Ko AI zai kori jaruman Kannywood?

Dirty Game

Asalin hoton, YUSRAH VENTURES FILM PRODUCTION

Bayanan hoto, Jaruman fim ɗin "Dirty Game" na kamfanin Yusrah
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ana cigaba da tafka muhawara kan yiwuwar amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI wajen shirya fina-finan Hausa, tun bayan da fim mai suna "Dirty Game" da aka yi da Ingilishi amma da zubin Hausa ya fito.

Fim ne da aka yi kacokam da ƙirƙirarriyar basira ta AI, inda aka ƙirƙiri labarin, sannan aka ƙirƙiri jarumai da murya da sauran abubuwan fim ɗin baki ɗaya.

An dai daɗe ana fargabar ƙirƙirarriyar basira za ta raba mutane da dama da aikinsu, duk da cewa fasahar ta riga ta zo, kuma tana tattare da alherai da yawa da masana suke bayyanawa.

Wannan ya sa aka fara fargabar shin AI zai raba jaruman Kannywood da aikinsu? sannan yaya mutane za su karɓi fina-finan ganin cewa ƙirƙirarrun jarumai za su zama tamkar mutum-mutumi ne?

A ɗaya ɓangaren kuma, masana'antar Kannywood dai tana fama da matsalolin tattalin arziki, waɗandan ba sa rasa nasaba da rashin samun kataɓus a kasuwannin fina-finai na duniya.

Sai dai wasu na ganin akwai rashin inganci daga ɓangaren fina-finan, laifin da ake ɗaurawa kan masu shirya fim na Kannywood, duk da sukan musanta tare da bayyana cewa suna bakin ƙoƙarinsu.

Shin AI zai samu karɓuwa?

Abubakar Bashir Maishadda, forodusa ne a masana'antar Kannywood da a yanzu yake jan zarensa, ya bayyana cewa sun karɓa domin tafiya da zamani, amma ya ce ba yadda ake tunani ba.

Maishadda wanda fim ɗinsa mai suna "Aisha" ne ya fi kowanne samar da kuɗi a sinima, ya ce ba sa tsoron ɗaukar duk wani mataki da zai taimaka wajen inganta masana'antarsu da ma ayyukansu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai ya ce akwai cikas da suke fargaba, domin a cewarsa, ba dole ba ne mutanen da suke fina-finan domin su, su amsa.

A game da yadda lamarin zai iya shafar Kannywood, Maishadda ya ce, ''Anya ai zai yi tasiri a Kannywoo kuwa? ba lallai ya yi tasiri ba saboda mutanenmu sun fi sha'awar kallon abu na zahiri, ba mutum-mutumi ba.''

Ya ce idan aka lura ko a ƙasashen waje, "ai akwai jaruman da idan ma za ka yi amfani da AI a ɗora su, suna da ƙa'idar haƙƙin mallaka da ba sa yarda a yi amfani da su. Shi ya sa nake ganin zai yi wahala ya yi tasiri sosai a ɓangarenmu," in ji Abubakar Maishadda.

A game da ko za a bar Kannywood a baya wajen ci gaban zamani, Bashir Maishadda ya ce suna tafiya da zamani sosai.

"Amma dole mu yi taka-tsantsan. Don haka za mu karɓa, ku kuma mu ce mun karɓa, amma ba yadda ake tunani ba gaskiya."

Maishadda ya ce tun tuni sun fara amfani da AI a wasu ɓangarorin shirya fina-finai a Kannywood.

"Akwai fim da na yi mai suna "Cikar Buri" akwai wata fitowa da aka manta ba a rufe ƙofa ba, da AI aka yi amfani daga baya waje rufe ƙofar. Ka ga ai zai iya mana amfani wajen irin waɗannan abubuwan, amma ba kacokam mu yi amfani da AI ba. Ku su YouTube na ga kuɗin da kake samu na iya raguwa saboda amfani da AI, har gargaɗi suna yi," in ji shi.

'AI ya riga ya zo"

A nasa ɓangaren, Farfesa Abdallah Uba Adamu, cewa ya yi akwai buƙatar a karɓa harkar da sauri, sai a rarrafa a tare domin tafiya da zamani, inda a cewarsa hakan zai sauƙaƙa wa masana'antar.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, masanin harkokin adabi da fina-finan ya yaba da ƙoƙarin daraktan fim ɗin "Dirty Game", Kamalu Mijinyawa bisa zama zakaran gwajin dafi.

"Kamal ya yi amfani da nau'ukan AI guda uku wato ChatGPT da Gemini da Grok. A fim ɗin babu kyamara, babu mai rubuta labari da tsarawa babu jarumai babu komai da ake buƙata wajen shirya fim. Komai da ke cikin fim ɗin ƙirƙirarsa aka yi da AI," kamar yadda ya rubuta.

Sannan a tattaunawarsa da BBC, Farfesa Abdallah ya ce babu laifi a shiga fargaba saboda zuwan AI, inda ya ƙara da cewa babu yadda za a yi, "tunda dai ya riga ya zo, kuma ba zai dakata ba, ya zama dole a karɓe shi a yi amfani da shi yadda ya kamata."

"Zancen ana karɓar abu da ɗari-ɗari a da ne, idan ba ka karɓa yanzu ba, za a bar ka a baya," in ji shi.

A game da ko Hausawa za su kalla fina-finai da akwai mutum-mutumi, Abdallah Uba ya ce masu kallo sun daɗe suna kallon irin fina-finan a baya, wanda hakan ya sa yake ganin ba zai zama sabon abu ba.

"Ai ba wai zuwa ɗaya za a daina amfani jarumai ba ne na mutane. Za su cigaba da fitowa har zuwa wani lokaci. Amma dai ya kamata mu karɓi fasahar da sauri domin ta riga ta zo, kuma ba za ta tafi ba."

A game da irin amfanin da yake tunanin za a iya fara amfani da AI, Farfesa Abdallah ya ce fasahar za ta taimaka wajen sauƙaƙa shiryawa da ɗaukar fim.

Ya yi misali da rubutawa da tsara labarai da aikace-aikacen tsara wajen ɗaukar fim da waƙoƙi da sauransu.

"Hatta tsalle-tsalle da ake fargabar za a iya samun rauni, za a iya ɗaukar hoton jarumin a saka a AI ya yi tsallen cikin sauƙi ba tare da ya samu matsala ko ya ji wani rauni ba," in ji Farfesa Abdallah.