishan na Katolika waɗanda ya samu ilimi a hannunsu sun so a ce ya zama malamin coci ne.

To amma Biya a lokacin da yake matashi ya zaɓi ya karanta fannin shari'a da siyasa a Jami'ar birnin Paris, sannan bayan ya gama ya koma gida ya kama aikin gwamnati.

Mutumin mai ra'ayin sauyi ya riƙe muƙamai da dama, inda ya riƙe manyan muƙamai har ya samu shiga a wurin shugaban ƙasar na wancan lokaci Ahmadou Ahidjo, wanda ya kasance kan mulki tun daga lokacin da ƙasar ta samu ƴanci a shekarar 1960.

Ya kasance firaiminista mai matuƙar biyayya na tsawon shekara bakwai, har zuwa shekara ta 1982 - lokacin da Mista Ahidjo ya ɗauki wani mataki mai ban mamaki, inda ya ajiye aikinsa tare da naɗa Biya a matsayin shugaban ƙasa.

Mista Ahidjo ya ci gaba da zama shugaban jam'iyyar, yana tunanin cewa muƙamin shugaban jam'iyya ya fi ƙarfi a kan na shugaban ƙasa.

To amma a wannan lokaci sai Biya ya yi amfani da ƙarfi, ya kori duk mutanen Ahidjo daga gwamnati tare da tursasa wa Ahidjo tafiya gudun hijira.

Daga nan ya nuna kansa a matsayin jarumi, ta hanyar murƙushe yunƙurin juyin mulki sau biyu, ɗaya a 1983 da kuma wanda ya biyo daga baya.

Ana ganin cewa ɗaya daga cikin sirrin dadewarsa a kan mulki shi ne matarsa ta biyu, Chantal mai shekara 38, wadda ya aura a 1994.

Wadda ta yi suna da shigarta da kuma launin gashinta, ayyukanta na tallafa wa al'umma sun sanya ta yi suna a kafafen sada zumunta.

Kafafen yaɗa labarun Kamaru na yi mata laƙabi da wadda ta mallake zukatan al'umma, wani abu da ya sa ta cike gurbin rashin jin duriyar shugaban.

Mutanen biyu sun haifi yara biyu, kuma har akwai wasu zakuna da aka sanya wa sunansu a gidan namun daji na Mvog-Betsi da ke Yaounde.

Haka nan sun yi ƙaurin suna kan rayuwar ƙasaita da suke yi a kasar ta Kamaru.